← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 64

Sashe 62

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dago da luhu-luhun idanuwansa jajaye ya kalli Malam ya qyada kai ya ce "Babu wanda ya fada min gaskiya har yanzu. Mun rabu da Zuhuriya a lokacin da ya rage min saura sati biyu in gama makaranta. Da sati biyu ta cika muka na zana jarrabawar qarshe sai na yiwa Malam Abbas da iyalansa sallama har da koke-koken rabuwa Aunty Asiya da 'yayanta muka yi,saboda mun shaqu. Mu ka yi hotuna da koke-koke ni da abokaina, sannan kowa ya kama hanyar garinsu. Da jakar kayana kacokan na nufo gida. Ina tafe ina zulumi, ina tunanin da Magarubar nan ina zan nufa gidan Innono ko gidan Zuhuriya? Na yanke shawarar gara in je wajen Zuhuriyata, don na damu na ga lafiyarta in ya so ko a zauren gidan sai in kwana kafin mu yi shawarar inda zan zauna. Ina isa kofar gidan na iske Malam Yahuza mai gidanta da sauran mutane. Na gaishe su, amma sai kowa yake yi min duba irin na tausayawa na lura da haka, amma ban kawo komai a raina ba na wuce zuwa cikin gida. Na iske sauran matan biyu su na zaune bisa tabarma daya sun hada kai su na qus-qus su na ganina sai na ga sun zabura sun miqe tsaye yayin da daya take qoqarin zurawa da gudu su na tambayata, Lafiya? Me na zo yi a gidansu? Sai na yi mamakin wannan tambaya ta su, amma ba su da wata amsar da zan iya ba su, domin bai kamata su tambaye ni abun da na zo yi ba a wajen Zuhuriya ba. Na kada kai na nufi dakinta. Abun da na gani shi ya firgita ni na tsaya cak yayin da na juyo da sauri na dube su. Yayin da bakina yake karkarwa na tambaye su "Ina dakin Zuhuriya, ina Zuhuriya?" Sai Bakura ya riqe kai ya barke da wani zazzafan kuka mai zubo da hawaye ba kakkautawa. Hankalin kowa ya tashi, yayin da gaban kowa ke faduwa. Yara da manya hawaye ne fal a idonsu. Sajida ta tambaya cikin damuwa "Me ya faru da dakin Zuhuriya?" Bakura ya dago da kyar ya dube ta ya fada ciki wata nakasasshiyar murya, "Dakin Zuhuriya ya kone kurmus sai toka." Zahra ta ce "Ina Umma Zuhuriyar? Ina bebin da ta haifa?" Bakura ya, girgiza kai saboda tsabar jimami ya ce "Zuhuriya na ciki ita da baby lokacin da wutar ta kama don haka suma sun qone." Su ka hada baki su duka "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Kowa ya yi shiru babu wanda ya iya cewa komai, fuskar Bakura na tsugunne a qasa sai hawaye ne ke zuba a kan tiles fat-fat-fat daga nan ya kasa ci gaba da labarin. Innono ce ta ci gaba ita ma cikin rurin kuka, hawaye ke zubowa kamar ruwan famfo ta ce, "Daga sanda Bakura ya ji Zuhuriya ta qone qurmus ko gawarta ba a fitar ba, sai toka, a take ya suma har bayan Isha'i bai farfado ba ana zuba masa ruwa. Washe gari da safe ya nufo Cinkilawa wajena. Bakura ka yafe min abun da na yi maka a rayuwa. Iyalan Bakura kuma ku yafe min shiyasa ake son mutum ya shuka abun alkhairi a rayuwarsa, ina ganinsa zai shiga Cikin gidan sai na zo na tare qofa da hannuna na tambaye shi ina zai je? Ya kalle ni galala kamar Zautacce sai na nuna masa hanyar waje na ce yau babu Zuhuriya a duniya, don haka babu kai babu zama a Cinkilawa ka hada kayanka ka koma Mangono. Ya Juya a sanyaye yana tafiya sai na ga idan ya tafi aka rasa shi ni za a kama a Mangono a ce ina dan da muka dauko sai na kira shi ya dawo na ba shi tabarma a zaure na ce ya zauna nan da kwana biyu zan hada kudin mota in mayar da shi Mangono da kaina. Bakura baya kuka sai dai ajiyar zuciya ko ba a fada maka ba ka san turniqin qunar da yake ji ba zai fasaltu ba. Kuma baya magana sai kallo da ido. Da Magaruba ya tashi ya fice ban sake ganin Bakura ba sai yau, neman duniya nasa a yi ba a ganshi ba. Baya Cinkilawa, baya Balle batai, baya Yan lanya, baya Jarawa, baya Warawa, baya Lahadin makoli baya kadara, baya Rimi,baya Token, haka baya Larabar gadon sarki sannan baya makarantarsu Wudil, don haka na ja bakina na yi shiru, duk wanda ya tambaye ni Bakura sai in ce ai tun bayan mutuwar Zuhuriya iyayensa suka zo suka dauke shi sun tafi da shi Mangono." Har wani lokaci mai tsawo Bakura ya dauka kansa a sunkuye bai dago ba. Can ya dago ya dubi kowa daya bayan daya ya sharbe hawaye. Ya ce "Kun ji yadda mutuwa ta raba ni da Zuhuriyar da nake matukar kauna take matukar sona a duniya. Na yi rashin uwa, na yi rashin uba, na yi rashin yayata, na yi rashin aminiya, na yi rashin mai sona. Daga sanda na ji Zuhuriya ta rasu daga lokacin na ji wani qaton abu mai kama da