Sashe 3
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawaye ta share ta ɗaga kai sama bayan ta ɗaga hannu ta ce, "Ya Allah ka kiyaye min marayanka, Allah ka kare shi. Ya Allah ka sassauta masa wannan zuciyar da yake fama da ita, ya Allah ka cire masa son wannan ɗabi'ar daga zuciyarsa." Ido ta share tare da sauke ajiyar zuciya ta shiga falo.
•••••••••
*ABUJA*
*SENATOR SAGIR SANI SHATIMA RESIDENT.*
Senator Sagir shine Sanatan Kano ta tsakiya mai ci yanzu, wayeyen mutum ne mai ilimi da kuma son ilimin boko. Kaf ma'aikata gidan sa daga masu degree sai masu master, daƙyar ake samu ya ɗauki mai kwalin diploma aiki, saboda a ganin mai wannan matakin karatu jahili ne bai san komai ba, shi kuma yana ganin aiki da wanda bashi da ilimi ba ya haifar da komai sai dana sani. Kaf masu aikin gidan mata da zama sun iya english, in suna turanci ba ka ce masu aiki ba ne saboda haka ne tsarin mai gidan. Ya raina wanda bashi da ilimin boko, yana kuma ganin wanda bashi da ilimin boko babu inda zai je a rayuwa sai dai ka ƙare a bara.
Ba ya mu'amala da wanda ba shi da ilimin boko, in kuwa ya yi to ta zama dole kuma sai dai a ɓangaren siyasa. Bai damu da ilimin addinin ka ba, shi dai indai kana da na boko ko kafiri ne kai ka fiye masa musulmi.
Matar shi É—aya tal wacce yake so kamar rai, yana da yara guda uku. Nabil, Narma sai Najwa.
    Babban falo ne mai kyau da tsari, kai da ka kalli falon ka san na manya mutane ne na na ƙananun mutane ba, ya tsaru iya tsaruwa duk da babu tarkace a cikin sa. Yanayin tsarin sa zai saka ka tabbatar da falon ba na ƙananun mutane bane ba. Wata kyakykawar budurwa ce fara tas a zaune a falon, sanye take da riga iya guiwa kanta babu ɗankwali hakan sai ya bayyanar da yalwar sumar da take da ita. Tana da kyau wanda a kallo ɗaya zaka fahimta saboda kyawun halittar da Allah ya yi mata.
Barr Narma Sagir Sani shatima kenan wacce ake yiwa laƙabi da Barr Nass. Second born a wajan Senator Sagir, ƴar kimanin shekaru ashirin da shida. Bata da ƙiba daga sama amma Allah ya yi mata baiwar ƙira mai kyau daga ƙasa, tana baiwar sura wacce in ka kalla za ka so ka sake kallo saboda yadda ta tsaru. Barr Nass manager director ce a ɗaya daga cikin kamfanin mahaifin ta. Sananniya a social media musamman a instagram da X.
"Daddy Ina so zan shiga Kano next week" ta furta cikin muryarta irin ta Æ´an gayu Æ´aÆ´an Daddy da Mummy.
Kallon ta ya yi a lokacin ta kai abinci bakinta ya ce, "me ake yi a Kano?." Ta É—an yi farrr da idanu wanda hakan ya zamar mata jiki ta ce, "arewa24 sun yi inviting É—ina then..akwai bikin friend É—ina Samra kamar ma ka san Dad É—in ta. Bashir na Gwaggo ne babanta."
Dad ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, "yes, i knew him. But, how many days are you planing to spend in Kano?." Ta ajjiye spoon É—in hannunta ta ce, "Uhumm two to three weeks. At least two weeks." Daddy ya girgiza kai bayan ya haÉ—e fuska ya kalle ta sosai ya ce, "Narma!." Jin yadda ya kira sunan ta sai ta kalle shi ta ce, "Dad."
"You know i don't want you to go to Kano, right?."
"Yes dad, but it's necessary. And dad I'm not a little gril fa, I know what I'm doing. Zan iya kare kaina daga duk abinda ka ke gudu, so just calm down." Kallon ta yake yi kafin ya kalli wacce take zaune a gefe sa ya ce, "Kina Jin abinda take cewa baza ki yi magana ba?."
Mum ta kalle shi ta ce, "wannan maganar tsakanin ku ne babu ruwana a ciki. Ta faÉ—a min batun zuwa Kano nace sai ta jira umarninka."
Dad ya kalle ta ya ce, "Narma kin san abinda ya faru last a zuwan ki kano ko? An yi attacking É—inki kin tuna wannan? Ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu bamu san meye ya faru ba."
"Yes Dad ban manta ba, amma hakan ba zai saka na daina zuwa Kano saboda wanda ban san su ba." Dad ya bita da kallo kafin ya ce, "well, I will think about this." Kamar zatayi kuka ta ce, "Dad don Allah kar ka ce bazan je ba."
"I'm not saying that, but sai nayi tunani."
"Okay, thank you" ta faÉ—a tana tashi ta hau sama tana danna waya.
Senator ya bi ta da kallo bayan ta wuce ya kalli Maman ta ya ce, "Kina ganin ya kamata na barta ta je Kano?." Mum ta ce, "yeah ka barta mana, na san Samra ƙawarta ce sosai bai kamata ace bata je ba. Sai ka bata security su kula da ita." Ya girgiza kai ya ce, "Okay zan san abinda zan yi" ya faɗa yana tashi shima ya saman yana tunani. Anya zai iya barin Narma taje Kano? Garin da aka kusa hallaka masa ƴar da yafi ƙauna a duk duniya?. Ko da zai bari taje sai ya haɗa ta da wanda yake tunanin zai kular masa da ita sosai.
