← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 64

Sashe 25

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bakura ya iso qofar gidan Malam Yakubu daf da magariba kamar yadda ya saba zuwa. Ya iske Malam tare da dalibansa wato manyan mazan da suke daukar karatu tsakanin sallar magarib da isha'i. Kamar yadda su ka saba bayan sun idar da sallar magariba sai suka shiga daukar karatu, har zuwa lokacin da Isha'i ta yi, su na idarwa sai kowa ya watse.
Bakura da Malam ne kadai su ka rage. Hira suke kamar abokai, hirar dai ba ta wuce hirar siyasa ba. Da aka fito da abinci sai Bakura ya nemi afuwa akan yau dai sai dai Malam ya yi masa hakuri ba zai ci abinci ba saboda duk randa ya je gida cikinsa a qoshe rigima ake da uwargida.
Malam yayi dariya ya ce "kwarai kuwa na fahimce ka, mata su na da wannan dabi'ar."
Malam ya bude kwanon tuwo da miya kamar kullum tuwon tsari da miyar busashshi kubewa ce babu nama a cikin miyar sai dai qamshin wake da daddawa ne ya ke tashi. Bakura yana hira ya na satar kallon Malam. Tausayinsu ya rufe shi ya shiga sake-saken yadda zai taimakawa wadannan bayin Allah. Sai ya yanke shawara a ransa in dai ya tashi tafīya yau zai yiwa Malam alkawarin wani kudi mai tsoka da buhunhunan abinci wanda zai agaza masa wajen samu ya ciyar da iyalinsa da abinci mai kyau.
Malam cin abincinsa yake kai kace ba garau- garau yake ci ba kamar wanda yake cin naman talo-talo.
Malam ya gyara zama ya dubi Bakura ya ce "Alh.
Babura na yaba da hankalinka, ka zama tamkar d'a na cikina ko in ce dan uwana na jini. Na yarda da kai sosai ina so ka bani shawarar da zata amfane ni. Bakura ina so ka tsaya cikin nutsuwa ka bani shawara akan wata matsala da ta addabe ni"
Bakura yayi quri yana duban Malam zuciyarsa cike da tsananin mamaki ya na tambayar kansa shin wacce irin alfarma haka Malam yake nema a wajensa yake jero irin wandannan kalamai?
Malam ya ci gaba da cewa "Bakura, ka bani shawara akan Sajida."
"Shawara akan Sajida?" Bakura ya tamabaya cikin murya mai tafe da tsananin mamaki. Ya qara da cewa "me yake faruwa ne game da Sajida?"
Malam ya nisa ya ce "so nake in aurar da Sajida domin in sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Saboda yaron nan Abdulmajid ba zai barta ba. Kuma duk garin nan kowa ya san ba aurenta zai yi ba lalata ta yake niyyar yi. A dalilinsa na hana ta karatu, a dalilinsa na hana ta fita amma duk da haka basu rabu da juna ba kwanciyar hankalina shine kawai in sami wani babba mai hankali wanda zai riqe min Sajida a matsayin matarsa. Wallahi Bakura ko baccin kirki ba na iya yi saboda kullum gani na ke Sajida zata bude qofa cikin dare ta je wajen Abdulmajid."
Bakura yayi shiru kamar wanda ruwa ya cinye ya rasa abunda zai ce. Can ya nisa ya dubi Malam ya ce "bayan Abdulmajid akwai wasu masu neman ta?"
Malam ya girgiza kai ya ce bayan Abdulmajid ba ta tsayawa da kowa. Akwai wani mai naci da ya qi tafiya duk wulakancin da za ta yi masa baya fasa zuwa shima yanzu ya hakura ya daina zuwa.Yanzu al'amarin Sajida ya kai ya kawo akan
Abdulmajid za ta iya rufe ido tayi tsiwa a gabana ta ce babu mai hanata auren Abdul Abdulmajid."
Sai hawaye ya surnano daga idanuwan Malam.
Hankalin Bakura yayi mutuqar tashi yayi shiru ya na tunanin irin shawarar da zai bawa Malam a matsayinsa na mai ilimi.
Malam ne ya katsewa Bakura tunani, ya ci gaba da cewa "ranar wanka ba'a boyen cibi. Bakura,
KAI KA FI CANCANTA ka auri Sajida."
Jin wannan kalma ta fito daga bakin Malam sai ya ji tamkar an harba bindiga a kirjinsa, ya ji kamar wani abu ya harba a cikin zuciyarsa saboda firgicewa. Ya dago da' sauri ya dubi Malam, duba irin na rashin fahimtar abunda yake nufi.
