Sashe 15
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba Adamu ya ce, "Aisha zan tafi, akwai abinda ki ke buƙata ne?." Didi cikin sanyin jiki ta ce, "Babu komai Baba, in akwai zan sanar da kai a waya."
"To akwai kayan abinci da nazo miki dashi, zo mu je yara sai su shigo dasu" ya faɗa yana miƙa mata rafar ƴan dubu-dubu guda biyu ta saka hannu biyu ta karɓa ta ajjiye. Omar ya kalle shi ya ce, "duk wanda ya ganni ya ganta ya san ba ma tare da yunwa." Babu wanda ya kula shi Didi ta kalle shi sannan ta bi bayan sa tana hararar Omar saboda kallon da ta ga yana yi mata.
Ba jimawa aka shigo da madara da milo da sugar da butter, kwai, taliya, doya, dankali, platain, da sauran abubuwa. A guje yaran suke ajjiyewa suna fita saboda Omar da yake kallon su daga falon.
Tana shigowa gidan yana fitowa daga parlon ya ce, "babu abinda za a ci a cikin kayan nan, ko ki mayar masa da tsiyarsa ko kuma na kwasa na zubar wallahi." Ta Harare shi ta ce, "wallahi bazan mayar ba, kuma baza a zubar ba Omar ba. Yayan mahaifiyata ne ya bani ba wani bare ba."
Da mamaki yake kallon ta ya ce, "ba gwara ace wani baren ne ya bayar akan ace shine ya bayar? Didi kar mu yi haka dake, ba za a ci abubuwan nan a gidan nan ba."
"Wallahi sai an ci!" Ta bashi amsa a kausashe tana kallonsa. Idanunsa sun yi ja saboda ɓacin rai ya kalle ta ya ce, "Akwai abinda babu a gidan nan ne? Faɗa masa aka yi yunwa tana tare damu ne da zai kawo mana wannan tarkacen?."
"Omar wai meye ya sa baka yafiya ne kai?." Ta kalle shi ganin sai wuci yake kamar zaki, idanun nan nasa sun yi ja haka jijiyar kansa ta miƙe kana kallon sa kasan ran masa ya ɓaci. "Tambayarka nake, meyasa baka yafiya ne?."
Bai iya yi mata magana ba sai wuce zai fita tayi saurin riƙo hannunsa ta ce, "Yayan mahaifiyarka ne in ka saka aka yi masa wani abun tamkar Mama ka yiwa, sannan ka tuna Mama baza ta taɓa alfahari da kai a yadda ka ke ba Omar. Zata yi alfahari da kai in ka kasance na gari, amma a haka baza taɓa alfaharin haihuwarka ba." Runtse ido yayi cikin ƙunar zuci ya zame hannunsa daga riƙon da tayi masa ya bar gidan da sauri.
Da kallo ta bishi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ya Allah ka shirya min ƙanina Omar, Allah ka yaye masa wannan baƙar zuciyar da yake fama da ita, Allah ka bashi ikon manta abinda ya riga ya wuce ya kama abinda yake gabansa, Amin." Kayan take ɗauka a hankali tana shiga dasu dan ta san in zasu shekara a wajan bazai taɓa ba, gabaɗaya jikinta ya gama yin sanyi itama, abubuwan da suka faru a baya suna yi mata yawo a zuciyarta.
*Book 1 free ne*
*Book 2&3 paid ne, akan naira 500 kacal*
*VIP group 1k*
*VIP2 on ArewaBooks.*
*domin biyan kudi ka tuntubi wannan number via WhatsApp*
wa.me/2349030398006
Dm to subscribe yours.
Nana Haleemaâ¤ï¸
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
Â Â Â Â Â Â Â Â©ï¸ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
https://chat.whatsapp.com/K8IEI39TB803y9pEtzMmdp?mode=ems_copy_t
*Book 1*
*P 07.*
*Abuja.*
Zaune suke a babban falo na alfarma su biyar suna cin abinci cikin yanga da iyayi, kai da ka gansu ka san kuÉ—i da ilimi ya gama zama a jikin dukkan su. Duba da irin shigar da take jikin Narma zaka tabbatar da wayayyun Æ´an boko ne.
Dad ya kalli Nabil ya ce, "Nabil ka san lokacin lissafi a store ya kusa ko?." Nabil ya kalli mahaifin na su ya ce, "Yes Dad, na sani."
"Ya kamata a dakata da karɓat kaya sai mun kammala lissafi."
"Okay Dad za a yi." Ya kalli Najwa ya ce, "Najwa yaushe zaki koma London?."
Najwa ya kalle shi ta ce, "Sai nan da three weeks Dad." Kafin ya bada amsa Mum ta ce, "My Dear tunda dai sun samu hutu lokaci ya yi da zamu je Paris. Akwai birthday party É—in friend É—ina, za a yi surprising É—in ta a can, so ina so nayi attending."
Narma ta kalli Mum tana turo baki ta ce, "Mum ni babu inda zan je gaskiya, beside ni Kano zan je." Najwa ta ce, "Yaya Narma wai me zaki yi a Kano ne?."
"Samra's wedding."
"Friend É—inki sai aure suke yi amma ke kin tsaya wasa." Narma tayi murmushi ta ce, "na kusa."
Mum ta ce, "to ke ki tafiyar ki Kano ni da Najwa zamu je Paris." Najwa ta ɗan ɓata rai ta ce, "Paris Mum?."
"In baza ki je ba kin huta, ai ba hanya ce ban sani ba." Najwa tayi dariya ta ce, "dole na ma." Mum ta kalli Nabil ta ce, "Nabil ka faÉ—awa Zuhra sai mu je tare, I hope Asim sun samu hutun school?."
