← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 54

Sashe 25

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sen wani takaici ya tokare masa maƙogwaro amma bai nuna ba ya ce, "Tiger ya kamata ka san ƴata ce yarinyar da ku ke tare."
"To dan tana Æ´arka sai me? Dan tana Æ´arka sai na bari tayi min abinda yake so? Ta tambayi waye ni a garin nan, babu wanda yake É—aga min murya balle rashin kunya ko zagi. Sanin Æ´arka ce ya saka nake faÉ—a maka, ka ja mata kunne. Senator ba haka Tiger yake ba, Tiger baya jure koda É—aga murya ne balle maganar baki."

Sen ya danne ɓacin ransa ya ce, "na ɗauka yadda ka ke girmama ni zaka girmama ƴata." Omar ya ce, "in da ta so zamu girmama juna, bata girmama ni ba nima bazan girmamata ba. Shiyasa na ce a bar aikin nan kawai." Numfashi Sen ya sauke ya ce, "na zaɓeka ne saboda na san zaka iya kular min da ita sosai, na zaɓeka akan jami'an tsaro masu bindiga amma na ga kamar hakan bai maka ba."

"Kawai bana tolerating nonsense ne" ya bashi amsa kai tsaye ba tare da wani tunani ba.

Tolerating nonsense, Senator ya maimaita a zuciyarsa cike da mamaki,  wai daman har yana da karatun da ya san ne kalmar take nufi, kuma dan bashi da hankali shi yake faɗawa haka akan ƴarsa?. Lallai ya zama dole ya san abin yi, da an kammala zaɓe zai saka a yi masa abinda zai manta ma ya taɓa sanin Sen a duniya.

Sen ya ce, "Amma Tiger meye buɗe mota? Da ka buɗe mata kun tafi da shikenan." Wani murmushi ya yi na rainin hankali kana ya ce, "a kaf duniya Yayata kaɗai zan iya yiwa haka, bayan ita babu wani ko wata a duniya da zan buɗewa mota. Ka faɗa mata indai sai na dinga buɗe mata mota zata shiga ta je inda take so to baza ta je ko ina ba." Duk da ba a zafafe yake maganar ba amma kalamansa ciwo suke yiwa Sen sosai kawai bashi da zaɓi ne.

"Is okay, ka koma ka kai ta yanzu."
"Bazan iya ba, na riga na dawo gıda sai dai wani lokacin."
"Well, gobe zata je interview ƙarfe sha daya na safe."
"Allah ya kaimu" ya amsa a daƙile dan wallahi gabaɗaya ma aikin ya fita daga ransa, dan ya san cigaba da aiki da ita babbar damuwa zai haifar, tabbas zai iya zama silar komawar sa prison dan wallahi bazan sasssuta mata ba.

Bayan ya kashe wayar gida ya shiga wajan Didi, ganin ta a zaune kamar ba ita ba ya saka shi ya ƙarasa ciki fuskar nan a tamke sosai ya ce, "Didi lafiya?." Ta kalle shi ta ce, "kaina ne yake min ciwo Omar, har zazzaɓi nake ji."

"Mu je a dubaki" ya faɗa  yana kallon ta. Girgiza kai ta yi ta ce, "kar ka damu na sha magani zan warke."
"Ki zo mu je a baki magani" ya sake maimaitawa yana kallon ta. Kallonsa itama tayi dan tasan baya ƙaunar ya ji tana ciwo kwata-kwata, yafi so da ta ce babu lafiya ayi maganinsa. Maganin da ta sha ta nuna masa ta ce, "na sha magani."

"Waye ya baki?."
"Jikar Hajja Salma, ka san karatun lafiya tayi." Shiru yayi kawai jin ance jikar Hajja kawai sai fuskar Nayla ta zo idanunsa ba tare da ya san dalili ba, ya kulle ido ya buɗe akan fuskar Didi ya ce, "yanzu da sauƙi?."
"Sosai ma."
"Allah ya ƙara lafiya" ya furta a sanyaye. Ta amsa da amin tana kallon sa tana mamakin abinda ya ɓata masa rai.

"Ki je ki kwanta" ya katse mata tunani yana kashe tv É—in. "Bana jin bacci Omar, Zaman kaÉ—aicin nan damuna yake yi sosai, in ka fita sai ni kaÉ—ai, na danna wayar na gaji, nayi kallon na gaji."

Bai ce mata komai ba ya zauna daga nesa da ita yana kallon ta. Gabaɗaya jikinsa yayi sanyi baya so yaji tana yin ciwon kai balle harda zazzaɓi, baya so yaga Didi na rashin lafiya, gabaɗaya sai ya damu kansa kamar shi ya ɗora mata. Didi ta kalle shi ganin yana kallon ta tace, "kar ka damu fa, da nayi bacci na tashi zan ji daɗi." Kai ya ɗaga mata kawai bai ce komai kuma bai daina kallon ta ba.

Ganin ya damu sai ta miƙe ta ce, "ka kashe hasken falon zan je na kwanta." Kai ya ɗaga mata kawai ta shiga ciki dan kawai ta kwantar masa da hankali.

Shiru yayi yana tunani, bai san dalili ba kawai fuskar Narma ta kawo masa ziyara a idanunsa, yadda take kallon sa tana tsaye da mamaki a idanunta na kalaman da take faÉ—a masa shi yake gani. Tsaki ya yi ya kawar da tunanin daga zuciyar sa yana zaune bai tashi ba.

Bai kashe hasken ba kuma bai tashi ba dan bazai iya tafiya ya bar Didi ita kaÉ—ai ba, in ya tafi sai yaga kamar ciwon zai same ta sosai. A kan kujera yayi bacci ba tare da ya san hakan ba sai dan bazai iya tafiya ya bar ta ba.

