← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 54

Sashe 19

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        ***** Didi haka ta koma gidan gabaɗaya zuciyarta da jikinta babu ƙarfi, haka ta soya awarar da suka gama ta rage wata ta saka a fridge dan ta ga da yawa sosai, ta zuba wata a food flakas ta zuba sauce ɗin ta fita da kanta ta kaiwa Hajja, Hajja take sanar da ita su Nayla  sun fita itama ta koma gida.

       Kamar yadda baƙon ta ya ce zai zo bayan la'asar hakan ce ta kasance, ita ta manta da zuwan na sa sai da yayi mata waya ya ce gashi nan ya tawo ta tuna. Dole ta miƙe tayi wanka tana fatan Allah ya sa shine na ƙarshen masu zuwa neman aurenta. Ba jimawa ta gama shiryawa ya zo ta sauke shi a harabar gidan dan bata shiga da baƙo ciki saboda bakin mutane.

Sun jima suna tattaunawa kuma ta yaba da kalamansa da nutsuwarsa da alama da gaske yake, ya kuma faÉ—a mata duk abinda ake faÉ—a a kanta shi kuma bai damu ba ya amince da auren ta a haka. A nan ya yi masa kwantancen gidan Kawu da lambar wayarsa dan yaje su tattauna inda dai gaske yake, bai jima sosai ba ya yi mata sallama ya tafi da alqawarin zuwa gidan kawu.

Haka kawai ta ke jin kanta da farin ciki fiye da sauran masu zuwa neman aurenta, zuciyarta lokaci É—aya taji tayi na'am da shi sosai ta kuma ji daÉ—i da har ya tafi Omar bai shigo ba, duk da ya san labarin Omar É—in da komai amma a yanayin da Omar É—in ya ke a ranar tsaf zai kwafsa.

Bata da uwa kuma ta da abokin shawara a kusa sai Hajja, Hajja ce maƙociya, kaka, uwa a gareta. Hakan ya saka ta gama abinda take yi ta rufe gidan ta shiga wajan Hajja. Hajjan kawai ta samu a zaune tana jan carbi tana kallon tashar madina.

Didi ta ce, "Hajja Æ´an matan basu dawo ba?."
"Ba su dawo ba Aisha, amma na san suna hanya tunda magriba ta taho."

Didi ta ce, "Hajja yau ma wani yazo da batun aure, abinda ban taɓa yi ba yau nayi, domin na tura shi wajan Kawu su yi magan." Hajja fara'ar ta ta ƙaru ta ce, "Alhamdu lillah! Aisha ai abinda ki ka yi daidai ne, shi kansa zai yaba da hankaliki da kika tura shi wajan na gama dake."

Didi ta ce, "Hajja ban taɓa jin na gamsu da duk masu zuwa neman aure na wani lokaci ɗaya ba sai shi." Hajja cikin farin ciki ta ce, "lokacin aurenki ne yazo Aisha shiyasa. Duk masu baki da kunu da suke ta magana a kai in yanzu Allah ya rubuta shine lokacin ki sai yanzun zaki yi aure."

Didi ta ce, "sunan saAbdulhamid kuma bashi da mata, ya sanar dani sun rabu matar da yara biyu kuma suna hannunta. Ya ce a yi bincike akan rabuwarsu da matar indai akwai damuwa a kansa bazai sake zuwa ba. Ma'aikacin gwamnati ne a wata babbar ma'aikata."

Hajja ya ce, "Alhamdu lillah! In sha Allah komai ya zo ƙarshe. Ai dai ka miƙa lamarinka ga Allah baka da sauran damuwa, Zaɓi na gari Allah ya yi miki shiyasa ya jinkirta miki auren, ko bani da rai zaki ce na faɗa miki Aisha."

