← Book details Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 54

Sashe 39

Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shirin shiga mota ta hange shi ya fito daga gidan yana kalle-kalle da alama Didi yake nema, hannu Didi ta É—aga masa sai ya É—aga kai alamun ya ganta ya juya bai sake kallon kowa. Nayla ita hakan ma ya yi mata, ko babu komai ta ganshi kafin tafiyarta Kaduna. Bayan motar ta buÉ—e ta shiga tana yi musu sallama suna yi mata addu'a ya ja motar suka bar cikin unguwar zuciyarta sam babu daÉ—i.

•••••••••

"Dad zaman Kano ya yi min daÉ—i sosai, I feel like na sake komawa cikin kwanakin nan" ta faÉ—a tana cin Apple. Mum ta kalla kafin ta ce, "Mum wai ya ba ku je Paris É—in ba?." Mum ta ce, "mun fasa."

Sen ya kalli Narma ya ce, "Tunda kin dawo lafiya haka nake so. Tiger ya kira ni tun jiya yana shaida min kin taho babu abinda ya same ki." Narma sai ta saki murmushi jin an ambace shi ta ce, "Classy boy kenan!." Da Sauri Mum ta kalle ta jin abinda ta ce taga murmushi ma take yi. Mum ta ce, "I hope bai cutar dake ba?."
"Babu abinda ya yi min, ya kula dani sosai fa Mum." Mum ta sake kallon ta tace, "amma da farko ai ya raina ki, yana ganin kanku É—aya dan kuna haÉ—a numfashi dashi a mota, yanzu a ina zai ganki ma balle ku zauna mota É—aya?."

Dad ya ce, "bai isa ba wallahi, ita dashi ai sai dai taimako shima ba daga hannunta ba, sai dai daga hannun personal assistant É—inta." Mum ta ce, "Yana da jin kai yaron kamar wani É—an sarauta, yana talaka, illirate, useless and dirty ya dinga irin wannan abun. I so much hate him wallahi, just imagine nonsense like him sayiing he won't open the car for her. Oh God! har yanzu na kasa mantawa da abin nan. Shi ba abin alfaharinsa bane ace ya buÉ—e mata mota? Talaka bashi da hankali sam, talakan ma irin sa jahili da bai san komai ba."

Dad ya murmusa ya ce, "saboda Æ´an iska irinsa na garin Kano ya saka na haÉ—a ta dashi, gashi kuma ta dawo lafiya." Mum tace, "kana ganin scar mark É—in hannunta kana cewa ta dawo lafiya? Ta dawo dai babu laifi amma ba lafiya ba."

Narma gabaɗaya bata jin daɗin zagin nan da suke yi masa ko kaɗan. Dad ya kalle ta ya ce, "block his number then delete it, Matsayinsa bai kai ya samu number ki ba kin gane?." Narma gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ta ɗauki wayar ta miƙe tsaye ta ce, "Okay Dad" abinda tace kenan ta hau sama zuciyarta a cushe cikin jin abinda iyayen ta suke faɗa akansa.

••••••••

Nayla basu shiga ba sai la'asar, a gajiye take tana shiga Jalil da suke kira aura ya ɗafe ta yana muryar ganinta. Dariya take yi ya riƙe jakarta ya shiga da ita. Drivern ya kai mata kayan zuwa cikin falon. Abiy ta samu a zaune yana kallonta da murmushi sai ta saki fara'a ta ƙarasa wajan sa ta zauna akan carpet ta ce, "Abiy na." Yayi murmushi ya bata hannu suka gaisa ya ce, "Ummina kin dawo?."

"Na dawo Abiy. Barka da yamma."
"Barka dai Mamana, ya hanya?."
"Lafiya lau Abiy. Na same ku lafiya?."
"Lafiya lau. Ya ki ka bar Hajja?."
"Hajja tana nan lafiya, tana gaishe ku." Mama da take kallon ta ta ce, "Nayla sannu da zuwa." Kallon Mama tayi ta ce, "Mama nayi kewar ku wallahi." Mama ta ce, "ai gashi kin dawo."

