← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 64

Sashe 27

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** *** **** Zahra da mahaifiyarta Samira kuwa su na kano Su na ta faman shirye-shiryen walima. Don qarfin hali har wani dan qaramin katin gayyata Zahra ta buga ta rarrabawa qawayenta na makaranta. Ranar asabar ne ranar da za'ayi walimar. Don haka ranar Juma'a da yamma washegarin ranar da za'ayi. Samira ta iske Zahra a falonta a zaune ta na kallo. Ta ce da ita ta je Zuhuriyya super market ta hado mata kayan qamshin girki (spices) kamar curry, thyme, dakekkiyar citta da dai sauransu. Zahra ta shirya tsaf ta fito caras sanye take da wani dandantsetsen leshinta shudi anyi masa zanen fulawa ruwan goro. kallo daya za ka yiwa leshin ka gasgata tsadarsa duk da daman dallar aka siyi leshin idan aka kiyasta kudinsa zai kai Naira dubu dari da tamanin. Kwararren telan da ya sarrafa dinkin leshin da ace qasar America zata sami labarinsa data dauke shi aiki a kamfanin dinka kaya (English wears). Domin idan ka kalli kayan a jikin zahra sai ka rantse daga kamfani leshin ya fito a dinke. Yankan siket din das a jikinta haka rigar, abinka da marar jiki, doguwa santaleliya kai ka ce taliya ce ke nutso a cikin ruwan zafi, idan Zahra ta na tafiya. Duk da tsayin da Allah yayi mata ta qara da wani cogen takalmi mai tsinin gaske a qafarta shima takalmin kalar ruwan goro ne. Ta nada daurin dankwali a gaban goshi, gashi keyarta kuwa lallausa mai raushi ne ta tufke shi da ribbon ruwan goro. Ta dauki dan siririn mayafi ta yafa a jikinta. Ta na rike da mukullin mota a hannunta. Samira ta dubi Zahra ta yi murmushi ta ce "baby kinyi kyau yau sosai. Ko za ki bar leshin nan gobe ki saka? Kamar zai fi na gobe kyau." Zahra ta ce "a'a mama kin manta kudinsu ne? Ai yellow da zan saka gobe ya fi wannan tsada kudinsa da na kiyasta naira dubu dari biyu ne da hamsim wannan kuwa dmdubu dari da tamanin ne. Kin ga ai ba kudinsu daya ba. Allah Ya kaimu goben shima za ki ga yadda zai yi min kyau." Samira ta ce "Magaji deriba ne zai kai ki ko?" Zahra ta ce " sabuwar motarki Discussion continues zan tuqa da kaina." Samira ta ce "ba wai ban yarda da tukinqinki ba ne amma fa har yau mahaifinki bai san kin koyi tuqi ba, ka da ki je wani abu ya faru Allah ma Ya kiyaye ya ce yaya aka yi ma ki ka fita ke kadai?" Zahra ta ce "Allah ma Zai kiyaye yanzu zan je na dawo." Samira te ce "Allah ya kiyaye mamana." Zahra ta saka bakin gilashinta saboda hasken gari, ta sakala hands free a kunnuwanta saboda amsa waya, ta shiga tsaliliyar motar nan mai launin silver nufi ZUHURIYYA SUPER MARKET. Daf da qofar Zuhuriyya Surper Market ta ja ta tsaya a inda ta dubi gefanta wata baqar mota ce qirar Brama mai bakin gilashi, ko kafi quda na ci ba za ka iya hango abinda yake ciki ba. T Tabbas ita ma motar ta hadu domin irin sautin kidan da yake tashi daga cikin motar da irin daukar idon da motar ke yi saboda da sheqi. Kamar yadda shekin motar Zahra take daukar idanuwan masu kallonta har 'yar qarama rigima ce ta tashi tsakanin saurayi da buduwar da ke cikin motar saboda yadda yake kallon Zahra har da leqe. Ba tare da Zahrar ta san abinda ke gudana ba. Zahra ta yunkura ta fito daga cikin motar in da ta danna remote alamar ta rufe motar. Ta na fitowa ta fuskanci wasu 'yan mata guda biyu sun fito daga cikin wannan baqar motar, daya daga gaba ta fito daya kuma daga gidan baya. 