Didi ta ce, "Allah ya sa Hajja." Ta amsa da amin Didi ta ce, "Sai dai Omar nake ji, in ya san na kai batun nan wajan Kawu babu zaman lafiya. Ɗazu ma fa shine yazo waje na kawo min katin bikin Ramla ƴarsa shine Omar ya tarar dashi, Wannan tsinin ɓacin ran Nayla ta tarar."

Hajja tayi dariya ta ce, "yayi faÉ—ansa ya gama dole sai an nemi maganatan ki a fannin aure, shi kansa da yake wannan abubuwan bara maganar auren na sa ta zo dole sai ya neme su. Babu mutumin kirkin da zai bashi auren Æ´arsa ba tare da ya nemi danginsa ba."
"Hmmm! Ina jin wannan ranar a zuciyata Hajja, ranar da Omar zai je ya nemo dangin mu saboda batun aurensa. Allah Hajja gani nake akan Omar ya neme su zai iya fasa aure, zai iya zuwa ya nemi wacce ba zasu damu da danginsa ba ya aura."

Hajja tayi dariya ta ce, "haka ki ke gani, amma zai neme su da kansa. Ban da abin Omar tunda har suka fahimci a baya basu kyauta ba kuma suke ƙoƙarin gyara laifin su ai ya kamata ya yafe musu." Didi ta ce, "Omar da kafiya, taurin kai, zuciya, riƙo, zafin rai, zafin zuciya ai aminan juna ne, Allah kaɗai ya san yadda zamu kwashe dashi in yaji na tura shi wajan Kawu."

  "To banda abin Omar in baki tura shi wajan Kawu ba wajan wa zaki tura shi?." Didi tayi dariya ta ce, "ya ce an faɗa min shi bai yi hankalin da zai bada aurena ba." Hajja tayi dariya sosai ta ce, "a shekaru dai yayi, amma ina hankalin da Ummaru zai bada aurenki?."

Didi tayi murmushi Hajja ta ce, "ki cigaba da yi masa addu'a, kamar uwa ki ke a wajansa, ki ta yi  masa addu'a wata rana sai labari."
"In sha Allah Hajja, addu'akullum ana yi masa har taimakon malamai nake nema akansa, in sha Allah canji zai zo. Ba dan malam Salahudden ya rasu ba ai da shine maganin Omar, yana matuƙar girmama malamin." Hajja ta ce, "a yanzun ma zai dawo hankalinsa in sha Allah, nan gaba shima mu sha biki."

Didi ta ce, "wai! Omar da mata." Hajja ta ce, "ba abun mamaki bane, kuma cikin ikon Allah daƙyar in ba ta silar mace zai canja ba." Didi ta ce, "wai ta hanyar soyayya?."
"Kina ganin bazai yu ba ne?."
"A'a, amma lamarin ne akwai firgici, wacce yarinya ce zata so Omar a haka?. Ga halinsa na bayyane ga zafin zuciyar da yake da ita?."

Hajja ta ce, "kadai Allah ya bamu lafiya, Allah ya yafi gaban komai." Didi ta ce, "Haka ne Hajja. Bara na koma magriba tayi in Nayla ta zo a gaishe su" Hajja ya amsa tana sake yi mata addua'a tana amsawa ita kuma ta fita tana jin Hajja kamar mahaifiyar ta saboda kirki da karamcin ta.

Nayla sai bayan i’sha aka dawo dasu daga gidan ƙanwar mahaifiyarta ya wacce suke cewa Mama. Ɗanta mai suna Abbas shine ya dawo dasu har gida sannan suka shiga wajan Hajja tare. Yana yin sallama Hajja ta ce, “wa nake ganin kamar Abbas?.” Yayi dariya ya ce, “ni ne Hajiya Hajja, kin wuni lafiya?.”

“Lafiya lau mara kunya, baka zuwa ka gaida mutane sai dai in zaka kawo babbarka sannan ake ganinka, yanzu ma na san saboda Nayla ne ka shigo ko?.” Yayi ƴar dariya ya ce, “Haba Hajja, ni da nazo ki bani dambun nama sai ki fara ƙorafi?.”