Baban Yayan su ne ya shigo da suke kira da Yaya ganin Nayla sai ya ce, "A'a mutanen Kano, saukar yaushe?." Ta kalle shi ta ce, "yanzu na dawo Yaya. Ina yini."
"lafiya lau Nayla, ya Hajja?."
"Tana gaishe ku." Nayla ta ɗauko saƙon Abiy ta bashi, bawa Mama nata saƙon. Abiy yana ta murmushi ganin gurar kano mai kyau kana gani ka san sabuwa ce ta saka yi masa. Ga Dambun nama a cikin wani ƙaramin bokiti. Yana ta murmushi yana sake girmama matsayin Hajja a wajan sa.

Mama ta buɗe nata kayan ta ga girki ne su kuka da kuɓewa da daddawa. Mama ta yi godiya tana ta murmushi. "Twiny." Nayla jin abinda akace ya saka ta kalli wacce take shigowa ta ga Jidda ta ce.

Nayla ta ce, "Twiny yaushe ki ka zo?." Ƙarasowa tayi ta zauna kusa da ita ta ce, "Jiya nazo. Kuma guess what? Kano zamu koma da zama." Wara idanu Nayla tayi ta ce, "da gaske?."
"Wallahi da gaske, Ke dai ki je ki huta zan shigo mu sha labari." Nayla ta kalle ta tana cewa, "gaskiya bana so ki bar Kaduna, in kika koma Kano ya zanyi?." Jidda ta riƙe hannunta suka yi ciki suna hira. Murmushi Abiy ya yi yana jin daɗin zumuncin da yake tsakanin ƴaƴansa, duk da Nayla ce kaɗai ba uwa ɗaya suke da sauran ba amma in ba sani ka yi ba bazaka banbance ba uwa ɗaya ce ta haife su ba.

Kowa ya san Jidda da Nayla tasu tafi zuwa É—aya saboda sa'anni ne kuma masu suna iri É—aya. Kwana goma sha huÉ—u Jidda ta bawa Nayla, tare suka tashi komai tare. Komai tare suke yi Aure ne Jidda ta riga Nayla shine abinda ya raba su.

Da daddare suna zaune akan dining da Abiy da Mama da Nayla, Jidda, Jalila, Jalil autan, Yaya Jawad wanda Nayla ke kira da Ya J. Hirar Kano kawai ake yi suna dariya kafin Abiy ya kalle ta ya ce, "Kin dai je Kano hankali ya kwanta." Nayla tayi murmushi ta ce, "Gidan Hajja akwai daÉ—i Abiy."
"Ai dole ya yi miki daÉ—i Nayla. Yaushe zaki fara aiki ne? Ko school ki ke so ki koma?" Sai ya kalle ta sosai ya ce, "Ko kuma aure?."

Gabanta ya faɗi, a da in an yi zancen aure bata jin faɗuwar gaba, amma yanzu ta rasa dalilin faɗuwar gaban da take ji ko yaushe. Nayla ta kalli Abiy ta ce, "duk wanda Allah ya zaɓar min Abiy? Amma nafi so na fara aiki tukunna."

Abiy ya ce, "Alright, zaki fara a cikin kwanakin nan in sha Allah." Nayla ta yi murmushi sannan ta kalli Yaya Jawad ta ce, "Yaya J aiki da wahala ko?." Dariya ya yi ya ce, "ɗauka ki ke sauƙi ne dashi? Hmm zaki gani yarinya." Abiy ya ce, "ƙyale shi tsorata ki yake yi." Tayi dariya tana cin abinci amma zuciyarta tana Kano musamman gidan Didi, a gidan Didin ma Omar take tunani.

