← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 64

Sashe 57

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta dauki Bakura ta dinga goya shi, tana bashi abinci, za ta dinka masa Sabon kaya ya yi kyau, ita ma za a dinko mata sabuwar atamfa. Abin ka da marar hankali. sai ta hau murna tana tsalle, aka cika mata kwanon ta da abinci ta tafi ta bar shi. Hakimi ya sa aka kira Baban Bakura aka sanar da shi, shima ya yi amanna ya yi murna da wannan taimako da aka yi masa. Daman iyayen Fatukamba sun rasu, yayanta ne guda daya a garin mai suna Bukar Shima hakimi ya kira shi ya shaida masa cewa Zuhuriya 'yarsa ce a Kano ba ta da d'a tana so ta riqe Bakura za su dinga zuwa akai-akai yana ganinsu. Bai yi musa ba, saboda shi ma baya taimakonsu korarta ma yake ita da danta daga gidansa, don haka ya yi farin ciki da jin haka. Kafin mu bar Mangono Bakura ya canja, Zuhuriya tana yi masa wanka tsaf-tsaf, ta samar masa kwancen riguna da wanduna a wajen matan hakimi. Abinci kuwa idan ta dinga tura masa bai san ya qoshi ba sai an hana ta. Goyo kuwa riqi-riqi ko sallah a bayanta yake yi. Farin ciki da shaquwarsu kuwa cikin 'yan kwanaki sai ka rantse sun shekara da sabawa ko ka zata ita ta haife shi. Ni kuwa haushinta nake ji don babu yadda zan yi in hana ta, so nake mu je gida in mata duka. Abinda babba ya hango yaro ba zai hango ba ko da kuwa ya hau bishiyar rimi. Kunyar sirikina nake ji Hakimi da na hana ta daukar yaron nan, idan na hana ta gari gaba daya za'a ce baqin hali gare ni, daman na yi qaurin suna a wajen dangin miji su na cewa ba ni da kirki, don a garin muka yi zaman zauna har mijina ya mutu mahaifin Zuhuriya. Ranar da za mu tafi, jama'a suka raka mu har tasha su na ta shi albarka su na yaba yadda Bakura ya canja cikin dan qanqanin lokaci. Jama'ar gari kacokan sun yi amanna da daukar Bakura. Ni kuwa wacece da zan ce ban yarda ba? Amma tun daga mota na fara dunguri, ina rankwashi, ina zagin Zuhuriya. Bakura ba zan boye maka ba idan ma na qi fada ai ka san komai, tun da tun baka fahimta har ka girma ka fahimci bana son zamanka da mu. Bakura ka yafe min, domin na zalunce ka, na zalunci kaina." Iya Azumi ta rushe da kuka Hawaye ya surnano daga idanuwan Bakura Ya ce "Ka da ki yi küka Innono, kada ki damu na yafewa wasu ma a dalilin Zuhuriya balle ke da kika haife ta da kanki." Babu wanda idonsa bai cika da hawaye a wajen ba, don tausayin Bakura. Hatta Sajidar da take iqirarin ta tsani Bakura kamar yadda ta tsani mutuwarta dan yaron nan Bakura ya bata tausayi har sai da hawaye ya surnano daga idanuwanta. Bakura ya ci gaba da cewa "Mu ka isa Cinkilawa, garin da Zuhuriya da mahaifiyarta suke aure a nan ne na fara bude ido, na fara sanin menene rayuwa. Sunan mijin Innono malam Audu ba shi da wata mata sai Innono. Sunan mijin Ummata Zuhuriya kuma Hashimu, shi ma yaro ne ita ce matarsa ta farko. A da an ce su na zamansu lafiya, amma tunda ya kyalla ido ya ga Zuhuriya da yaro ta yi masa bayani sai ya bata rai ya nuna baya so, ba zai riqe ni ba. Ita kuma ta ce duk wanda baya sona ba ta sonsa, dan haka sai dai ya sake ta. Daga nan dai zama ya rikice kullum ba dadi, domin duk wanda ya taba ni sai inda qarfinta ya qare da yake ita ma in an taba ta ba kyalewa take yi ba, akwai ta da tsiwa, yanzu nan idan ta jiyo kukana zata figo gyale ta fito a yi fada da wanda ya dake ni ko da iyayen yaran. Daga qarshe dai zama ya wi dadi, Hashimu ya saki Zuhuriya a kaina. Muka kinkimo kayanmu a amalanke da Magaruba muka taho gidan Innono. Tana ganinmu ta ce "Bakura ya kashe miki aure ko?" Ta kwana tana dukanmu, ni da Zuhuriya muka takure a jikin katanga kamar wasu qadangaru ta hana mu abincin dare har na yi barci a haka, amma sai da Zuhuriya ta tashi da tsakar dare ta gutsirar min tuwon dumame ta tashe ni ta ba ni a baki har na qoshi." Samira ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah Ya saka mata da alkhairi." Bakura ya ce" Amin, na gode Samira." Ya ci gaba da cewa "Haka muka yi zaman zawarcin nan da wahala, saboda tsangwama. Abin ka da qauye da zarar an ji bazawara tun bata gama iddah ba zawarawa sai su fara kawo hari balle Zuhuriyar da duk surquqin qauyukan nan tafi kowacce mace kyau. Idan bazawari ya zo sai ta aika ni in leqa in gani da jaki ya zo ko keke, idan jaki ne ko keke sai ta kama hannuna mu fita da gudu