         Ƙarfe huɗu na dare ta farka kamar kullum, tayi mamakin ganin haske a falo a kunne, ta leƙo ta ganshi a kwance yana bacci hankalinsa kwance. Murmushi tayi ta ƙaraso ta kashe hasken falon ta koma ɗaki ta yi alwala ta tayar da sallah.

Sai da aka kira asuba sannan ta ƙaraso inda yake ta kalli gefen sa taga ya ajjiye ƙaramar wuƙa da wani ƙarfe da alama a jikinsa suke, ta girgiza kai ta tashe shi ya buɗe ido ta sanar dashi lokacin sallah ya yi sannan ta koma ciki shi kuma ya tashi ya fita.

Bayan an idar da sallah ya dawo har É—akin ta ya shiga kamar yadda yayi tunani tana kan sallaya ya ce, "Didi ina kwana." Murmushi ta yi ta ce, "ka tashi lafiya mai bacci a falo?." Murmushi shima ya yi sannan ya ce, "ya jiki?."
"Na ji sauƙi sosai. Yau baka tashi sallar dare ba, ko baccin ne?."
"Kawai ban tashi ɗin bane, Allah ya ƙara lafiya" abinda ya ce kenan ya wuce ya fita daga falon nata.

Kamar yadda Sen ya ce masa ƙarfe sha ɗaya bai jira sha ɗayan tayi ba ya tafi dan shi mutum ne mai girmama lokaci, baya son african time kwata-kwata, shiyasa in kace masa ƙarfe goma to tabbas goman zaka ganshi, in ka san ƙarya ka ke ma gwara kar ka faɗa masa. Tare da Tk suka je har cikin gidan ya nemi waje ya zauna bayan suka gaisa sama-sama da masu aikin gidan.

Su kam mamaki suke yi ganin da alama ba a kore shi ba akan abinda ya yi jiya, suna jinjina ƙarfin hali da kuma sa'ar da yake da ita, in ba haka ba waye zai yiwa Narma haka ya kwana lafiya. Yahya ne ya zo zai zauna kusa dashi Tk ya ce, "kai yanee?." Yahya ganin Tk da yanayin sa ya saka shi yin sak ya miƙawa Omar hannu ya ce, "Omar barka da safiya." Kallon sa ya yi suka gaisa Tk ya ce, "to kama gabanka."

Kallon sa Omar kawai ya yi sai Tk ya yi shiru shi kuma ya kalli Yahya ya ce, "ka zauna." Ba musu ya zauna ya ce, "ban ɗauka ma zan ganka kazo yau ba duba da abinda ya faru jiya, na ɗauka shikenan kwantiragin aikinka ya ƙare." Omar bai amsa masa ba sai agogo da ya kalla sha ɗaya saura mintina goma sha biyar. Numfashi ya sauke ya ce, "tana da sauran mintina sha biyar."

Yahya ya ce, "don Allah Omar na tambayeka." Kallon sa kawai yayi alamun ina ji shi kuma ya ce, "don Allah ne ka ke taƙama dashi ka ke yiwa ƴar sanata haka?." Omar ya ɗauke kai daga kallon sa ya ce, "ka tambayi sanatan."

Zai sake magana kawai suka ga an taho a guje an zube a gaban Omar yana cewa, "Madugu uban tafiya, madugu uban matsiyata, a hauka a zame ka hau mutum ka zauna daidai. Gadon ƙaya ka ke wallahi duk wanda ya hauka babu shi babu bacci, wando ƙarfe ka ke saka ka sai wanda ya shirya. Ba ayi maka wargi ka ƙyale, jan wuya jinin Didi, Allah ya ja da ran yayar mu."

Kallon wanda ya zube a gaban na sa ya ke yi ya kalli Tk sai Tk ya ce, "Damisa ai kunama ne ɗan yankin su Jijiya." Kai ya girgiza kawai ya kalli yaron da ya miƙe ya ƙaraso wajan Tk yana cewa, "kai ashe babbar giwa ce da kanta a wajan nan, ina na sani ina can ina shirme."

Yahya ya maimaita sunan Damisa yana kallon Omar Tk ya ce, "eh Damisa, shine dai wanda ka ke jin labari a radios shine a zaune a gaban ka! Kayi hattara domin taken Damisa ƙi sabo." Yahya ya girgiza kai yana mamakin to me ya haɗa shi da Sanata kuma? Lallai dole ya yi jiji da kai, wannan kirari dake kwarara masa, kuma ga sunan sa da yayi tambari kusan kowa ya san shi, ko baka san shi ba kasan sunan sa.

Yahya ya sake kallon sa ganin maza buyu suna gefensa a tsaye shi kam sai aikin danna waya yake yi yana kuma kaɗa ƙafa, in ka shigo gidan sai ka ɗauka mai gidan ne a zaune saboda yadda ya kame kai baza ka ce ma shi bane.

Mamaki Yahya yake yi sam bai yi kama da ƴan daba ba sai ma kama yake yi da jaruman gaske, kallo ɗaya zaka yi masa kayi tunanin babban hamshaƙin mai kuɗi ne ko ɗan mai ƙudi saboda yanayin fatarsa da kyaun da Allah ya bashi, in ka sake kallon sa sai ka ɗauka soja ne, saboda kwarjini da ƙirarsa. In ka kalli fuskarsa kaga yalwar gashi sai ka ɗauka wani babban ma'aikacin gwamati ne ko hamshaƙin ɗan kasuwa. Dan ƙananun kaya ya saka harda takalmi sau ciki, kai baza ka kalle shi kace Damisan da ke zance bane.
Chapter 25 · 0% Book details