'Yan matan dukkansu sanye suke da wandon jeans da riga iya gwaiwarsu, sai dan gyale yalolo a maqale a kansu da cogen takalma a qafafuwansu. Nan da nan suka dunguma tare da Zahra suka shiga cikin Super market din. Daga yadda 'yan matan nan biyu suka ga ma'aikanta super market su na dukawa Zahra su na kwasar gaisuwa Hajiya sama Hajiya qasa sun san tabbas yarinyar nan 'yar wani ce a qasar nan. Inda su ka sake tabbatar da hakan sai sanda suka ji ta umarci daya daga cikin ma' aikatan cewar ya samu leda ya je ya zabo mata spices kalą-kala masu qamshi daban-daban kamar roba ashirin ya kai mata mota. 'Yan matan biyu sun ci gaba da zazzagayawa su na zazzabar abinda suke so. Kicibus su ka yi da Zahra a daidai kantar greeting cards. Yayin da su dukka ukun suka duqufa wajen karantawa don su zabi wanda yayi dai-dai da kalaman da suke buqata, kamar daga sama kunnuwan Zahra su ka jiyo mata daya daga cikin 'yan matan ta ce da dayar. " Iyayye, kin ga wani kati wanda yayi daidai da wanda zan bawa Abdulmajid." Jin sunan Abdulmajid ne ya sawa Zahra wata mummunar faduwar gaba ta dago da sauri ta dubi mai maganar. Zahra ta zare bakin gilashin dake fuskarta ta dube ta sosai inda ita ma mai maganar ta tsaya cak ta na duban Zahra yayin da su ka dauki 'yan dakikai ba su daina kallon juna ba kowa ya na qoqarin tuno inda ya san wannan fuskar. Lokaci guda kwakwalwarsu ta sanar musu cewa wannan Zahra ce, kwakwalwar Zahra ta sanar mata wannan Sajida ce. Qara-qara- qa-qa, ga Zahra, ga Sajida. Ya za'ayi kenan'? Zahra ta yi murmushi ta ce "kamar na sanki, ba ke ce Sajida ba?" Cikin gadara Sajida ta ce "Sajimajid ce, kwarai ashe kin tuna ni kamar yadda na tuna ki Zahra. Ina neman ki daman tamkar ruwa a jallo. Na dade ina addu' ar Allah ya nuna min irin wannan rana." Sai Zahra ta ji gabanta ya yanke ya fadi kan ka ce kwabo zuciyarta ta fara harbawa ta na dukan uku- uku. Ta tambayi Sajida cikin kidemewa "me ya faru?" Sajida ta yi murmushin mugunta ta dubi kawarta Iyayye ta ce "ki taya ni duban yarinyar nan, Ki taya ni fada mata ko ni wacece ko kuma yaya nake. Dan rainin hankali ma wai tambayata take me ya faru? Ba ta ma san me ta yi min ba ko? To bari ki ji Zahra babu yadda za ki yi da ni da Abdulmajid sai dai kallo da Ido babu mai raba mu, ke ko uban daya tsugunna ye haifeni ma sai dai ya yafe min amma ba zai iya hana ni son Abdulmajid ba." Gaban Zahra ya sake faduwa ta shiga saqe-saqe a ranta "tabbas Sajida ta ji labarin Abdul majid ya na yi min waya ada." Sajida ta rike kugu sai girgiza take tana huci tana hararar Zahra, tamkar mayunwacin zakin da yaga nama. Zahra ta juya ta dubi Ibrahim ma'aikacin da