Sashe 41
Kiran Rabo Book1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Didi ta yi dariya ta ce, "babu komai. Amma na san baka manta ta ba, kawai halin wulaƙancin naka ne ya motsa." Ɗauke kai ya yi yana mai jin haushin Nayla a ransa, ita kanta Didi haushinta yake ji, haka kawai ta dinga nuna masa yarinyar kuma ta ce lallai sai ya game ta kamar wata ƙanwarsa. Fushi ya yi ya tashi ya bar mata falon bata ma wawaye shi ba ta cigaba da harkokinta dan in ta saka lamarin sa a zuciyarta ciwo zata yi.
    •••••••
Nayla kuwa kamar yadda Abiy ya faÉ—a kaf É—insu suka tafi Umra, suna garin Madina suna ibada kafin su tafi makka. Nayla gabaÉ—aya bata da karsashi zaman, saboda zuwa lokacin ta tabbatar da son Omar take yi, so ba wai na wasa ba na gaske wanda ake kira so. In ta tuna waye Omar da halayensa, ta tuna waye Abiy sai gabanta ya faÉ—i tsoro ya mamaye mata zuciya ta kasa sukuni gabaÉ—aya.
Ta saka tunanin Omar a ranta ta hakan ya saka ta rame, bata ma zaman hotel ko yaushe tana masallaci tana kaiwa Allah kukan ta amma abin babu sauƙi sai sake gaba da yake yi. Duk ƴan uwanta sun fuskanci canji a lamarinta, in suka tambaya sai ta ce babu komai. A wannan yanayin suka shiga makka suka yi umra Abiy bai ji Nayla tana zancen zata je Makka mall ba, dan ya san indai suka zo sai Nayla taje Makka mall ta yi siyayya ta dawo.
Suna zaune a falon hotel ɗin su gabaɗayan su Abiy ya kalle ta ya ce, "Mamana zo nan." Ba musu ta ƙarasa inda yake ta zauna, ya kalle ta ya ce, "ban ji kina zancen zaki je Makka mall ba, lafiya ki ke?."
Nayla ta ce, "bana son zuwa ne, duk abinda zan siya zan siya a nan ba sai naje can ba." Yadda take magana a sanyaye ya saka ya kalle ta da kulawa ya ce, "Mamana me yake damunki? Na lura da rashin walwalarki, kina ware kanki ke kaɗai bakya son zama cikin mu, sannan baki da ƙwarin jiki, sannan kuma kin rame. Me yake damunki?. Duk lokacin da muka zo ƙasar nan har neman ki mu ke yi muna rasawa saboda yawo, amma gabaɗaya yanzu ki canja. Me ya faru?."
Zuciyar Nayla harbawa take yi sosai, idonta ya kawo ruwa kafin ta farga har hawayen ya sakko. Abiy ya damu ganin tana kuka ya ce, "Sanar dani damuwarki Mamana." Nayla ta goge ido ta ce, "Babu abinda yake damuna Abiy."
"Yaushe ki ka fara yi min ƙarya Mamana?." Ta sunkuyar da kai ya kalli ƴan uwanta ya ce, "in kuma kina so su bamu waje sannan ki faɗa min sai su bamu waje."
Nayla ta kalli Abiy ta ce, "A'a Abiy, babu abinda yake damuna." Abiy ya murmusa ya ce, "Mamana kina da damuwa, damuwar ma ba Æ´ar kaÉ—an ba. Ki faÉ—a min abinda yake ranki."
Nayla ta sunkuyar da kai ta rasa abinda zata ce, saboda ko giyar wake ta sha bazata faÉ—awa Abiy abinda yake damunta ba, da ta faÉ—a masa gwara abinda take ji ya kashe ta. Dabara ce tazo mata sai ta ce, "Ummana, mafarkinta nake yi a kwanakin nan Abiy" ta faÉ—a tana fashewa da kuka.