ta ce ya yi ta dana ni akan jakinsa ko keke, ina jin dadi. Idan kuwa ba shi da jaki ko keke, daman ba za ta fito ba. Wannan al'amari namu yana batawa Innono rai, wanda take kiransa rashin hankali. Don haka kullum fada take da kumfar baki a kan Zuhuriya ta fitar da miji ta yi aure. Ni kuma ta mayar da ni gidanmu kada in sake kashe mata aure. Ko kadan Zuhuriya ba ta yarda da zancen mahaifiyarta ba, ta nuna akan ta mayar da ni gara ta goye ni mu tafi mu bata a rasa mu. Duk wanda ya fito aurenta sai ta sanar masa cewa tana da d'a da shi za ta je, idan ya ga bai yarda ba kada ya sake dawowa. Da yawa idan sun tafi basa dawowa, amma Mutari wanzami ya yarda ya amince zai aure ta tare da ni, sunan qauyensu B'alle bantai, qauye na kusa da Cinkilawa daga kudu. Ya kawo kayan aurensa atamfa uku, sai sadaki a kowacce atamfa sai da aka dinka min ma'ana anko muka yi ni da amarya. Aka daura aure muka kwashi kayanmu kacokan muka koma qauyen Balle bantai muka bar Cinkilawa. Sabuwar rayuwa a Balle bantai, ga uwar miji ga kishiya, gani kuma agola dan haka ba zaman lafiya a gidan. Zuhuriya ba ta da aiki sai goyona ko'ina rabe- rabe abun ka da marar jiki har rinjayarta nake kamar Za mu fadi, ga shi duk atamfar da za ta saka anki muke nima irinta take sa tela ya dinka min riga da wando. Na Zama dan shagwa6a idan na ga dama sai in qi taka qasa in ce sai dai ta goya ni, abinci in qi ci sai dai ta bani a baki. Wannan al'amari nawa yana bawa mutanen gidan nan haushi. Uwar mijin har wani suna ta saka min wai "tarar ni wuce ni. Wato na zo na sami 'yan gida har na fi su zaqewa. Mutari wanzn ya na sona, saboda yana son Zuhuriya, dan haka Zuhuriya ita ma take sonsa saboda yana sona. Amma kishiyarta Rahi da mahaifiyarsa Ingade ba sa son ganina a gidan. Don haka fadan safe daban, na rana daban. Idan ranar girkin Zuhuriya ne abinci tun yana kan wuta ake fara ba ni tabi, idan ranar girkin Rahi ya zagayo ba ni da kashi sai dai Zuhuriya ta ba ni nata in ci, idan na qoshi ta ci sauran idan na cinye dukka ta kwana da yunwa. A haka a daddafe muka yi wata takwas a Balle bantai, sannan uwar miji ta tubure ta tilasta dole har sai da danta ya sake mu. Dolensa ya sake ta yana son mu a nan ma Zuhuriya ba ta samu ciki ba. Ba na mantawa da hantsi rigimar ta taso don haka da muka hada kwanukanmu na tsakar gida muka datse a daki, sai yan kayanmu seti biyu muka kullo a dankwali muka taho. Da qafa ake tafīya a lokacin, duk nisan tafiya babu mota. Don haka muka kamo hanya zuwa Cinkilawa tana riqe da hannuna idan na cije na qi tafiya ta goya ni, idan ta gaji da goyon ta dauke ni, haka muka yi ta yi. Na dube ta na ce "Juhuliya, lokacin ba na iya cewa Zuhuriya ta ce na'am Bakura. Na ce, "Tsoro nake.ji kada Innono ta dake mu." Sai ta fashe da kuka, don tausayina ba ta damu da dukan da za a yi.mata ba, ni take tausayawa ta san akwai matsala, idan ta je gida ta ce an sake ta, kuma su ji labari a kaina ne. Innono za ta tubure ta ce sai ta mayar da ni garinmu ni nake hana ta zaman aure. Dan haka muka yanke shawarar kada mu koma gida mu yi zaman mu a cikin dawa qarqashin wata bishiya. Muka yini a dawa muna tsalle-tsalle, ta dora ni akan wuyanta in tsinko mana dinya, aduwa, dorawa, tsamiya da dai sauransu. Idan na kasa tsinkowa ita sai ta hau bishiyar ta tsinko mana. Haka muka, yini muna ta walagigi har Magruba. Akwai gidan gonar wani tsoho a kusa da inda muke. Ashe tun da safe yake lura damu ya ga har rana ta fadi ba mu da niyar tafiya, don haka ya zo da bulala ya ritsa mu. A tunaninsa Zuhuriya yayata ce aka aike mu da qulin kaya muka zo muka zauna muna wasa, dan haka yake yi mana fada mu hanzarta tafiya inda aka aike mu. Simi-simi ya saka mu a gaba har kusa da garinmu Cinkilawa ya raqe da bulala. Kan ka ce kwabo an hango mu, yara suka hau tsalle su na fadin "Ga Zuhuriya, ga Bakura." Labari ya iske kunnen Innono, tana jin haka ta san ba zuwan lafiya ba ne da magrubar nan, dan haka ta girka kujerarta a tsakar gida ta tanadi bulalarta ta na jiranmu. Mu ka qi shiga cikin gidan muna jikin katanga a labe. Can Zuhuriya ta dora ni a wuya na leka cikin gidan daidai lokacin muka yi ido hudu da ita. Ta ce "Waye wannan?" Na ce "Bakura ne, Inonono an sake mu." Su Malam suka kwashe da dariya, har da Bakura. Da alama labarin nan ya na ratsa zuciyar duk
Chapter 57 · 0% Book details