Sashe 28
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
iske a falo, ta na ganin goshin Zahra sai ta dauki salati mai hade da kuka dadin dadawa ma bushashshen jinin da ta gani a jikin tufafinta. Abinda ya fara fado ma ta a rai shine ko hadari ta yi a hanya, amma ganin ma aikantan shagon sai ta fara tunanin ko a bakin kantin hadarin ya faru. Zahraa rungume mahaifiyarta tana rusa kuka, Samira ta zaunar da Zahra akan kujera itama kukan ta fara yi tana tausayin 'yarta tana tausayin kanta, domin arangamarta da Bakura ba zai yi kyau ba dalilin da ya sa ta bari Zahra ta dauki mukullin motarta ta fita ita kadai. Ga gargadin da yake yi mata cewar ta sa ido sosai akan Zahra, yana fatan, yana kumå addu'a Zahra bata fita ta raqashe a bayan idonsa. Cikin karkarwar jiki Samira take tambayar ma' aikatan da suka rako Zahra har su hudu. Daya daga cikinsu ya ce "ina jin tuntube tayi ta daki jikin kanta gwangwanin madara ya datso mata a goshi." Daya yayi karaf ya ce "ba gaskiya ba ne babu yadda za' ayi dan mutum ya dan daki kanta gwangwani ya fado, wannan ba abin rufa-rufa ba ne don idan muka rufa mu kuma zai iya shafar aikinmu, idan maigida ya zo zai iya korar dukkan mu ya ce bama lura. Akan idon Ibrahim abin nan ya faru dan haka Ibrahim ka yi bayani." Ibrahim ya matso ya ce "îna biye da Zahra a baya sai wasu 'yan mata suka hau zaginta sai ta ce da ni in matsa daga wajen zasu yi magana. Matsawata ke da wuya sai na ga daya daga cikin 'yan matan tayi tsalle ta ciccibo gwangwanin madara qato ta kirba mata a goshi amma ko Sama ko qasa ban ga ta inda 'yan matan suka bi suka gudu ba." Samira ta juya ta dubi Zahra ta ce "wadanne 'yan mata ne waɗannan? Me kika yi mu su haka har da zasu fasa miki kai? Ke da baki da abokin fada tun ki na yarinya. Me kika yi musu har ya tunzura su suka fasa miki kai?" Zahra hawaye take ba tare da ta iya bada amsa ba. Ana cikin wannan hali Bakura ne ya kira wayar Samira tana jin ringing sai ta ce "yauwa ga Abbanki nan ya kira bari na fada masa tunda ni kin qi fada min gaskiya." Samira na dannawa ko gaisawa basu yi ba ta ji Bakura ya na fada har da kumfa baki, hankalinsa a tashe. Ya ce "wai me yake faruwa ne aka yi min waya aka ce wata yarinya ta fasawa Yagana kai a cikin Super Market? Wacce yariya ce, kuma waye Ubanta a Kano?" Samira ta ce "yanzun nan su ka shigo min da ita ban ma gama jin abinda ya faru ba. Yagana kuka take ta qi yin magana, sai dai ga Ibrahim wanda abin ya faru akan idonsa zai yi maka bayani." Samira ta miqawa Ibrahim kan waya, Ibrahim ya karba gami da yin sallama. "Me ya samu 'ya ta?" tambayar da Bakura ya yiwa Ibrahim kenan kafin ya amsa masa sallamar. Ibrahim ya hau bayanin iya abinda ya gani akan idonsa. "ina yarinyar take?" in ji Bakura. Ibrahim ya ce "kafin na ankara na neme su na rasa sun gudu." Nan da nan Bakura ya hau Ibrahim da bambamin fada yi yake yana dukan teburin da yake gabansa. Ya na yiwa Ibrahim barazanar rasa aikinsa akan wannan sakacin da yayi. Malam Yakubu ne a zaune a gefen Bakura yana lallashinsa, yana bashi baki cewar ya kwantar da hankalinsa abi abin a hankali. Bakura ya kashe waya sai huci yake yi, wani gumi mai zafi ne yake ta keto masa. Ya ce da Malam Yakubu "wallahi, wallahi sai na dau fansa akan wannan yarinyar da ta bi Yagana har cikin kantin Mahaifinta ta dau katon gwangwani ta fasa mata kai, sai na ga mahaifin yarinyar nan inji ko shine ya sa take rashin mutunci a Kano. Ban taba rigima akan yarana ba, ban taba rigima da kowa ba tun sanda na zo Kano, amma zan fara akan wannan yarinya." Malam Yakubu ya ce "daman bai kamata a bar maganar nan ba, saboda idan aka bar maganar nan gaba waya san abinda zata yi mata idan taga ba'a dau mataki ba, amma abi abin a hankali saboda yanke hukunci cikin fushi yana jawo dana sani ko nadama." Bakura yayi ajiyar zuciya ya ce "to malam, na ji zan bi a hankali amma Ko me Yagana ta yiwa yarinyar nan bai kamata ta bi ta har cikin shagona ta fasa mata kai ba, har da jini face-face. A iya sanina Yagana ba ta fada, ko an tsokane ta bata tankawa. Ba ta iya fada ba, bata ma san yadda ake yinsa ba. Haka kawai ta bi ta har cikin kanti ta fasa mata kai ni kuwa sai na ji da wa take taqama a qasar nan kuma sai na ga mahaifinta inji dalilin da yasa 'yarsa ta fasawa 'yata kai, shari'a ni da shi babu mai saka ni na janye." Malam Yakubu ya ce "tabbas kar ka bar maganar nan nima ban goyi da bayan ka bar maganar nan ba,zan tambayi Yagana da kaina ta fada min gidan su Yarinyar sai mu je har da ni mu ji dalilin da yasa 'yarsa ta fasawa Yagana kai. Idan ya nuna 'yarsa bata yi laifi ba ko tayi daidai to ya cancanci a kai maganar kotu suyi musu tsakani." Bakura ya gyada kai ya ce "Allah ya kai mu Kano lafiya." Malam ya ce "amin Allah Ya kai mu lafiya." Na