Abiy ya ce, "Amma maganar aure ma ya kamata ayi ta Mamana, bayan tafiyar ki ina ta samun masu neman aurenki, harda Abbas cousin É—inki." Gabanta ya faÉ—i sosai ta wara ido ta ce, "Abiy Ya Abbas yazo nan?."
"Yazo. Ya tabbatar min da yana neman auren ki ko ke bai sanarwar da yana sonki ba. Hakan da ya yi ya min daÉ—i sosai, duk da É—an uwanki ne amma bai nemi soyayyar ki kai tsaye ba ya biyo ta wajena."

Nayla tayi shiru gabanta yana faÉ—uwa sosai ta ji Abiy ya ce, "yana da kyau ki yi tunani, zan basu damar magana dake dan mutane uku kenan har Abbas. Kin ce a ajjiye batun Sadiq ko? To an ajjiye, bayan shi akwai uku har Abbas yayan ki. Bana son yawan tara samari kema kin sani, ya kamata ki san abinda zaki yi. Abinda ya jawo rabuwarki da Jidda kenan, dan haka kema yazo kan ki, ki nutsu ki yi addu'a."

Nayla jikita yayi sanyi ta kalli Abiy ta ce, "to Abiy, ka taya ni addu'a."
"Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi Mamana." Suka amsa da amin kafin ya ce, "ina jin next week sai muje umra ko kwana goma mu yi sai mu dawo." Ihu suka yi cikin murna, Abiy ya yi murmushi ya tashi ya hau sama. Yana jin daɗi in yaga iyalansa suna farin ciki, hakan yana ƙara masa jin daɗi a zuciyarsa.

*Bayan Kwana biyu.*

Omar ya yi ƙoƙari ya yakice tunanin Narma ya koma sabgoginsa, baya bari tunaninta ya hana shi wani abun dan tun bayan tafiyarta basu sake koda waya ba, hakan kuma ya yi masa daɗi dan baya son abinda zai hana zuciyarsa sukuni.

Ɓangaren Narma duk yadda tayi ta jure share Omar ta kasa, tayi-tayi amma abin ya girmi tunaninta. Har ta kai ta kawo ta fara ware kanta a gida da wajan aiki, saboda gabaɗaya bata son magana sai aikin tunaninsa da ganin fuskar Omar a idonta. Ta rasa meyasa take jin abinda take ji a kansa, gabaɗaya ta kasa sarrafa kanta akan tunanin Omar.

Yau ta kama Sunday bata je aiki ba tana kwance a É—aki sai ga Mum ta shigo, ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce, "Narma tashi zaune." Ba musu ta tashi ta kalle ta ta ce, "me yake damunki? Tunda kika dawo daga Kano baki da walwala, me ya faru?." Narma ta ce, "babu komai Mum, kawai bana jin daÉ—i ne."
"Kin je asibiti ne?." Ta girgiza kai alamun a'a, Mum ta ce, "meyasa baki je ba?."

"Zan je Mum." Mum ta ce, "good. Yanzu ki zo ga Ashraf nan a falo yana jiranki" Mum tana faɗa mata haka ta fita. Haushi taji ya tokare mata zuciya jin wai Ashraf ne yazo. Yanzu ta rasa meyasa yake ɓata mata rai, haushi yake bata yanzu, kwata-kwata bata son magana dashi. Ɗankwali kawai ta ɗaura ta fito falon cikin shigar ta kullum ta same shi a zaune, yana ganin fitowar ta ya miƙe tsaye har ta ƙaraso ya ce, "Why Narma? Bakya picking calls ɗina, bakya responding messages ɗina. Me yake faruwa?."

Narma ta É—an yi ajiyar zuciya ta ce, "babu komai."
"akwai komai, ki faÉ—a min abinda yake faruwa. GabaÉ—aya kin canja, ko a Kano ba haka ki ke ba."
"Na faÉ—a maka babu komai, kawai bana jin daÉ—i ne, yanzu Mum tace naje naga Dr." Ashraf ya bita da kallo ganin yadda take yi masa in yazo gidan yanzu ta canja, yadda take welcoming É—insa gabaÉ—aya ta canja.
Chapter 39 · 0% Book details