Malam ya dubi
Bakura duba na fuska da fuska.Ya ce "kai nake so ka auri 'yata Sajida idan kayi haka ba karamin jahadi kayi ba, ka taimaki rayuwarta ka taimaki rayuwata ni ubanta. Babu wanda ya fi ka sanin illar haduwar Sajida da Abdul majid. Saboda a hanya ka tsince su kaga halin da zasu shiga ka garzayo ka fada min don in tsawatar ba qaramar qaunarmu kake yi ba. Na yarda da tsananin tsoronka, saka ido akan tarbiyyar iyalinka. Na yi sha'awar hada zuri'ata da taka ba don komai ba, ko don wani abu ba sai don saboda Allah. Idan kana ganin baka da ra'ayin qara aure ko baka da ra'ayí akan Sajida kar ka boye min Bakura ka fada min, wannan magana muke ta fahimta.
Na yarda a cikin jama'arka ko daga cikin abokanka zuwa yaran gidanka ko Malaman masallacin qofar gidanka ka zabi mai hankali, mai addini mai tsoron Allah ka bashi Sajida. Na amince maka na san ba za ka cuce mu ba, ko ina raye ko ina a mace. Sajida 'yarka ce, kanwarka ce ka dauke ta tamkar Zahra."
Bakura yayi shiru kansa a sunkuye a kasa kamar wanda aka saka igiya aka daure shi tamau ko yatsa baya iya dagawa saboda rikirkitaccen tunanin, kwakwalwarsa ta kasa warwarewa.
Malam ya ci gaba da cewa "wanda zai auri Sajida ba na buqatar ya kawo min komai in banda sadaki. Sadakin ma kalilan ya isa kamar yadda shari'a ta yarda, ina da filina anan ringi road zan saka shi a kasuwa in sayar na san zai isa in yi mata gado da 'yan kujeru da zannuwan daurawa. Me kuma ake nema a rayuwar aure dai? Burina a killace min ita ta zauna lafiya ta cire ranta daga kan dan iskan yaron nan. Na fada ma ta nan da sati guda zanyi ma ta miji ko ta na so ko bata so, nan da wata guda ayi biki. Hankalina bai kwanta da masu zuwa wajena ba ne.
Da yawa sun sha nuna min su na son auren Sajida na qi amincewa saboda ban yarda da rikon da za su yi mata ba haka ina tantama da tarbiyyarsu. Kudi ba komai ba ne, mutunci shine ya fi komai. Ko dan dakon da yake neman halalinsa mai tsoron Allah, wanda ya san Allah ya san yadda zai bautawa Allah mai ilimin addini, wannan mutum shi ya fi cancanta a zauna da shi ba mai kudin da yake takama yana da kudi ba don haka yake ganin yafi karfin ya bautawa Allah ba."
Bakura har yanzu kalma guda daya ta gagari bakinsa ya na kallo, yana sauraron Malam babu abinda yake sai kada kai alamar yana gasgata zancen Malam.
Daga karshe malam ya ce "na baka wuka, na baka nama Bakura ka je kayi tunani nan da sati biyu ka zartar da duk hukuncin da ka ga yayi daidai akan 'yata Sajida."
Ba tare da Bakura ya furta wata kalma ba ya mike zuwa wajen motarsa. Malam ya raka shi har jikin mota yana mai yi masa addu'ar Allah Ya kai shi gida lafiya.
Bakura ya duqa ya cewa Malam "na gode Malam, zan tafi sai kuma gobe idan Allah Ya kaimu."
Ya shiga motarsa ya ja ya tafi. Malam ya dawo kofar gida ya ci gaba da tunanin shin wacce shawara Bakura zai yanke akan Sajida?
Bakura kuwa tsabar tunani sau biyu yana shiga layin daba layin gidansa ba, bayan fadawa a ramuka da kwatoci ba adadi. Ya rasa abinda zai zaba wanda yafi cancanta a ciki game da Sajida. Na farko a sanadiyyar tsanananin kamar da Sajida take yi da Zuhuriyyarsa ya
ji baya gajiya da kallonta tamkar wata talabijin haka Idan ya tuna tsantsar rashin kunyar Sajida sai ya ji gwbansa ya fadi saboda shi yana da kunya kuma baya son ayi masa rashin kunya.
Kalmar farko da Sajida ta fara furta masa ido da ido tawa Bakura ita ce "na tsaneka."
Dan haka babu tantama wannan tsanar tana nan a dauwame a cikin ranta babu mai goge ta. Zahra yarinya qarama ba ta san Sajida ba amma har ta gane halin Sajida bashi da kyau a take ta ce bana son Sajida bata da tarbiyya. Ga matarsa mai tsananin kishi muddin ta sami labarin Bakura zai kara aure tabbas zata iya hadiyar zuciya ta suma idan ma bata zarce gaba daya ba. Bakura ya sake Juyawa ya dubi amintar da take tsakaninsa da mahaifin Sajida Malam Yakubu ya san zai ji nauyin ya ce masa baya son 'yarsa. Yaya za'ayi kenan? Sajida ta zame masa kadangaren bakin tulu.
Chapter 25 · 0% Book details