yake biye da ita a baya. Ta ce ya matsa ya bar wajen ta na son ta yi magana da qawarta, ya amsa mata cikin ladabi ya tafi da sauri ya bar wajen. Zahra ta matso kusa da Sajida ta ce "Sajida, wallahi ban san Abdulmajid ba, ban taba sanin yaya kamanninsa su ke ba, ba ni da wata alaqa da shi dan haka ne ma nake mamakin tuhumar da kike yi min a akansa." Sajida ta ji tamkar Zahra ta soka ma ta mashin wuta a qahon zuci. Ta fada a fusace "dubi bakin qofar shigowa." Zahra ta waiga da sauri, sai ta hango wani dan kyakykyawan saurayi a tsaye. Sajida ta ce "to Abdul majid dina kenan, ki koma ki sake fadawa Babana kin ganmu tare." Sajida ta kwallawa Abdul majid kira nan da nan ya qaraso in da suke. Ta ce da shi "ga Zahrar da nake fada maka wacce na taba kiranka da wayarta, daga qarshe ta hada min tuggu wajen Baba." Abdulmajid ya ji gabansa ya yanke ya fadi kamar yadda na Zahra yake faduwa lokaci guda suka zubawa juna ido har wani lokaci mai dan tsawo kowannan su ya na tunani a ransa. Abinda ya fara fadowa Zahra a ranta sai kalmar "inna lillahi wa'inna ilaihi rajiî'un. Yau me ya ke shirin faruwa da ni ne haka? Na rabu da Abdulmajid a waya ga shi na gan shi yau a zahiri?" Abdulmajid kuwa kan ka ce kwabo farin ciki ya lullube zuciyarsa da Allah Ya nuna masa Zahra a zahiri, kwakwalwarsa ba ta taba kwatanto masa haduwar Zahra ta kai haka ba, ba makawa Zahra itace irin kalar macen da yake burin ya mallaka a rayuwarsa.Tun fitowarta daga motarta tun ma bai san wacece ita ba zuciyarsa ta fara muradinta domin ta cika gaba daya abubuwan da namiji yake bukata a wajen mace. Nan da nan ya ji qafarsa ta kasa daukar jikinsa.Ya kidime ya fita daga hayyacinsa, amma gudun kada Sajida ta gane halin daya shiga sai ya juya da sauri ya fice ya nufi wajen motarsa ya shiga ya zauna ba tare da ya ce uffan ba. Iyayye ta ce "au daman itace munafukar da kike fada min ta na hada miki tuggu?" Idan hankalin Zahra yayi dubu ya tashi, nan da nan idonta ya cika da hawaye. Ta girgiza kai ta ce "actually I don't understand what is happening here...." Kafin ta rufe bakinta Sajida ta daka tsalle ta kinkimo qaton gwangwanin madara babba wato (giant size) ta datsa mata wajen kaifin a goshi, ko sakon daya ba'a qara ba jini ya wankewa Zahra fuska. Zahra ta kwalla ihu mai tsanani ta yanke jiki ta fadi qasa. Kafin kiftawar ido Sajida da kawarta Iyayye sun bace daga cikin kantin. Ma'aikatan shagon kacokan dinsu suka taru su ka zageye Zahra su na mamaki, su na al'ajibi yadda gwangwanin madara zai fado mata a goshi. Daya daga cikin ma'aikanta ne ya ke bayani wato Ibrahim cewar akan idonsa wannan budurwar ta jawo gwangwanin madara ta rotsa ma ta a goshi Sauran ma' aikatan gaba daya suka yiwa Ibrahim caaa akai su na tuhumar sa da cewar me yasa bai damqe yarinyar ba har ya bari ta gudu?" Hankalinsu a tashe suka garzaya da Zahra asibiti dan tsayar da jinin da yake zuba, aka kuwa ci sa'a ba a yi mata dinki ba, iodine da plasta aka saka mata aka liqe suka kawo ta gida. Samira suka
Chapter 27 · 0% Book details