dutse ya zo ya tokare min a tsakiyar kirjina har yau bai sauka ba. Ban fara kukan mutuwar Zuhuriya ba da hawaye sai da na shekara biyar zuwa shida bayan mutuwarta, saboda abun da nake ji ya fi kuka ciwo. Kukan da na fara shi ne sauqin ciwon mutuwar har yau ban taba kwana biyu ba cur ban zubar da hawayen dacin mutuwar Zuhuriya ba a zuciya ba. Ban taba samun naira daya, ban yi hawayen daman Zuhuriya na nan in ba ta ba. Ban taba miqawa wani kudi ko kaya ban tuna dama Zuhuriya nake bawa ba. Alhamdulillah Alakulli halin, Allah ne mai yadda ya so da bayinsa. Tsakanina da ita sai addu'a marar adadi, sai na dinga sadaukar mata da sadakatul jariya. Ina addu'a, Allah ya kai mata rahama cikin kabarinta." Su duka suka amsa masa da, "Amin." Zahra ta sharbe hawaye ta ce "Abba, a lokacin shekarunka ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba kana yaro, ina ka tafi da ba'a ganka ba, ko Mangono ka koma?" Bakura ya girgiza kai ya ce "Ban yi tunanin Mangono ba, ban yi tunan komawa Wudil ba. Ban yi tunanin a duniyar da na ke ba, ni dai na sa gabana gadi ina ta tafiya a dawa cikin dare. Ban damu da duhu ba, ban damu da maciji ba, ban damu da 6arayi ba ko 'yan fashi, ba ko gajiya, tafiya nake ni kaina ban san matsayina ba a raye nake ko a mace? Ban san ina na nufa ba ko ina na dosa. Ashe cikin Kano na nufa a cikin kasuwar Singa Asuba ta yi min na fadi a bakin hanya sumamme." Ya dubi Zahra ya ce "Daga nan Allah ya hada ni da kakanki, mahaifin Mamanki Samira. Allah ya yi wa Alhaji albarka shi yasa aka dauke ni aka kai ni asibiti aka yi ta qaramin ruwa har kwana uku, sannan aka sallamo ni ya fara tambaya ta garinmu. Ban fada masa komai ba na dai ce masa ban san kowa ba anan kuma ba ni da inda zan je sai dai ya dauke ni aiki. Ya saka ni a cikin yaransa muka fara aiki, sai ya yaba da hankalina gashi kuma ni kadai ne na iya rubutu shi ma bai iya ba. Don haka ya ja ni a jiki. Ya na aikena har cikin gida in kai sakon cefane, ko kuma kafin ya fito kasuwa ya kira ni in shigo har falonsa in yi masa lissafi da cike-ciken takardu. Anan sai Allah Ya jarrabi Samira 'yarsa da tsananin sona, nima ina sonta, amma abun da kamar wuya a ganina ba zai yiwu ba. Babu abin da ya gagari Ubangiji, Alhaji ya amince min na aui Samira, amma sai da ya tisa ni a gaba na kai shi Mangono ya ga mahaifana. Sai da Samira ta qare sakandire aka yi aurenmu lokacin tana da shekaru goma sha shida, ni kuma ina da shekaru ashirin. Ya ba mu aron gida muka zauna ina zuwa kasuwa na ci sa'a na sami mace ta gari mai tsananin sona, mai lallaba ni, mai ba ni hakuri, idan ta ga ina cikin damuwa. Amma duk da haka ba na jin dadin rayuwata. Wata rana na hadu da wani babban ma'aikaci ya yaba da hankalina ya samar min tallafí daga gwamnatin tarayya. wato (Scholarship) zuwa qasar England don yin degree. Gwamnati ta dau nauyina da matata muka tafi England har tsawon shekaru uku a can muka haifi 'yar mu ta fari na saka mata sunan Zuhuriya, muke kiranta da Zahra, ko in kira ta da Yagana. Tun daga lokacin Allah Ya fara buda min hanyoyin samu. Na dawo Nigeria na fara aiki ina kasuwanci ina zuwa England ina saro kaya ina shigowa da su. Har rana irin ta yau kullum ci gaba nake samu a rayuwata. Na shiga cikin matsananciyar fargaba a lokacin da na fara ganin Sajida a rayuwata, saboda tsananin kamar da ta yi da Zuhuriya sak kamar an tsaya kara" Sajida ta dago da sauri ta dubi Bakura ta dafe kirji ta ce "Ni, ta yaya zan yi kama da Zuhuriya?" Bakura ya gyada kai ya ce "Haqiqa duk wanda ya san Zuhuriya, yaga Sajida sai ya fadi haka. Wannan dalili yasa na bi Sajida gidansu, dan ganin su waye iyayenta, kuma ta ina ta samo kamannin Zuhuriyata. Na ga mahaifinta, na ga mahaifiyarta, na ji tarihinsu babu ta inda suka hadu da Zuhuriya. Hankalina ya qi kwanciya, tun ranar da na baro Cinkilawa ban sake komawa ba sai sanda na hadu da Sajida, anan na fara zuwa Yan lanya na tambayi wani tsohon makwabcin gidan malam Yahuza ya shaida min malam Yahuza ya rasu tuntuni matansa ma daya ta sami tabin hankali. Na tambaye shi game da abun da ya faru da Zuhuriya, sai ya ce Zuhuriya da 'yar da ta haifa suka qone a cikin dakin. Na fito daga Yan lanya na shiga Cinkilawa na tarar Innono ba ta garin, mijinta ya dade da mutuwa. Na tambaya ko Zuhuriya ta bar 'yar da ta haifa? Sai aka ce min ai namiji ta haifa, shi ma daga baya yaron ya mutu. Na rasa gaskiyar magana, hankalina ya
Chapter 62 · 0% Book details