← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 54

Sashe 48

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara zama y yi ya ce, "Narma!." In ya faɗi sunan nan kamar ya soka mata abu a zuciya haka take ji, bata taɓa jin wanda yake faɗar sunan ta daidai kamar sa ba. Ta narke tana kallon sa ya ce, "kar ki sake yi min wani yare in ba hausa ba in muna tare kin gane?." Jin yadda ya faɗa a kausashe sai ta nutsu sosai ta ce, "in sha Allah bazan sake ba. I'm sorry..." hararar da ya yi mata ya saka ta tsorata sosai ta ce, "ka yi haƙuri" ta faɗa a sanyaye. Bata taɓa zaton soyayya zata saka ta tsoron wata halitta irin Omar ba, tsoronsa take ji matuƙa bata son abinda zai ɓata masa rai ko kaɗan. Shiyasa take kiyaye dokikinsa dan a zauna lafiya.

"Yaushe zaka saba dani ne Faruk? Ka kasa sakin jiki dani har yanzu. Ina sonka, da kai kaÉ—ai nake so na rayu. Don Allah kar ka dinga amfani da rauni na akan sonka kana cutar dani." Kallon ta ya yi bai san lokacin da ya yi murmushi ba, kamar shashasha itama sai tayi murmushi ta ce, "na gode da wannan kyauta Faruk."

Miƙewa tsaye ya yi alamun zai tafi ta ce, "Zaka tafi ko ruwa baka sha ba."
"Zan sha wani lokaci" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba, dan in yana kallon ta wani ne yake shiga jiki sa take sai yanayinsa ya canja.

Miƙewa itama ta yi ta kalli window ta kalle shi ta ce, "Ga irin wajan zaman ka can a wancan gidan, naga kana son zama a gazebo, dole gidan auren mu kasance da gazebo saboda ka shiga ka huta" ta faɗa cikin son burgewa. Kallon ta ya yi kafin ya ɗauke kai ya ce, "kina tunanin samunta a aurena?."

Narma jin ya bata amsa sai ta sake karya murya cikin iyayi ta ce, "ko ba yanzu ba ko nan gaba. Kuma gidana da nake ginawa akwai."
"Gidan ki!" ya maimaita yana yi mata kallon bakin da hankali kafin ya sake cewa, "kina tunanin in Allah ya ƙaddara na aure ki ni Omar zan zauna a gidan da yake naki? Hmmm baki san Omar ba har yanzu, ki yi gaggawar canja tunaninki a kan hakan" ya sake cewa, "In har da gaske kina son auren Omar ki san irin tunanin da zaki yi" ya faɗa dan ya tuna mata, dan shi ba irin mazan da suke zama a gidan mata bane, gwara ya yi mata gargaɗi da babbar murya.

Narma a sanyaye ta ce, "Ina yi mana fata a rayuwar auren mu mu samar da ita."
"Dakyau!" ya furta yana fita ta biyo bayan sa tana ta yi masa shagwaɓa yana sharewa kamar bai gani ba ko kamar baya jin shagwaɓarta a jikinsa, yana ji kawai bazai nuna bane, dan in ya nuna mata shine a ruwa. A haka suka yi sallama ya fita ya samu Bashir na jiran sa suka koma gidan Didi.

         Bayan fitar Omar Didi tana zaune rana ta buɗe sosai tana shan iskar fankar solar taji anyi sallama. Amsawa tayi tana jiran mai shigowa sai kawai suka haɗa ido da Nayla. Didi ta wara ido ta ce, "Nayla!." Nayla tayi dariya ta ƙaraso kusa da Didi ta zauna ta ce, "Na'am Didi." Didi da farin ciki ta ce, "Saukar yaushe? Wannan bazata haka."
"Saukar É—azu. Ina yini." Didi ta amsa da fara'a tana tambayar ya mutanen gida ta tabbatar mata da kowa lafiyar sa lau.

Didi ta ce, "wallahi nayi kewar ki Nayla, haka kawai nake ji bana so ki bar Kano." Nayla tayi dariya ta ce, "wallahi nima bana son barin Kano Didi, amma ya zama dole dan yanzu na fara aiki ma a can."
"Ma sha Allah, amma na taya ki murna Nayla. Allah ya sanya alkhairi ya kaÉ—e fitina."
"Amin ya rabbi. Na gode sosai Didi."
"Amma kwanaki zaki mana ko?." Nayla tayi dariya ta ce, "Ranar Sunday da safe zan tafi, kin manta na ce Ina aiki?." Didi ta ce, "kai! Wallahi ban ji daÉ—i ba. Amma babu komai in sha Allah É—an Kano zaki aura, kin ga sai dawo Kano gabaÉ—aya mu dinga ganin ki."

Nayla tayi murmushi amma a zuciyar tana aiyana in sha Allah ƙaninki zan aura Didi, amma a bayyane sai bata ce komai ba. Didi ta kalle ta tace, "an sha saudia. Ina fatan kin roƙawa mutumin ki shiriya a wajan Allah kamar yadda na ce, kin yi min?."

Wani iri taji a zuciyarta, domin kuwa babu ranar da zata fito ta koma bata ambaci sunan Omar a addu'arta ba, ba wai tana cewa Allah ya bata shi bane, tana roƙon Allah ya shirya shi ya cire masa dukkan abinda yake yi ya dawo mutum kamar kowa. Ita kanta bata san sau dubu nawa tayi masa addu'a ba. Har ɗawafi ta yi akan Allah ya canja Omar, ta yi ɗawafi bama sau ɗaya ba.

