← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 64

Sashe 45

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*** *** ***
Haka gidan Bakura ya kasance, tamkar gidan 'yan adawa. Bakura da Samira ba dadi, tsakanin Sajida da Samira da 'ya'yanta ba dadi. Tsakanin Bakura da Sajida ba dadi. Sajida ta sake kudirar sai ta damula gidan gaba daya, don haka rashin mutunci kala-kala, na yau daban na gobe daban, sai futsara da tsiwa take yi wa Bakura, ta yi wa matarsa.
Samira ta ce ta gaji, don haka babu ruwanta da abincin Sajida, balle ta taka qafarta a dakinta. Grace ce Bakura ya wakilta kacokan ta kula da ci da shan Sajida da kula da gyaran dakunanta da wankin bandakuna. Kai hatta undies dinta Bakura ya ce Grace ta dinga wanke mata zai biya.
Tsawon wata guda kenan da zuwan Sajida bai fi sau biyu ba Zahra ta ga Sajida. Shi ma a qofar dakin Sajida suka hadu, Sajida ta leqo kiran Grace, Zahra kuma ta zo wucewa za ta shiga dakinta suka yi kallon- kallo kowa ya dauke kai.
Duk ranar girkin Samira, Bakura zai kame a dakinsa, Samira ta zo, amma ranar kwanan Sajida sai dai ya bi ta daki, shi ma datse qofar falon take sai dai ya shigo ta qofar baya wacce shi kadai yake da mukullin. Kada ku ce idan ya shiga dakin wani abu ne zai faru, a'a a gaba take sa shi sannan ta danno lambar Abdulmajid su yi ta soyayya don ta saka shi takaici dan idan ya gaji ya sake ta, amma sai ta ga Bakura ko damuwa ba ya yi. Kai har in credit din wayarta ya qare sai ta ga ya zaro recharged card na dubu daya da dari biyar ya ba ta ya ce ta ci gaba da wayarta, ya na gefe yana kallonta cike da murmushi.
Al'amarin Bakura wani lokaci yana ba ta tsoro, don ba ta san abinda yake hada mata ba, dan wannan kasaqen da ya yi mata akwai magana.
Sajida ta ga an doshi watanni biyu da aure, babu alamar gajiyawa a tare da Bakura, ba shi da niyyar jin haushi, balle ya sake ta.Sai ta yi yunqurin hada kaya ta gudu cikin dare, amma abu ya ci tura.Ta kalli tsawon katangar gidan nan ta ga ba irin katangar gidansu ba ce wacce take iya haurawa ba. Ta nufi get ta tabbatar masu gadi su na aikinsu tun karfi ko da yaushe get a datse yake da manya-manyan kwado. Kafin a bude maka get sai sun jero maka tambayoyi, balle a ce su ganta da kayanta a hannu ba a mota ba ta ce za ta je unguwa, ko daya ba za su bar ta ba. Gashi an hana kowa zuwa daga gidansu.

