← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 64

Sashe 63

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kasa kwanciya." Umma Furera ta gyara zama ta goge hawaye ta ce "Malam Yahuza yayana ne uwa daya uba daya, amma ni a garin Shanono na girma shi kuma a Yan Lanya ya girma kasancewar yawon almajiranci ya je yi. Ya yi aure-aure da dama, amma Allah bai bashi haihuwa ba, na ji labari ya auri Zuhuriya, amma ban taba zuwa lokacin da suke tare ba, ta samu ciki ta haifi 'ya mace. To kamar yadda aka ba ni labari da muka je zaman makokin Zuhuriyya. An ce ta haihu da kwana biyu sai ba ta da lafiya, saboda haka tana kwance a daki akwai wani Malami da ya zo daga Balle bantai ya ce a kawo yarinyar zai yi mata addu'a, sai Malam Yahuza ya shiga ya dauko 'yar a kwance a gaban Zuhuriya ya ce min har Zuhuriyar ta yi masa magana ta ce masa kada a yi wa jaririyarta zane, dan Allah a bar mata fuskarta haka, kasancewar mu Fulani ne ta ga duk 'yan uwanmu da zane irin nawa nan, ya ce ai ba wanzami ba ne, malami ne ya zo zai yi mata addu'a. Ya ce min ya fito ya bar ta da garwashin wuta a gabanta cikin kasco saboda sanyin da ake yi sai dai idanuwanta lumshe kamar mai magagin barci. Ita kadai ce a dakin kasancewar babu wata wacce ta zo ta zauna da ita daga Cinkilawa, amma mahaifiyarta na zuwa ta yini, sannan ta koma. To bayan ya fito da 'yar jaririyar zaure aka mata addu'a ya karbe ta zai mayar da ita wajan mahaifiyarta sai ya iske wuta ta gauraye dekin har rufin dakin babu ta inda mutum zai fito. Babu kowa a tsakar gidan sauran matan su na dakunansu. Sai da Malam Yahuza ya yi ruri yana kiran "Jama'a ku taimake ni wuta!" Sannan kowacce ta fito daga dakinta da gudu, maza daga qofar gida suka shigo ana ta zuba ruwa da qasa, amma ina abu ya ci tura, sai da daki ya qone kurmus Zuhuriya na ciki ko ihunta ma ba a jiyo ba, sai toka babu alamar bil adama." Bakura ya gyara zama yayin da Sajida ta qurawa mahaifiyarta ido tana dubanta zuciyarta cike da mamaki hade da tunani mai firgitarwa ta qagu ta ji qarshen labarin, kwakwalwarta ta kasa tantance mata abun da yake shirin faruwa. Umma Furera ta ci gaba da cewa, "Labarin rasuwarta ya iske mu muka dungumno daga Shanono muka iso Yan lanya don yin gaisuwa. Ba tare da doguwar magiya ba na roqi yayana Yahuza cewar ya ba ni 'yar in rike tunda ban taba haihuwa ba a lokacin. Nan da nan ya ce in dauka ya ba ni ita tunda ba mu da iyaye ni da shi ne kawai mu ka rage" Sajida ta ji wani jiri ya fara tasowa daga cikin kwakwalwarta, ta dubi Umma Furera yayin da hawaye ya cika idonta ta fada cikin wata murya mai karkarwa "Umma, baki taba fada min kin taba rike wata 'ya ba, rasuwa ta yi ne daga baya?" Umma Furera ta girgiza kai yayin da wata fargaba ta rufto mata. Ta dubi maigidanta Malam Yakubu ta rushe da kuka ta ce "Malam ka fadawa Sajida gaskiya, yau ne ranar farko da ya kamata ta san gaskiya." Sajida ta waiga da sauri ta dubi Malam ta fada cikin tashin hankali ta ce "Baba me yake faruwa ne? Ka fada min gaskiya." Ta tashi da gudu ta tafi wajen lya Azumi (Innono) ta rike ta tana kuka. "Ki fada min abun da ban sani ba, mene ne yake faruwa ko ba ni da iyaye tsinta ta aka yi?" Samira, Zahra da kannenta suka shiga rikitaccen tunani, sun kasa gane abun da zai faru. Innono ta sharbe hawaye ta ce, "Ke ce yarinyar da Zuhuriya ta mutu ta bari. Ma'ana ke 'yar Zuhuriya ce da malam Yahuza ba Furera da Yakubu ne suka haife ki ba." Ba ta rufe bakinta ba Sajida ta cukuikuye ta kame a gefe ta rusa kuka, saboda tashin hankali. Bakura ya yi kabbara hade da hamdala ya dubi Sama ya ce "Allah Kai ne mai hikima, Kai ka san abun da yake boye. Ni ban san gaibu ba, amma na san tabbas akwai wani sirri na boye game da kamar da suka yi." Umma Furera ta je wajen da Sajida ta qame ta dafa kanta gami da murza bayanta ta na kuka itama ta ce, "Sajida ki yi hakuri ki yafe mana, na san ba za ki ji dadi ba, ya kamata ki sani tuntuni musamman lokacin aurenki. Ban san yadda zan fada miki ba, kasancewar mun shaqu ko Malam baya so ki san babu wata alaqa a tsakaninku.' Umma Furere ta zauna a gefen Sajida tana rungume da ita, ta ci gaba da cewa "Na karbi Sajida daga hannun dan uwana a bisa amana zan rike ta har aurenta. Bayan da aka yi sadakar bakwan mahaifiyarta Zuhuriya ko da yake Fatsima na ji mijin yana fada mata, don haka ya ce a mayarwa 'yar sunan mahaifiyarta Fatima, shi