A bayyane ta ce, "Nayi masa sosai Didi, ba ma shi kaɗai ba har da ke. A jikina nake jin Allah zai amsa da gaggawa." Didi ta ɗaga hannu ta ce, "Allah Amin" ta kalli Nayla ta ce, "na gode Nayla, Allah ya bar zumunci." Nayla tayi murmushi ta amsa da amin. Didi ta kalle ta tana murmushi ta ce, "wallahi Nayla haka nan Allah ya saka min ƙaunarki, Ina jinki kamar ƙanwata." Nayla ta murmusa ta ce, "nima Ina jinki kamar yayata Didi."

Didi tayi murmushi ta ce, "Amma Nayla naga kin rame, kin yi rashin lafiya ne?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "haka ake cewa na rame amma ni bana gani, lafiya ta lau kawai kiɓar nake so na rage." Didi tayi dariya ta ce, "ai baki da kiɓa Nayla, gaki nan ƴar chubby dake in kika rame ai baza ki yi kyau ba. Gaskiya ki daina." Nayla tayi dariya kawai bata ce komai ba sai ledar da ta shigo da ita ta miƙawa Didi ta ce, "ga tsabar ki."

Didi ta karɓa ta ce, "Nayla harda tsaraba? Ai ni iya addu'ar da kika yi min itace babbar tsaraba a wajena." Didi ta buɗe ta ga doguwar riga irin mai babban mayafin nan da ake yayi, original ƴar Saudia dan a yanayin jikinta ma zaka tabbatar da ba fa irin ƴan Nigeria ba ce. Sai zamzam da chocolate da kuma cross shoe. Didi ta fara godiya Nayla ta ce, "Didi yanzu ki ka ce ni ƙanwarki ce ko? Don Allah ki bari."

Didi bata daina ba ta cigaba da addu'a tana yi mata godiya. Nayla ta sake bata leda ta ce, "Ga na...." Sai ta rasa wanne suna zata kira shi, Omar zata ce ko Tiger? Didi kallon ta take yi tana so ta ji na waye, Nayla ta ce, "Na Yaya Omar."

Didi tayi dariyar tsokana ta ce, "A'a, harda su kaza a cin danƙoo? Kuma yaushe Omar ɗin ya zama Yaya Omar?." Nayla tayi murmushi ganin tana tsokanarta, ta karɓa ta buɗe taga doguwar riga irin ta maza mai dogon hannu, ga wata cover ƙarama mai kyau a ciki, ta ɗauko ta buɗe idon ta ya faɗa kan lafiyayyar azurfa mai bala'in kyau.

Didi ta kalle ta a sanyaye ta ce, "Nayla duk wannan na Omar ne? Azurfa da take da tsada a nan ƙasar ma balle a Saudia?. Bayan azurfa ma harda doguwar riga ga wani abu ma a ciki ina ji" ta faɗa tana fito da ƴar ƙaramar kwalba ta oil perfume ta ce, "ga turare. Nayla hidimar bata yi yawa ba?."

Nayla ta ce, "Haba Didi wallahi babu komai, an zama É—aya kar ki damu." Didi tayi ta ce, "To Nayla, mun gode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, Allah ya baki miji na gari." Nayla ta amsa da amin kafin Didi ta ce, "Su Omar an samu azurfa, daman hannun nasa babu komai kamar ba saurayi ba, kin taimaka kin fito dashi ya zama mutum shima kamar kowa. Kwanaki ya je kasuwa zai siya aka ce masa azurfa mai kyau daga ko dubu talatin ta fara, ya dawo na ce ya baka siyo ba wai ai ba hauka yake yi ba, ta sha zaman ta." Nayla tayi murmushi kamar yadda Didi take murmushin itama tana sake yiwa Nayla godiya.

Basu ji sallama ba kawai sun ganshi ya shigo falon, Didi ta kalle shi ta ce, "shigowa babu sallama Omar?." Kallon Didin ya yi kafin ya kalli wacce take zaune a kusa da ita yana aiyana wacce baƙuwa ce tazo musu gida. Nayla tunda taji an shigo an kuma ce Omar ta nutsu ta sunkuyar da kai ƙasa.

Sake kallon Didin ya yi ya ce, "Nayi sallama baki ji ba ne." Ajiyar zuciya Nayla tayi jin murya sa a kunnen ta, ido ya cikowa da ƙwallar kewarsa da take ji. Didi jin ajiyar zuciyar da tayi sai ta kalle ta a tausashe tace, "Nayla ki bar jin tsoron Omar don Allah, wannan ajiyar zuciya ta meye haka? Kar ki dinga cutar kanki fa." Nayla bata ce komai ba domin Didi baza ta gane ba, ita ba ajiyar zuciyar tsoron sa take yi ba, ta soyayyar da take yi masa ce.

Ta kalli Omar ta ce, "ga tsaraba Nayla ta kawo maka daga Saudia." Sarai ya gane Nayla É—in ya haddace sunanta tsaf a wajan Didi, har mamakin haddace sunanta da yayi yake yi, da zarar ta ce Nayla fuskarta zata zo idonsa. Bai san me yasa hakan ba amma ya É—auki hakan a yawan kiran sunanta da Didi take yi ne, da kuma faÉ—an da ta yi masa a gabanta. Basarwa yayi kamar bai gane ba ya É—age gira sama ya ce, "Wace haka?."

Wani iri Nayla taji a zuciyarta, amma jin muryarsa na kore waccan damuwar. Didi ta Harare shi bata yi magana ba ta ce, "ga tsarabar sai kayi mata godiya, nima ta gwangwaje ni da doguwar riga. Kuma irin ta jikinta sak, ni sai yanzu ma na lura" ta faÉ—a tana nuna masa.
Chapter 48 · 0% Book details