← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 54

Sashe 42

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Narma ta ce, "A Kano yake, kuma yanzu na samu labarin baya jin daÉ—i Ina so naje na duba shi Mum." Mum ta bita da kallo mamaki ta ce, "anya shima yana sonki kuwa?."
"Yana sona sosai Mum, yana sona. Tunda Dad baya nan gobe da safe zan je Kano zuwa jibi sai na dawo kin ji Mum?." Mum ta bita da kallo cikin tausayin yanayin da take ciki ta ce, "is okay, sai Najwa ta rakaki."

"No Mum bana so kowa ya ganshi mamaki nake so na baku, ni kaÉ—ai zan je." Mum ta ce, "shikenan dai. Amma jibi zaki dawo da safe, kuma ban amince da wannan Tiger É—in matsayin driver ba. Ki kira drivern Kano su zo su É—auke ki ki gama abinda zaki yi ki dawo kin gane?." Jin abinda Mum ta ce sai gabanta ya faÉ—i, amma da yake an barta zuwa Kano bata damu ba ta amince da hakan.

"Kar ki damu Daughter, zaki auri wanda ki ke so kin ji?." Kai ta É—aga cikin farin ciki Mum tayi hugging É—inta tana rarrashi kafin ta fita barta. Narma tana fita ta tashi ta kalli kanta a madubi tana so ta gane itace ko kuwa ba ita bace, domin ta san ta canja, halayya ta da kamanninta duk sun canja saboda Omar. Mamaki take yi wai daman zata iya fara soyayya da wanda bai ma san tana yi ba? Soyayyar ma kuma da mutum irin Omar. Itace fa Narma da maza suke so ta yi musu replying message balle kuma ta yi magana dasu, amma ga Omar ya haukata ta lokaci É—aya ta fita daga hankalin ta.

Ajiyar zuciya ta yi ta lumshe ido tayi tana sake buÉ—e ido a bayyane ta ce, "Faruk gani nan zuwa."

        Washe gari.

Jirgin ƙarfe takwas ta hau dan haka da wuri ta shiga kano, tana fitowa taga Yahya wanda ya san da zuwan ta tun a daren jiyaa. Gida aka kai ta daƙyar ta iya haƙura aka yi sallar azahar ta hau mota ta nufi gidan Didi kai tsaye. Sai da taje ƙofar gidan sannan ta kira Omar a waya.

A lokacin yana kwance a É—aki abubuwa sun yi masa yawa, ya kasa gane abinda ya damunsa gabaÉ—aya wani irin yanayi ya damu zuciyar shi da gangar jikinsa.

Kiran ta ya shigo wayarsa ya kalli wayar, bai yi saving ba amma ya gama haddace ƙarshen number ta ko dan kiransa da take yawan yi a kwanakin nan ne bai sani ba. Kai ya dafe bai ɗauka ba yana kallo har ta katse, wani kiran ya sake shigowa kamar bazai ɗauka ba sai ya ɗauka.

Narma da ta fara kuka yana ɗauka ta ce, "Faruk Ina ƙofar gidan ku." Da hanzari ya miƙe zaune ya ce, " ki ka ce?."
"Uhum, Ina ƙofar gidan ku."
"Me kika zo yi gidan mu?."
"Ina kiran ka baka É—auka shiyasa nazo." Kasa magana ya yi ya tashi ya fita ya kuwa hango motar ta a ajjiye a gefe, ganin sa sai ta buÉ—e motar ta fito.

Kallon ta ya yi itama shi take kallo ta ɗauki wayar hannunta sake kiransa ya ɗauka ta ce, "na ƙaraso ko zaka zo mota mu yi magana?." Omar yace, "meyasa kika zo?." Narma tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Da yake yana kallon ta tana kallonsa sai ya ce, "ki koma gida zan zo."
"Na san ba zuwa zaka yi ba" ta faÉ—a tana yanke wayar ta nufo gidan, yana kallon ta tana tahowa zuciyar sa cike da tsoro da kuma tsantsar mamakin zuwan ta gare shi.

Sai da ta shigo gidan sannan ta zuba masa ido tana kallon sa ko kofta ido bata yi. Numfashi ta sauke ta kawar da kai gefe tana jin haushin zuciyarta da ta saka ta fara son wannan mutum mai shegen shariya da nuna ko in kula kamar sa.

Narma ta kalli gidan ta ce, "Sister fa?."
"Bata nan" ya bata amsa babu ɓata lokaci dan ya ƙagu ya ji abinda tazo dashi. Tayi shiru bata ce komai ba, hakan ya saka ya ce, "Ina jinki, me ya kawo ki Kano har kika zo nan?. Kar ki ɓata min lokaci ki faɗi abinda yake ranki."

"Babu abinda ya kawo ni Kano, na zo Kano saboda kai kuma saboda kai zan koma." Narma ta gyara tsayuwa tana kallonsa ta ce, "ban san me zan ce maka ba, ban iya ɓoye-ɓoye ba haka zalika ban san wani abu tsoro ba indai a kan abinda yake zuciyata ne. Abinda na sani kawai Ina sonka Faruk! Ina sonka so na Aure!."

*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.

