Sashe 14
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abiy ya ce, "har abada bazan iya barwa kowa Nayla ba, ke bama Nayla ba kaf ƴaƴana biyar har Nayla shida bana tunanin zan iya barin su su je wani wajan su zauna gaskiya. Sai dai aje ayi ziyara a dawo, ni ne na haife su haƙƙin riƙe su a hannuna yake."
"To ka ƙara mata lokaci kafin ta fara zuwa aiki ta zauna a Kano wajan Hajja."
Abiy ya sauke numfashi ya ce, "zan yi tunani a kan hakan na gani, amma a yanzu dai sati ɗaya na bari tayi, in naga zan ƙara mata sai na ƙara mata, In naga bazan iya ba ta dawo gidan mahaifinta." Mama tayi murmushi ta ce, "Hakan yayi, Allah ya kaimu." Ya amsa da amin kafin ya tashi ya shiga ɗaki ya bar Mama a zaune a wajan.
    "Nayla hmmm! Ai wallahi sai na raba ku, yadda ta bar gidan nan a bana tunanin zata sake dawowa cikin sa, in ma ta dawo na ɗan lokaci ne kawai amma sai nayi amfani da wayo da dabarar da na nisanta ka da Nayla. Sai na san yadda na yi Nayla ta je gidan mijin da zai ci ubanta, ya hanata walwala ya kuma hanata jin daɗi. Burina Nayla ta rayu a gidan auren da zata sha wahala kamar ydda uwarta ta wahalar dani, Zan fashe wahalar da na sha akanta!." Girgiza kai Mama take yi tana hasaso lokacin da wannan buri na ta zai cika. Bata nufin Nayla da ko wanne irin sharri ko makirci, ta raini Nayla daidai da yadda ta raini ƴaƴanta, ta bata tarbiyya da rayuwa mai kyau. Ita babban burin ta Nayla ta yi aure a inda zata sha wahala kuma sai tabbatar da ta cika wannan buri na ta hankalin ta zai kwanta, ta yi ƙwafa ta miƙe zuwa daƙi.
Washe gari
Kano.
Washe gari Alhamis Nayla da azumi ta tashi kasancewar ta mai ibadar azumin litinin da alhamis, ranta a jagule gabaɗaya bata da walwala saboda rashin chajin waya, daman gidan Daddy da suka je da daddare ne ya saka ta cikar wayarta kuma ta ƙarar gashi yanzu kuma babu wuta kuma ba a gyara solar Hajja ba.
Hajja na kula da ita tana zaune a falo tayi shiru masu yiwa Hajja aiki suna ta aikace-aikacen su kafin kammala su bar wajan. Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u baki da lafiya ne? Ko ki karya azumin." Ta kalli Hajja ta ce, "Rashin chaji bala'i ne Hajja, duk shi ya saka ni a wannan yanayin."
Hajja ta ce, "ki kaiwa Aisha ta saka miki mana." Nayla ta dafe ƙirji ta ce, "har kin saka gabana ya faɗi, ni in sake shiga wannan gidan...? Ai har abada." Hajja ta ce, "To a ina zaki saka chajin?."
"Bara Salma ta tashi mu ji ya za a yi." Salma ce ta fito da kayan bacci ta kalli Nayla ta ce, "meye naji kina maganata?."
"Salma chaji nake so wallahi, Ke kin san bana son zama babu chaji."
"Ga power bank É—ina can ki saka, amma ba zai yi miki da yawa ba dan shima babu chajin."
Jin haka sai taji daɗi ta saka chajin amma duk da haka bai mata ba dan da gani chajinsa ya kusa ƙarewa. Sallama aka yi aka shigo falon duk suka kalli wanda ya shigo.
Ganin Daddy ya saka Nayla ta miƙe tana cewa, "Lah Daddy sannu da zuwa." Kallon ta yayi yana murmushi ganin fuskar ƙanwarsa Bilkisu a kan fuskar Nayla ya ce, "yauwa Hawwer, yanzu ma ki ka tashi kenan?" ya faɗa yana kallon Salma da ta fito daga kitchen da kofin shayi.
Hajja ta ce, "Yanzu kam suka tashi dan ko wanka ba su yi ba." Gaisawa suka yi da Hajja kafin suma su gaishe shi ya kalli Nayla ya ce, "Jiya kun je bamu haÉ—u ba, ya services É—in naki?."
"Daddy ai na gama, yanzu aiki nake jira."
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya kawo miji na gari." Hajja ta amsa da amin kafin ta ce, "Duk sun girma sai aure, su huÉ—u ne gasu nan kan su É—aya. Hauwa'u, Salma, Ummimi da Zainab." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne wannan, Allah ya kawo namiji na gari."
Hajja ya ce, "Amin. Amma ga mazaje nan a gidajen ku meye amfanin su?. Zaratan samari nawa muke dasu?." Salma da Nayla suka kalli juna Daddy ma dariya ya yi ya ce, "basu da amfani kan Hajja, muna jira wani ya furta yana son Æ´ar uwarsa ne sai ayi."
"Har sai an jira? Lallai kace zan rarraba su ga duk wanda naso. Duk wanda na ce na bawa É—aya a cikin su ai babu wanda zai musa ko?."
"Babu kam Hajja."
"Yauwa, to ku jira zan fara watandarsu tunda na ga ku kun yi sanyi." Dariya Daddy ya yi ya kalli Nayla ya ce, "Ya gidan babu wuta? Naga kina gumi ki kunna ac mana."