Duk sai kowa jikinsa ya yi sanyi ba kamar Abiy da take kusa dashi, fuskarta ya riƙe ganin yadda take kuka sai baice komai ba ya kwantar da kanta a kafaɗarsa ya bata dama tayi kukan. Ita kuwa Nayla kukan rashin mafita da tausayin kanta kawai take yi, sai da tayi mai isar ya sannan ta tsagaita kukan ya ɗago ta daga jikinsa ya ce, "Kina yi mata addu'a?." Nayla ta ɗaga kai alamun eh ya ce, "To ki yi haƙuri, addu'a itace kawai soyayyar da zaki nuna mata kin ji?." Ta ɗaga kai alamun to ya share mata hawaye ya ce, "Yanzu ki shirya ki tafi kasuwar ki yiwa Hajja da Salma siyayya, ko baza ki basu tsaraba ba?."
Sai tayi murmushi ta ce, "zan basu." Ya yi murmushi ya ce, "to maza riƙe twnity ɗinki ku tafi kasuwar." Ta ɗaga kai Abiy ya ce, "ki saki ranki bana son wannan ɗabi'ar da kika ɗauko kin ji." Tayi murmushi ta ce, "To Abiy." Ta kalli Jidda da take kallon ta ta ce, "Twiny mu je?." Jidda ta ce, "Zo mu je ɗaki ɗauko kuɗi sai mu je." Tare suka fita zuwa ɗakin su dan nan wajan Abiy ne, ɗakin suka shiga basu jima ba suka fita. Sai da suka je reception na hotel ɗin sannan Jidda ta riƙe hannu Nayla ta ce, "Twiny."
Nayla ta kalle ta dan ta san daman sai ta tambaye ta, in akwai wanda ya san halinta a gidan su to Jidda ce. Jidda ta ce, "Twiny kin san dai ban yarda da abinda ki ka cewa Abiy ba ko? Ai ba yau kika sana mafarkin Umma ba, Meyasa baki taɓa shiga damuwa ba sai a wannan lokacin?." Nayla ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Jidda ta ce, "Twiny ki faɗa min damuwar ki don Allah."
Nayla ta fashe da kuka ta rungume Jidda tana kuka sosai. Jidda ta riƙe ta tana shafa bayanta a hankali dan ta san ƴar uwarta ta tana da babbar damuwa. Sai da ta bari ta gama kukan sannan ta ɗago tagoge idanun ta ta ce, "mu je mall mu dawo." A haka suka tafi dukka su babu mai walwala a tare dashi, sun jima sosai duk da basu yi wata siyayya ba, sai dan kawai kasuwar da nisa inda suke.
ÆŠakin su ita da Jidda ne kawai sai matar Yaya Anty Halisa dan Jidda babu mijinta suka zo. Da suka dawo Anty Halisa bata nan hakan ya saka Jidda cire mayafi ta zauna kusa da Nayla. Kallon ta tayi sosai ta ce, "FaÉ—a min damuwarki." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "Twiny wani ne." Jidda ta ce, "me wanin ya yi miki?." Tayi shiru bata ce komai ba. Jidda ta ce, "kin faÉ—a soyayya ko?."
Nayla ta kalle ta sai hawaye ya sakko mata, Jidda ta riƙe hannunta ta ce, "tun a Kaduna naga yanayinki ya yi min kama da wacce ta fara soyayya, kuma na tabbatar a Kano ki ka yi gamo da ƙaddararki. Waye shi? Ya san kina sonsa?."
Kai ta girgiza tana kuka ta ce, "ban san sonsa nake yi ba Twiny, da na san zan fara sonsa da ban je Kano ba, da na yi zamana tare da Mama da Abiy a gida, wallahi da bazan je ba." Jidda ta ce, "ƙaddarar kenan ai. Kuma ita soyayya ai ba kai make sakawa kanka ita ba, Allah ne, kuma yin kanta take yi a zuciyar ɗan adam."