Nana Haleema❤️

*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025

©️ *Nana Haleema.*

Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.

*Book 1*
*P 20.*

Wani irin dumm Omar yaji a zuciyarsa, ya zubawa fuskarta ido yana kallo ba cikin mamakin da ya gama É—aure masa jiki. Ya kasa motsi sai kallon idanunta da yake yi kamar yadda take kallon sa. Narma tayi murmushi tare da hawaye ta ce, "kayi mamaki ko?." Sai ta girgiza kai ta ce, "nima kwana nake Ina mamaki, kwana nake Ina tambayar kaina Narma ta ya hakan ya faru. Kullum tambayar kaina nake yi Narma meyasa ki ka shiga wannan rayuwar, meyasa ki ka fara son wanda bai damu dake ba. Da wannan tunani nake kwana nake tashi tunda na bar garin nan har yau da nake tsaye a gabanka."

Narma ta ce, "Ina sonka, Ina sonka!. Ban san me zan ce maka ka yarda ba amma abinda nake ji a raina kawai Ina so nayi rayuwa da kai a matsayin mijina, ban damu da abinda zai biyo baya ba, ina so na rayuwa da kai daga nan har a tashi duniya. Ban damu da abinda kowa zai ce ba, kawai Ina so na dinga duba gefena na ganka a tare dani ko yaushe, ban damu da kowa ba, ban damu da komai ba. Da zuciyata kawai na damu, abinda yake cikinta kuma soyayyar ka ce, Ina son ka!" Ta faÉ—a tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta.

Kai ta girgiza tace, "ba wasa nake yi ba wallahi, zan iya aurenka na zauna da kai a ko wanne yanayi. Please Faruk! ka amince dani as your life partner, wallahi ina sonka!" Abinda take faÉ—a kenan kamar zata zubar da hawaye. Bai yi zato ba, bai yi tsammani ba, ya tafi duniyar tunani kawai yaji ta kwanta a jikinsa ta rungume shi sosai tana kuka.

"Innalillahi!" Ya furta a bayyana yana riƙe hannayenta ya janye ta daga jikinsa ya ce, "Narma!."  Kallon sa tayi karo na farko da ya kira sunan ta, bata ɗauka ya san sunanta ma tunda bata taɓa ji ya faɗa ba sai yanzu. Hasalima bashi da sunan da yake faɗa mata tunda ba magana yake yi mata ba.

Ganin irin kallon da yake mata ya yi kama da na fushi da fusata sai jikinta ya yi sanyi. A kausahe Omar ya ce, "Ki bar wannan abin da kike yi, Ko da wasa kar ki sake kuskuren cewa zaki riƙe ni, bana son wannna shirmen kin fahimta!?" Ya faɗa a fusace yana nuna ta da yatsa. Kai ta girgiza ta ce, "I'm sorry!."

Omar ya ce, "Sannan ki koma gida, ki bar cikin gidan nan yanzu. Abinda ki ke so baza ki same shi daga gare ni ba." Narma ta narke fuska ta ce, "Kana nufin baza ka iya sona ba?." Ya É—aga mata kai alamun eh kana ya ce, "in ma wasan kwaikwayo kika shirya ki dakatar dashi bazai yi tasiri a kaina ba. Kar ki sake zuwa cikin gidan nan ba tare da kin sanar dani ba, bana so na sake ganinki, ki fita daga gidan nan kafin na nuna miki asalin waye ni."

Kallon sa kawai Narma take yi jin yana ambatar wasan kwaikwayo, yanzu kenan soyayyar da take yi amsa ce ya É—auka wasan kwaikwayo ko bayyana masa É—in da tayi ne ya zama wasan kwaikwayo?.

Narma murya na cracking ta ce, "Wallahi Ina sonka, wallahi i'm ready to marry you. Ban damu da abinda zai biyo baya ba indai zan samu cikar burina na amince zan zauna da kai a ko wannan yanayi."

Kuka take yi mara sauti duk sai ta sake dagula masa lissafi, shi bai san da wacce makama zai ɗauki maganarta ba dan shi gani yake kamar akwai abinda ta shirya shiyasa ta zo masa da wannan maganar. In ba haka ba kai tsaye tazo ta furta tana son shi kamar ba mace ba? Macen ma irin ta mai aji da kuɗi da mulki na siyasa? Ta ya zai amince da wannan tatsuniyar mai kama da wasan yara?. Kuma shi wata mace bata taɓa kallon sa ta furta masa wannan kalma ba, bai taɓa tsayawa da wata mace na adadin mintinan da yake tsaye da Narma ba. Shifa Didi kawai ya sani, itace komai na sa, Bai taɓa alaƙantuwa da ko wacce mace ba in ba ita ba. Shiyasa yake jin kansa uncomfortable saboda ita ce mace ta biyu a rayuwarsa da ya samu kusanci da ita, da ita ya taɓa haɗa jiki, da ita ya taɓa tsayawa suna doguwar magana, da ita ya fara zama waje ɗaya shida mace, itace ta fara furta masa kalmar so a rayuwarsa. Jin kansa yake yi yayi nauyi, nauyi yake a zuciyarsa dan yanayin ya zama baƙo a gare shi.
Chapter 42 · 0% Book details