*** *** ***
Wata rana da daddare, dare har ya fara nutsawa Bakura bai dawo gida ba. Sha daya na dare, har ta wuce ba Bakura babu wayarsa, don haka hankalin Samira da 'ya'yanta ya tashi, ko barci suka kasa yi. Yi suke su na qara yi wajen buga wayarsa, amma wayar a kashe. Babu abokinsa da ba ta kira ba, sai su ce ba sa tare da Bakura a yau. Sha biyu daidai wayar Samira ta yi qara alamar ana kiranta, ita da Zahra suka hau rige- rigen dauka. Samira ta danna wayar, gami da kadawar hanta da fargaba. Ta fada "waye yake Magana?"
Cikin harshen turanci mutumin ke magana da alama Inyamuri ne, ya fara da gabatar da kansa. Ya ce, "Sunana Doctor Isreal daga International Hospital. Dan Allah ina magana da Samira ne Mrs. Bakura ne?"
Ai tuni Samira ta rusa kuka ta fara kwakwazo. "Doctor ni ce Samira. Me ya faru da maigidana, ya mutu ne?"
"Bai mutu ba, amma ya sami rauni." sai ta sake fashewa da kuka ta ce, 'Hatsari ya yi ne?"
Ya ce"A'a an kawo mana shi dai ana tunanin yan fashi ne suka dake shi har an farfasa motarsa. Ki kwantar da hankalinki ga shi nan ya miqe yana magana, shine ma ya ba ni lambarki ya ce in kira kı."
Doctor ya sakawa Samira muryar Bakura yayin da ita ma ta danna speaker yadda yaranta za su jiyo muryar mahiafinsu, don su dukka kuka suka zo suka kewaye ta su na yi.
Cikin kuka suke kiran. "Abba, Abba me ya faru da kai?"
Cikin sanyin murya Bakura yake lallashinsu fadi yake, "Na ji sauki, ku daina kuka."
Dukka wannan abinda ake Sajida na bayansu a tsaye ta jingina à jikin bango ta kama kirji ta qame kamar soja. Da alamar akwai sanyin jiki a tare da ita.
Amma da ta ga sun juyo gaba daya su na kallonta, sai ta tabe baki ta harare su sama da qasa ta wuce zuwa dakinta, don kada ma su đauka ya dame ta.
Samira ta aika Zahra da Abubakar, Boy's quater su taso Lurwanu direba ya zo ya kai su asibiti wajen Bakura. Da gudu Zahra da qaninta suka nufi Boy's quater suka taso shi, a gigice ya dauko mukullin mota ya fito. Ba tare da bata lokaci ba Samira da 'ya'yanta suka duru a mota suka nufi asibiti, sai addu'a suke su na koke-koke a hanya.
Sajida na shiga falonta ta jawo wayarta ta bugawa Abdul majid, zuciyarta cike da 6acin rai, domin tana zargin da sa hannunsa a cikin wannan al'amari,
Ya na amsawa ta harbo masa wannan tambaya. "Abdul majid me kasa a yiwa Bakura?"
Ya tabe baki ýa ce "Me ki ka ga an yi masa, wannan wacce irin tambaya ce kike yi min? Kar ki raina min hankali mana."
Ta fada cikin tsawa da bacin rai, "An ce 'yan fashi sun tare shi sun dake shi, har sun fasa masa mota. Ina tunanin kai ne kasa a yi masa haka."
Ya ce, "Ki daina tunanin nasa an dake shi, nine da hannuna na tare shi ni da su Shehu abokaina muka farfasa masa kai dazu da magruba a Hotoro G.R.A. Kin fara sonsa ne, ina ruwanki ko mutuwa ya yi?"
Ta fada a fusace, "Ka ga Abdul majid ba na son haka, ya za ka nemi ka kashe mutum ba da hakkinsa ba. Me ya yi maka? Mutumin nan ya ba mu damar mu yi magana har ma katin waya yake siya ya ba ni in kira ka. Me ye laifinsa?"Kai ka fi cancanta..

Gashinta kuwa mai laushi ne aka gyara aka zubo mata da shi har bayan qeyarta, aka nade mata daurin dankwalin leshin a samansa, sannan aka yafa ma ta mayafin da ya dace da leshin wato mai ruwan goro, takalmi ma kalarsa ne, yayin da aka feshe duk illahirin jikinta da turarurruka masu qamshi na cikin lefe.
Aka ruqo ta zuwa tsakargida aka zaunar da ita akan wata doguwar kujera aka fara daukar hotuna. Babu yadda Sajida za ta yi, domin an ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma zuciyarta cike take da baqin ciki da damuwa. A zaune take tamkar gunki, sai kallon mutane take sasarai kai ka ce ba ta da laka a jikinta. Duk sanda ta tuna ita da Abdul majid shi kenan sun rabu sai ta ji zuciyarta ta harba kamar ana harba bindiga. Idan ta tuno mutumin da aka daura mata aure sai ta ji ta qara tsanarsa.
Ta ce a ranta "Lallai kuwa mutumin nan ya yi kuskuren aurena. Iyayena sun yi kuskuren ba shi aurena, sun yi kuskuren karbar dukiyarsa saboda asara ce. Sai na zame masa tamkar kunama mai cizo a shimfidarsa. Zan zame masa duhu alhali da hasken rana. Sai na disashe farin cikin zuciyarsa, ya koma tsananin baqin ciki da damuwa kamar yadda ya sakani ni da Abdul Majid dina. Sai na fardo wannan kyakkyawar kwaryar tasa da yake ji da ita wacce ya saqale a ragaya, idan ta fado qasa ko ba ta fashe ba, zata yi gagari a tsakar gida. Sai na yaqi uwar gidansa na hana ta sukuni a gidanta. Sai na takurawa duk wani mai rai a gidan in ya so idan ya gaji zai sake ni, ko ya kore ni, sai ya ji ya tsani zama da ni."
Sajida ta yi murmushin mugunta, wanda har wushiryarta ta fito ta girgiza qafa, 'yan biki suka dau shewa hadi da guda a tunaninsu amarya ta saki ranta ta amince da auren.
Chapter 45 · 0% Book details