Hajja ta ce, “nayi ɗin, baka zuwa gidan nan kai kwata-kwata sai da dalili.” Yayi murmushi ya kalli Nayla da take jona chaji kasancewaar an gyara musu wutar gidan. Hajja ta bishi da kallo tana kallon abinda yake kallo ta ce, “ya ƙannen naka da Yayar?.”
“Lafiya lau Hajja, kowa yana gaisheki.”
“Ina amsawa da kyau.” Daga nan suka yi shiru ya sake kallon Nayla da take aikinta ba ta shi yake yi ba.

Hajja ta ce, “Hauwa ga saƙo ki can Aisha ta kawo miki tun yamma.” Nayla ta kalli Hajja ta ce, “to.” Abbas ya miƙe ya ce, “Hajja ni zan koma, sai Allah ya dawo dani.”
“Allah ya kiyaye.” Ya kalli Nayla ta ya ce, “Hawwa zan tafi.” Ta kalle shi ta ce, “To Yaya Ab ka gaida gida.”
“Bazaki raka ni ba?.” Ta shagwaɓe fuska ta ce, “na gaji Yaya.” Yayi murmushi ya ce, “ki huta.” Itama murmushin tayi ya fita daga falon.

Salma ta bi shi da kallon ta kalli Nayla ta ce, “Nayla anya Yaya Abbas bai ƙyasa dake ba?.” Nayla ta wara idanu ta ce, “rufa min asiri ki bar zancen nan.”

Hajja ta ce, “babu zancen a rufa miki asiri ai gaskiya ta faɗa, ni kaina na lura da yana sonki Hauwa’u.” Gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba ta kalli Hajja ta ce, “don Allah Hajja ki daina faɗar haka, ni ɗan uwana ne babu wannan batun a tsakanin mu. Kuma kun san shi yana da wasa da dariya babu lallai abinda ki ke zargi ne. Ga su Yaya Muhmmad da su Yaya Aliyu, da Yaya Khaleed duk ba a ce haka ba sai shi?.”

Hajja tayi murmushi ta ce, “Mai Babban suna da Ali babu wanda ya nuna wani abu a kan ki kamar yadda Abbas ya nuna, daman ni ina son auren zumunci kuma in sha Allah a cikin zuri’ata sai an yi auren zumunci ba ɗaya ba ba biyu ba. Da kaina zan cewa Abbas ya samu Daddyn ku da maganar ki.”

Nayla kamar tayi kuka ta ce, “Don girman Hajja ki bar zancen nan, wallahi ni bana so” ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki dan ita in akwai abinda ta ƙi jini bai wuce auren zumunci ba. Haka kawai baya burgeta balle tayi tunanin zata yi nan gaba. Balle ma kuma Abbas da ya kasance mai ƙirar mazan da ta tsana, bana son namijin da gym ya nuna shi, ita ta fito son mai normal ƙira ba murɗaɗɗe ba.

Didi tana zaune har takwas na dare Omar bai shigo ba duk sai ta damu ta ɗauko waya tana kiransa amma wayar ma taƙi shiga. Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ta amsa tana kallonsa ganin fuskarsa tana nan kamar ɗazu a ɗaure tamau. Didi ta ce, “ina ka shiga ina ta jiran ka tun dazu?.” Kamar ba zai ce komai ba sai daga baya kuma ya ce, “ina nan.”

“Ka zauna kaci abinci.” Kai ya girgiza alamun baya ci sannan ya ce, “meyasa baki kira ni ba lokacin da baƙonki yazo ba?.” Ta kalle shi ta ce, “na san ba zaka dawo ba saboda ranka a ɓace yake sosai, Yanzu ka zauna kaci abinci.”
“Bana son cin komai.”
“Ko abincin rana baka ci ba na san kuma kai ba mai son abincin waje bane, ka zauna na kawo maka awara nayi maka da kaina.”
Chapter 19 · 0% Book details