← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 54

Sashe 34

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falo ta zauna shima ya zauna yana kallon ta ya ce, "Ina tambayarki, me ki ke yi a wajansa har kina yi masa murmushi haka?." Narma ta kalle shi ta ce, "ba na faɗa maka abinda ya faru ba akan ƙwacen waya? Tun daga nan na gane yana da kirki shine mu ke gaisawa. Kuma jiya ne da ya kaini shopping complex ya yi mantuwa a mota shine na bashi."

"Kawai dan ya taimake ki sai ki fara sakıin jiki dashi? To daman taimakon ki a dolensa ne ko baya so, saboda aikinsa ne, biyansa aka yi dan ya kula dake. Ki san matsayinki Beb, ke fa ba gama garin mutane bace you have to know that."
"Na sani, kuma ni ba wani abun ne ya kaini wajansa ba."
"Gaskiya ya kamata ki koma gida, zaman Kanon ya isa haka tunda dai an gama bikin da ya kawo ki. Ta ya zaki dinga tsayawa kusa dashi kina yi masa murmushi kamar wani mate ɗinki?. He's just your driver, driver ɗin ma ɗan daba shashasha, mara ilimi, ƙazami, jahili ne wanda bai san komai ba sai...."

Narma bata san ta katse shi ba ta ce, "Ashraf stop please! na faÉ—a maka dalilina na zuwa wajan sa why are you insulting him like that?."

Da mamaki yake kallon Narma ya kafa mata ido ya kasa koda motsa idon yana kallonta, sai a sannan ta fahimci abinda ta ce cikin mamakin kanta ta kalle shi itama kafin tayi magana ya ce, "just because i insulted him that's why you are upset?." Jin a yadda ya yi tambayar cikin jin haushi sai ta ce, "Ba haka bane, kawai bana so ka dinga yi min faÉ—a ne akan abinda na faÉ—a maka dalili. Ka san wacece ni ai, na san abinda zan yi."

Shi dai mamakin ta yake yi sosai dan Narma tana neman canjawa daga yadda ya santa, amma sai bai nuna ba ya ce, "Well, is okay" ya faɗa cike da jin haushi yana ƙoƙarin miƙewa. Riƙe hannunsa ta yi ta ce, "Are you upset?." Miƙewa tsaye ya yi itama ta miƙe tana riƙe da hannun sa ya ce, "kin nuna min driver ya fi ni a wajan ki Narma." Ta buɗe idanu ta ce, "haba Beb, what are you saying? Ni ban haka nake nufi ba."
"No! driver ki ya yafi ni, you show me my limit. Saboda na zage shi ki ke yi min shouting ko?."
"Sorry beb, ba haka bane" ta faɗa da shagwaɓe tana kallonsa.

Lumshe ido ya yi kafin ya buÉ—e ta kwanta a jikinsa ta ce, "kar ka ji haushi, i'm sorry." Hugging É—inta back ya yi na wasu seconds kafin ta janye jikinta tace, "Smile." Murmushi ya yi yana kallon ta ya ce, "I love you." Itama murmushi tayi ta ce, "I love you too." Waya ya É—auka ya yi musu selfie suka yi kyau kuwa kafin ya kalle ta ya ce, "ina zaki je yau?."

"Babu ko ina, na gaji kaina na ciwo so bana son fita."
"Okay yanzu zan je wani aike da Abba ya yi min, so in na dawo zan dawo." Murmushi ta yi ta ce, "okay sai ka dawo." Har bakin mota ta raka shi ya shiga ya fita ita kuma ta koma ciki.

Omar lokacin da ya koma Didi tana a falo zaune ya shiga shima ya zauna ya ce, "ya jiki?." Ta kalle shi ta ce, "da sauƙi Omar." Ledar hannunsa ya miƙa mata ta karɓa ya ce, "jiya na kai yarinyar can wani kanti sai na siyo miki, na san ki da son turare da kuma son milo."

Murmushi tayi ta buÉ—e turarenta ga kuÉ—in sa a jiki naira dubu talatin da uku ta ce, "Omar wannan turare mai tsada haka?."
"Eh, ki dinga fesawa in sirikina zai zo." Dariya tayi ta ce, "Ka raina ni." Shima murmushi ya yi kafin ya ce, "Ya maganarsa kuwa?."

"Sun gama magana da Kawu to rashin lafiyar nan tawa ban sammu mun tattauna sosai ba, ko mai yake faruwa zan faÉ—a maka." Kai ya girgiza kafin ta kalle shi ta ce, "Omar yaushe ka iya mota?." Murmushi ya yi É—an daman ya san sai ta tambaya, ya gama sanin halinta ko wanne motsi in ta yi zai fahimci me take nufi kamar yadda ta sa nasa. Ya kalle ta yaga shi yake kallo, kafin yayi magana ta ce, "Omar kana bani tsoro fa, a ina ka san Sen har ya baka Æ´arsa kana yawo da ita?."

"Didi" ya faÉ—a yana gyara zama ya kalle ta sosai ya ce, "na san abinda nake yi fa, kar ki damu kanki." Ta ce, "nima ban ce baka sani ba Omar, amma abubuwan ne suke bani mamaki sosai."
"Kar ki damu, babu komai sai alkhairi."
"Allah ya sa hakan" ta furta tana buɗe turaren dan ya yi mata ƙhamshi sosai. Bai sake magana ba ya tashi ya fita itama bata sake cewa komai ba saboda kanta ya fara yi mata ciwo.