Nayla kuka take yi sosai tana cewa, "ban san ya zanyi ba, kullum cikin kewar ganinsa nake, kullum cikin son jin muryarsa nake amma ko number wayar sa bani da ita Twiny. Meyasa soyayya zata yi min haka? Meyasa zan fara son wanda bani da tabbaci akan zai so ni?. Twiny ko kallo ban ishe shi ba, hasalima maganar minti ɗaya bata taɓa haɗa mu dashi."
Jidda cikin sanyi ta ce, "Waye shi?." Ɗagowa tayi daga jikin Jidda ta ce, "Ki yi haƙuri Twinny, zan faɗa miki amma ba yanzu ba." Jidda ta ce, "kina addu'a?."
"Ina yi sosai."
"Ki sake dagewa kina faÉ—awa Allah damuwarki, in ba alkhairi bane Allah ya cire shi daga rayuwarki, in kuma alkhairi ne Allah ya daidai ku."
Da jajayen idanun ta ce, "gwara na yi addu'ar Allah ya cire min shi É—in, dan ko yana sona bana tunanin Abiy zai amince."
"Me zai hana ya amince?." Nayla ta girgiza kai tana aiyana dan bata san waye bane shiyasa take faÉ—ar haka.
Jidda ta ce, "yanzu dai tashi mu je mu shiga mataf ki sake faɗawa Allah damuwarki, zama bai kama mu ba ai Twiny." Nayla ta miƙe tsaye Jidda ma ta miƙe sai Nayla ta ce, "yau ban ji kina waya da Baby ba." Jidda tayi murmushi ta ce, "yana can Kano yana neman gida, ya dage sai unguwa ɗaya yake so kuma gidan sai wanda ya yi masa wai ai kuɗinsa ne, siya zai yi ba haya ba." Nayla tayi dariya ta shiga tayi alwala Jidda ma tayi suka fita zuwa masallaci.
    A ɓangaren Abiy bayan fitar su Nayla kowa ya fita ya zama daga shi sai Mama ya yi shiru bai ce komai ba. Mama cikin ƙarfin hali ta ce, "ka yarda da abinda Nayla ta ce maka?."
Abiy ya kalle ta ya ce, "koda abinda ta faÉ—a yana damunta to tabbas akwai wani abun da yake damunta bayan wannan." Mama tayi murmushi ta ce, "ka fahimta kenan, nima na ga haka a tare da ita sosai."
"Amma me kike gani yana damunta?."
"To in na faÉ—a sai ka ce ba haka ba, gwara nayi shiru kawai." Abiy ya ce, "kina nufin Hajja?."
Kafin Mama tayi magana ya ce, "kinga mu bar zancen nan, domin bazan amince son zaman Kano ne ya mayar da Mamana haka ba. Akwai dai abinda yake damunta amma ba wannan ba." Mama ta yi shiru kawai bata ce komai ba amma ya zama dole ya nemo damuwar Nayla ko dan ta san meye in zata amfane ta tayi amfani da ita.
••••••••
Narma gabaÉ—aya ta susuce soyayya tayi mata mugun kamun da bata yi tunani ba, ta koma wani iri ko yaushe cikin tunani take da faÉ—uwar gaba. Yanzu gashi in ta kira Omar É—in ma baya É—auka, gabaÉ—aya sai ta sake shiga damuwa ta yi wani iri kamar ba ita ba.
Iyayenta duk sun lura da yanayin ta ranar Mum tayi nufin sake tambayarta. Ɗakin ta ta shiga ta same ta tayi tagumi ta zauna a gefen ta ta ce, "Narma." Narma ta kalli Mum ta ce, "faɗa min abinda yake damun ki kika zama haka." Narma ta ce, "Mum nima ban sani ba, amma Ina sonsa sosai Mum, Ina ji in ban aure shi ba zan iya mutuwa." Mum ta riƙe fuskar ta tace, "Waye shi? A Ina yake?."