ne muke kiranta da Sajida tunda duk Fatima ce. Mun hadu da Iya Azumi a zaman makokin sau daya, amma ta yi fushi ta fice daga gidan mutuwar da ta ji labarin ni a ka bawa jaririya ba ita ba. Ta so a ba ta jikarta ta rike mahaifin Sajida ya qi amincewa, don haka da ta tafi ba ta sake waiwayar yarinyar ba, amma qanwarta ta taba zuwa ta nemo mu kuma ta zo bikin ita ce ta tafiwa da iya Azumi kayan biki , sai jiya da muka ganta kwatsam. Na dawo gidana goye da jaririya, sannan na yi wa Malam bayani sosai ya yi farin ciki, kasancewar ni da shi dukka muna tsananin son haihuwa, Allah bai ba mu ba. Muka dinga qulla-qulla, muna tanade-tanaden kudin madarar da muka shayar da 'yar jaririya har Allah ya raya ta, ta fara cin abinci sosai. Na shaqu da Sajida, haka Malam ma, sajida ta kasance yarinya ce mai wayo da yawan suruu, don haka ne ma ko da wasa ba na fadawa kowa wannan sirrin cewa Sajida ba 'yata ba ce, haka shi ma Malam yake cewa 'yarsa ce ta cikinsa. Da ta isa sawa a makaranta ma Nursey School mai kyau muka saka ta.Akan keke yake kai ta, ya dauko ta, har ta shiga primary tana amfani da sunan Malam wato Sajida Yakub. Allah mai amsa addu'ar bayinsa, kwatsam sai na ganni da ciki Allah ya ba ni ciki a lokacin da ya so in haihu na haifi da namiji muka sa masa suna Yahuza, sunan mahaifin Sajida kenan da Allah ya yi masa rasuwa tun tana da shekaru biyu kacal a duniya. Don haka Sajida da Yahuza suka taso a matsayin uwa daya, uba daya, ba tare da sun ga wani bambanci daga wajen Malam ko daga wajena ba." Umma Furera ta yi shiru tana sharce hawaye da gefen gyalenta, yayin da kowa ya yi tsuru kamar masu zaman makoki. Sautin kukan Sajida ne kawai yake tashi, yayin da ta miqe qafa a qasa ta kifa kai a kan kujera. Tana rusa kuka mai tsanani, gami da cewa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, ba ni da uwa, ba ni da uba ashe, ban san uwata ba, ban san ubana ba, babu wanda ya taba fada min gaskiya. Kakata wacce ta haifi uwata ce ta rage min amma ba ta taba neman in da nake ba. Sai yanzu? Ashe ba ni da kowa, ba ni da wa ba ni da qanwa, ko qani, ban san asalin garina ba, balle in san dangin uwata da ubana ba. Wannan baqin ciki ya ishe ni har gara a ce Allah Ya đauki raina in mutu in je in sadu da mahaifaina, zamana a duniya ba shi da amfani. Wayyo Allah Zuhuriyya, ban sanki ba, ban taba sanin kamanninki ba, ko a mafarki ban taba kwatanto ki a raina ba. Allah yayi miki gafara." Kowa ya fashe da kuka, musamman Bakura, ji yake zuciyarsa na tafasa tamkar za ta fice, saboda tashin hankali. Ya sunkuyar da kai qasa sai hawaye ke ta shatata. Ya damqe kai dam da hannayensa guda biyu yana jinjina ikon Allah mai yadda Ya so Yake tsaro rayuwar bayinSa. Malam Yakubu ma hawaye yake yayin da kalaman Sajida ya ji kamar an watsa wuta a zuciyarsa. Ya yi gyaran murya ya ce, "Sajida, hakika za ki ji ba dadi lokaci guda a tare ki a ce iyayenki da kika dauka su suka haife ki ba iyayenki ba ne na gaskiya.To amma sai ki duba ki ga wanne irin riko suka yi miki, wanda ya sha bamban da na dan da suka haifa a cikinsu. Kin ga ai ba bambanci, bambanci daya ne Allah bai kaddaro ta jikinmu za ki tsaga ki fito ba, wannan kuma Allah ne ke tsarowa kowa daga cikin wance, wane zai fito. Domin uwar wani, ko uban wani baya haihuwar dan wani. Allah ya kaddaro Zuhuriya ce za ta haife ki, bayan tsawon shekarun da ta yi ba haihuwa, ta same ki ashe mu ta haifawa ta mutu ta bar ki. Mu ka ga ba anmfanin sanar miki gaskiyar al'amari, saboda ba komai zai qara miki a rayuwarki ba sai damuwa, daman da ace iyayenki na raye ne sai mu kai ki ki gansu, to yanzu ko mun fada miki basa nan, duk da mun san komai dadewa wata rana za ki ji labari, idan na mutu ko Furera ta mutu. Dangin da kike cewa ba a nuna miki ba, ai duk dangin Furera da kika sani sune dangin mahaifinki, kasancewar uwa daya, uba daya suke da mahaifinki Malam Yahuza. Garinku da kike kira ba akai ki ba, ai Shanono ne garinku na ainahi, Yaya Yahuza yawan almajiranci ne ya kai shi can amma ba ku da dangi a garin. Dangin mahaifiyarki kuwa da ba a nuna miki ba, ba da gangan müka qii nuna miki ba, ba mu san su ba ne, kakarki Iya Azumi ita kadai ce a Cinkilawa, ita ma tun ranar da aka taho da ke ba a sake jin labarin inda take ba, domin ita ma mijinta da take zama dominsa a Cinkilawa ya rasu jim kadan bayan mutuwar mahaifiyarki. Ba mu
Chapter 63 · 0% Book details