Da daddare Hajja ta shigo ita da Nayla da Salma dan su duba Didi, kamar ko yaushe yana zaune a falon shi da ita duk da ba hira suke ba ita tana abinda yake gabanta shi kuma yana ta danna waya.

Sallamar su ya saka suka kalli masu shigowa Didi da fara'a ta ce, "Hajja kece da kan ki?." Hajja ta ce, "Aisha an ce baki da lafiya harda su kwnaciya a asibiti ai dole nazo."
"Sannu da zuwa" ta faÉ—a da fara'a tana kallon Hajja. Hajja ta zauna suka gaisa da Didi kafin ta kalli Omar suka haÉ—a ido ta ce, "Omar Faruku mazan fama, ja daku ba dai rago ba. Wannan hakimcewa da ka yi a falo sai ka sa a É—auka mai gidan ne ai."

Samun kansa ya yi da sakin murmushi mai sauti haka kawai yake jin farin ciki a zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba, ya kalli Hajja ya ce, "Ina yini."
"Lafiya lau Ummaru, Na É—auka ai baka ganni ba da naga ka É—auke kai." Bai ce komai ba kuma fuskarsa bata bar murmushin ba.

Nayla suman zaune tayi ganin yana murmushi a karo na uku da ta ga yana yi, sai taji ƙirjinta yana sama da ƙasa wani irin abu yana fizgar ta zuwa gare shi kamar ta saka igiya ta jawo shi haka take ji. Daƙyar ta iya ɗauke ido daga kansa suka gaisa da Didi kafin ta kalle shi ta ce, "ina yini." Jin ta gaishe shi sai Salma ma ta gaishe shi ya ɗago ido ya kalli Nayla da take kallon sa kamar zai amsa sai ya yi shiru.

Hajja ta ce, "Kana ji ana gaishe ka fa."
"Ni bana son gasuwa ni kam, Lallai sai an gaishe ni?" Ya faÉ—a yana kallon Hajja kafin ya kalli Didi. Hajja ta kalli Nayla ta ce, "to kin ji sai ki daina gaishe shi. Daman ai dodon ki ne ko yaushe cikin tsorataki yake." Didi ta ce, "Omar meye haka? Gimamawa ce zata saka a gaishe ka, kai wanne irin mutum ne da komai baka so?."

Salma ta taɓe baki cikin jin haushi, daman in banda karanbani irin na Nayla ina ita ina gaishe shi? Gabaɗaya haushin kanta take ji da ta biye mata itama ta gaishe shi, ita kuma tayi haka ne saboda kar Hajja tayi mata faɗa tace bata gaishe shi ba.

Hajja ta ce, "ƙyale shi, wataƙila in ya amsa ɗin ma tsoro zai bawa Hauwa'u." Nayla ta sauke ido ƙasa zuciyarta babu daɗi akan abinda ya yi mata, amma bata gajiya za kallon sa daƙyar ta iya sauke idon ta ƙasa.

Nayla ido na ƙasa ta ce, "daman in an gaishe shi baya amsawa."

Kallon wacce Hajja ta nuna da Hauwa'u ya yi yaga Nayla ce ta sunkuyar da kai sai yaji wani iri a ransa kamar bai kyauta ba, ɗauke kai ya yi daga kallon ta ya kalli Didi da take kallon sa ya ce, "Lafiya lau, shikenan na amsa ko? To ki daina hararata" ya faɗa yana miƙewa ya fita daga falon.

Hajja tayi dariya ta ce, "ja'irin yaro, zan ga matar da zaka aura ai, sai na fara yi mata huɗuba na zama da kai kafin ta shigo, dan Omar jarbin ƙwai ne jansa sai me nutsuwa." Didi ta ce, "Ai Hajja dodo da donanniya zamu haɗa kawai" ta faɗa tana kallon Nayla cikin wasa tana dariya.

Hajja ta ce, "shikenan ba, ayi maganin tsoro da rashin son gaisuwa." Suka yi dariya gabaÉ—aya yanzu har Nayla. A baya in aka yi irin wannan maganar haushi take ji, amma yau sai taji daÉ—i a zuciyarta har tana murmushi zuciyarta na taya ta murmusawa. Basu jima sosai ba suka yi mata sallama suka tafi bayan Salma tayi mata allura.

Basu jima da fita ba aka yi sallama tare da shigowa falon. Da mamaki Didi take kallon wacce ta shigo ta ce, "wa idona yake gani kamar Barr Nass?." Narma tayi murmushi ta ƙaraso ta ce, "ni ce." Didi ta ce, "ki zauna mana."

Narma ta zauna tana kallon Didi itama ita take kallo ta ce, "Sannu da zuwa."
"Yauwa, ya jiki?."
"Jiki da sauƙi na samu lafiya, Bara na kawo miki ruwa."
"Ki barshi kawai, daman cewa nayi bara nazo na gaishe ki na barki babu lafiya." Didi taji daÉ—i sosai a ranta tace, "kai amma na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci." Ta amsa da amin.

Didi ta ce, "yanzun nan kuma ya tashi amma na tabbatar yanzu zai dawo." Kafin Narma tayi magana suka ji sautin murya sa yana magana dasu Bash tare da shigowa falon. HaÉ—a ido suka yi da Narma tayi masa alamun hiii da hannu, ya kalli Didi da take murmushi ta ce, "yanzun nan yazo, ta ce ta zo gaishe ni."
Chapter 34 · 0% Book details