Narma ce ta sakko cikin shirin fita, sanye take silk adire kalar ja wanda aka yi masa ɗinki mai ɗaukar hankali. Gabaɗaya ya bi jikinta ya kwanta yana bayyanar da zallar surar da take jikinta, hatta bra ta da saka ana ganin shatin ta komai ya fito kamar bata saka kaya ba. Duk namiji mai lafiya in ya kalli Narma a wannan shiga sai ya ji yanayin da bai shiryawa jin sa ba har ƙwaƙwalwarsa. Ɗauke idanu daga kan Narma a wannan lokaci abu ne mai wahala, sai mai juriyar gaske ne zai kawar da ita daga idanunsa.Ta tsaru a cikin rigar, ta kuma yi mata kyau kamar ka ɗauke ta ka gudu.
Kallon Mum tayi da take zaune ta ce, "Mum zan je shoprite" ta faɗa tana gyara zaman hular kanta. Mum bata kalle ta ba ta ce, "ki taho min da diet stick ɗina ya ƙare."
"Okay Mum" ta amsa tana fita.
A harabar gidan ta tsaya tana ƙarewa motar ta kallo, ta san ta ce a wanke mata amma sai ta ga kamar ba a taɓa ba. Cikin ɗaga murya ta ce, "Ina Kashim!?." Kashim jin maganar ta ya fito cikin sauri da rawar jiki ya ce, "ga ni Ma'am." Nuna masa motar ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ya kalli motar ya kalle ta ya ce, "i'm sorry ma'am, bani da lafiya ne shiyasa......" dakatar dashi ta yi ta ce, "in ka ƙarasa wallahi sai na mare ka." Jin abinda ta ce sai ya kalle ta dan kuwa a shekaru ita ba sa'ar sa ba ce, ko yayanta Nabil ya girma balle ita.
"Who do you think you are...? You won't wash my car, and now you're telling me you're not feeling well?. Damn your sickness!" Ta faɗa cikin ɓacin rai tana kallon sa.
"I'm sorry" ya furta a sanyaye yana kallon ta. Narma ta saka baƙin glasses ɗin hannunta ta ce, "ko mutuwa ce a kan ka kar ka sake aikata wannan gangancin, in na ce ayi kawai ayi in ba haka ba you must regret about it."
"In sha Allah, Sorry Ma'am."
"Zan ƙyaleka saboda wannan ne karo na farko da ka yi haka, kar ka sake maimaitawa" ta faɗa tana barin wajan kafin ta ce, "And make sure you've washed it before i get back" ta faɗa tana karɓar key ɗin motar Mum ta shiga. A guje gate man ya buɗe mata gate ta fita a guje.
Sai bayan ya kulle gate ɗin ya kalli Kashim ya ce, "ka yi sauri ka ƙoƙarta ka wanke kafin ta dawo, yarinyar nan bata da kirki, a iya watan nan masu aiki goma ta kora ta kuma ɗauko guda goma. Ka yi haƙuri ka yi kar ta ci maka mutunci a banza." Kashim ya ce, "wallahi bani da lafiya."
"Haka zaka yi haƙuri. Kuma wallahi ba a wanke musu mota a gidan nan car wash ake zuwa, kawai saboda ta samu hanyar ciwa wani mutunci ne ya saka ta ce ka yi. Dan ita tana so ta ga tana ciwa mutum mutunci. Ta waje guda take da kirki wani lokacin, in ta ga mutum a kwance babu lafiya a nan zata ɗan tausaya masa. Amma sai ciwo ya kai ciwo, bata ɗauki ƙaramin ciwo a komai ba." Kashim ya yi ajiyar zuciya ya wuce jiki a sanyaye. Inda an sabo da wulaƙanci da cin fuska da ƙasƙantar da mutum da yanzu sun saba a wajan Narma.
•••••••••••
*KADUNA STATE*
*ALHAJI ABDALLAH AHMAD RESIDENT.*
Alhaji Abdullahi sannen ɗan kasuwa ne mai ji da kuɗi da iko da kuma alfarma a faɗin ƙasa nigeria. Yana da matuƙar kirki da daɗin mu'amala ga kowa, ko ma'aikatan gidan sa ya ɗauke su kamar ƴan uwan sa baya wulaƙanta su ko tozarci ko yaushe cikin wasa da dariya suke. Mutum ne wanda ya san ya kamata, bashi da wulaƙanci ko kaɗan kamar ba mai kuɗi ba, in ka ga fushinsa akan abu tabbas ransa ne a ɓace.
Mutum ne mai kyautatawa iyalan sa da matuƙar ƙaunar su, baya bari iyalan sa su yi kukan babu ko ya ya abin yake. Haka kawai zasu kulle gidan a bar ƙasar kawai dan jin daɗin ƴaƴan sa da walwalar su. Babu abinda iyalan sa suka nema suka rasa, kuɗi, mota, fita ƙasashen waje da sauran kayan more rayuwa ya tanadar musu dashi. Shiyasa suka kasance ƴan gata gaba da baya.
Matar sa É—aya mai suna Zeenatu, uwar gidan sa mai suna Bilkisu Allah ya yi mata rasuwa shekaru masu yawa da suka wuce. Yaran sa shida, biyar daga wajan Zeenatu É—aya tal daga uwar gidansa. Ahmad shine babba, Jawad, Jidda, Nayla, Jalila, Jalil. Yara ne masu tarbiyya da sanin ya kamata, dukkan su sun tashi a turbar tarbiyya mai kyau, ilimi, addini da kuma kyakykyawar rayuwa.