Nayla cikin shagwaɓa ta ce, "ba solar ta lalace ba har yanzu ba a gyara ba." Daddy ya ce, "Subahanallah! Har yanzu ba a gyara ba daman? Ke Salma meye amfaninki da baki faɗa min ba?" Ya faɗa yana ɗauko waya tare da kiran masu aikin solar suka tabbatar da zasu zo a lokacin. Nayla murna kamar tayi me saboda zata samu chaji yadda take so. Daddy sallama ya yi musu bayan ya basu kuɗi ita da Salma ya tafi.
    Omar kuwa a safiyar yana zaune a falon Didi yana cin indomie ita kuma ta kitchen tana wanke-wanke. Sallama akayi tare da shigowa falon ya ɗago yana kallon wanda ya shigo. Ɗiff yayi ganin wanda yake tsaye a bakin ƙofar shi bai shigo ba kuma bai koma ba. Omar bai amsa sallamar ba sai ma ɗauke kai da ya yi. Didi jin sallama kuma bai bada amsa ba ya saka ta fito falon tana kallon inda yake kallo.
Da Yayan Mahaifiyarsu ta haɗa ido Baba Adamu sai kuwa ta saki fara'a ta ce, "Lah Baba kai ne tafe? Sannu da zuwa." Ƙarasowa tayi shima ganin ta sai ya shigo yana murmushi ya ce, "Ni ne Aisha."
"Sannu da zuwa, Ka zauna mana Baba."
Ya zauna yana satar kallon Omar da yake cin indomie kamar bai san ma ya shigo ba. Gaisawa suka yi da Didi ya ce, "ya kike ya sana'ar taki? Fatan komai Lafiya."
"Lafiya lau Baba, É—azu nake zancen gobe juma'a zan zo mu gaisa in sha Allah."
"Allah sarki, Allah ya baki ladan niya." Ta amsa da amin ya kalli Omar ya ce, "Omar ina kwana."
Wani iri Didi taji na rashin jin daÉ—i ganin babban mutum kamar Baba Adamu shine yake gaishe da Omar. A sanyaye ta kalli Omar da kamar bai ma ji abinda aka ce ba ta ce, "Omar magana ake maka, ka gaishe da Baba."
In bowl É—in da yake hannunsa ya amsa shima ya amsa. Didi ta ce, "Omar!."
"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba.
"Baka ji abinda nace ba ne?."
"Naji mana."
"To ka gaishe shi." Ya kalle ta ya ce, "bazan ba."
Zata sake magana Baba Adamu ya girgiza mata kai alamun tayi shiru ya kalle shi ya ce, "Omar ina kwana." Nan ma ya sake yi masa banza Didi zata yi magana Omar ya ce, "Bana iya girmama wanda bai girmama mahaifiyata ba, bana iya girmama wanda bai tashi nuna min mu masa bane sai da haƙora talatin suka fito a bakin mu. Kar ki ɓata bakinki Didi, kema kin san bazan yi ba."
Baba Adamu ya ce, "Omar kayi haƙuri, kuskure ne an yi shi a baya kuma na nemu afuwar ku."
"Ita wacce ƙasa ta rufe idonta fa, itama ka nemi afuwarta ne?"Omar ya faɗa yana kallonsa da rikitattun idanunsa. Baba Adamu ya ce, "Ina yi mata addua'ar samun gafara a wajan mahaliccinta." Omar ya ce, "yadda bakwa son mu wallahi nima bana son ku, yadda ku ka wulaƙanta mahaifiyar mu dan kawai tana auren mahaifin mu babu wanda zan iya ganin darajarsa wallahi, kum...."
"Omar!" Didi ta katse shi da ƙarfi tana kallon sa.
Kallon ta yayi sai ya fasa faɗar abinda zai ce kuma bai tashi daga inda yake ba, dan bai isa yazo ya same shi ya tashi ya bar masa wajan ba. Baba Adamu ya ce, "ƙyale shi Aisha. Daman magana ce nazo da ita akan sabon company na da na buɗe, in Omar ɗin yana so sai yazo mu fara aiki gabaɗaya." Kallon ƙasan ido ya yiwa Baba Adamu kamar zai yi magan sai ya fasa ya cize bakinsa cikin ƙunar zuci.
Didi ta washe baki ta ce, "Lah yaushe aka buÉ—e Baba?."
"Satin da ya wuce."
"Allah ya sanya alkhairi ya sa albarka, Me zai hana ya zo? Zai ma yi aikin...."Â
"Gwara na koma bara akan titi da dai nayi aiki a ƙarƙashinsu wallahi" Omar ya katse a yana ɗaga mata hannu.
Zata yi magana ya ce, "Didi! Ke kin san waye ni, babu ɓoye-ɓoye, babu kare, wallahil azim bazan yi ba. Wato nayi aiki a ƙarƙashin su a samu damar wulaƙanta ni a zage ni ko? Kema kin san bazai yu ba, ai ko rahama ake rabawa a company na amince ta wuce ni na samu a wani wajan daban. Hanyar samun ta ai yawa ne dashi."
Baba Adamu ya ce, "babu laifi Omar. Amma duk lokacin ka ji kana da ra'ayi ƙofa buɗe take, Kuma har abada baza ka taɓa goge mu a rayuwarka ba, mu ɗin dai mu ne gatanka saboda mu ne jinin mahaifiyarka."
Omar ya taɓe baki ko kaɗan baya jin nauyi da girman Baba Adamu duk da ya girma sosai. Ya ce, "Allah ne gatan mu gaba da baya, babu wata halitta da zata zama gatan mu a duniya in ba Allah ba." Murmushi Baba Adamu yayi dan ya san shine ya jawo kuma ya san halin Omar da shegen riƙo da taurin kai, shekara sama da goma sha ana abu ɗaya amma har yanzu yaƙi sakin jikinsa.