"Yes Mum, sun yi hutu."
"Okay" ta furta tana cigaba da cin abincin ta.
Dad ya kalle Narma ya ce, "Yaushe zaki je Kano din?." Narma ta kalle shi ta ce, "Ranar Sunday zan tafi." Dad ya kalle ta ya ce, "Ranar yaushe zaku fara events É—in?."
"Wednesday."
"Okay. Narma ban da yawo ke kaÉ—ai ba, kin yanayin Kano ba wani security ne dashi ba. Dan ma kin takura ne da babu abinda zai saka na bar ki ki je." Narma tayi shiru bata ce komai na dan kar ma tayi magana a hana ta zuwa.
*Kano.*
Didi share Omar tayi dan ta san yinin ranar a ɓacin rai zai yi shi in tace zata biye masa itama ranta ne zai ɓaci. Aikace-aikacenta ta cigaba da yi gabaɗaya abubuwan da suka wuce suna yi mata yawo a kanta, duk yadda ta so ta kawar itama ta kasa hakan ya sanya idanunta zubar hawaye tunawa da iyayen su da suka rasa a shekarun da suka wuce.
Bata sake tunanin Omar ba dan ta san bazai dawo ba ransa a ɓace yake da ita sosai ta fi kowa sanin hakan. Ta kuma san in ba dan ita ɗin babu babu halittar da yake ɗagawa ƙafa, shi bai san kara ba, bai kuma son alfarma ba. Haka ranar ta yini sukuku bai dawo ba har yamma, ko da ya shigo bai ce mata komai ba daman ta san bazai ce ba ɗakinsa ya shiga bai jima ba ya fito ya sake fita.
Sai bayan sallar magriba kamar yadda ya saba shigowa ko yaushe sannan ya shigo kamar baza ta yi masa magana ba ganin ya haɗe rai sai kuma ta ce, "Baza ka ci abinci ba ne?." Kallon ta yayi yana shan ruwa ya ce, "Na daina cin abincin gidan nan har sai abinda ya kawo ya ƙare." Ta rausayar da kai ta ce, "Omar! Omar!! Wai wacce irin zuciya ce da kai ne don Allah?."
"Wacce Allah ya yi min Didi."
"Shikenan naji. Amma abinda na dafa yau ko abu ɗaya a cikin abinda ya kawo ban taɓa ba. Kazo kaci abincin ka." Ya kalle ta alamun bai yarda ba ta ce, "da gaske nake, ka san ai bazan maka ƙarya ba. Ka je ka ɗauko abincin, ka kira su Tukur su ci ga na su." Shiru yayi kamar zai ci ɗin sai kuma ya girgiza kai ya ce, "su dai zasu zo su karɓa, ni kam bazan ci ba."
Duk sai Didi ta damu a tausashe ta ce, "in baka ci ba me zaka ci?."
"Assalamu alaikum, Damisa na dawo." Jin muryar Bashir a cikin yaransa ya saka shi ya fita tsakar gidsa sai ga shi ya dawo da packs da alamun abinci aka siyo masa. Didi ta kalle Bashir ta ce, "Bashir ku zo ku É—auki abinci." Bash ya ce, "An gama babbar Yaya, godiya mu ke Allah ya saka da alkhairi." Kitchen É—in ta shiga ta É—auko musu ta bashi shi kuma ya fita.
Lokacin da ta dawo ta tarar grill tilapia fish ne da chip a cikin pack É—in irin mai sauce É—in nan da ake siyarwa yana ci hankalin sa kwance. Daman ta san shi masoyin kifi ne sosai, bai damu da cin nama ba akan yadda yake son cin sa ba. Numfashi ta sauke ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ta zauna akan kujera.
Wani pack ɗin taga ya miƙo mata sai tayi murmushi, daman ta san bazai taɓa siyan abu bai siya da ita ba, koda a waje ne in ya ci itama sai ya kawo mata. Ganin bata karɓa ba sai ya ajjiye mata ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya maganar saurayinki?."
Dariya ya bata sosai, wai saurayinta a ganin ta ai sai dai ace bazawari ba saurayi ba, ita mantawa da take itama tana cikin sahun wanda za a kira da budurwa. Ganin tana dariya sai ya kalle ta ya ce, "me ya baki dariya?."
"Kaine ka bani dariya Omar, wai saurayina. Ina laifin ka ce mai neman aurena? Saurayi ai sai dai irin ku masu neman yara su aura."
Shima sai ya É—an saki fuska yana kallon ta ya ce, "Yaushe zai zo É—in?." Ta ce, "ba ka ce gobe ba? ya ce goben zai zo in sha Allah."
"Ya yi" ya faɗa yana ɗauko waya yana dannawa. Abinda ya faɗo ƙasa ta kalla garin ɗauko wayar ya faɗo daga aljihunsa. Ta kalle shi ta ce, "Omar me nake gani a kusa da ƙafarka?." Kallon wajan ya yi sannan ya kalle ta ta ce, "Omar baka daina shan sigari ba daman?."
"Na daina Didi, ɗazu ne da raina ya ɓaci shine...."
"Shine ka sha?."
"Uhum."
"Omar ba ka ce min ka daina ba?." Ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Didi na daina wallahi, ɓacin rai ne kawai." Shiru tayi alamun ranta ya ɓaci, ya kalle ta ya ɗauke kai ya cigaba da abinda ya ke yi. Jin shirin na ta yayi yawa ya sake kallon ta ya ce, "Didi yau ne kawai, kuma daga yau har abada bazan sake ba."