← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 64

Sashe 53

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da kuka ta taho da sauri ta rungume shi, su duka kuka suke yi. "Kanka da zafi da alama ciwo yake. Mu je daki ka sha magani, ka kwanta." Samira ta ce da Balkura. Allahu Akbar! Soyayya saboda Allah ba karya ba ce. Ina masoyan zamani? Washe gari Sajida ta bude ido ta ga su Samira daram a zaune a gida suna ta hidindimunsu kamar kullum. Haushi ya rufe ta ta sake tsanar Bakura. Idan zai kwana yana yi mata magana ko kallonsa ba ta yi. Haka ta dinga takale-takalen masifa a cikin gidan nan babu mai kula ta, kasancewar Bakura ya ja musu kunne kar su kara sauraronta duk abinda za ta yi a zuba mata ido. Ta bangaji wannan, ta harari wancan, ta yi tsaki ta tsartar da yawu, babu wanda ya damu da ita. Har tsawon sati biyu Bakura na jinya ko sannu ba ta hada shi da Sajida ba. Ya warke ras ya ci gaba da harkokinsa bai taba cewa kowa ga abinda ya same shi ,ba, ko Sajida da Samira bai fada musu cewar ya san wadanda suka yi masa wannan ta'addancin ba. Haka Malam Yakubu ya yi ta bugowa Bakura waya yana tambayarsa lafiya kwana biyu bai ganshi ba, Bakura ya fake da cewa baya gari ya yi tafiya.Koda yaushe Malam na tambayar Bakura yanayin zamansa da Sajida, Bakura yana nunawa Malam ai yanzu Sajida ta yi laushi lafiya kalau suke zaune. Bai taba fadawa Malam halin da suke ciki ba, don haka hankalin Malam da matarsa a kwance. Ba su san Sajida na da waya ba, don haka har tsawon watannin nan uku ba su yi magana da Sajida ba, kuma ba su zo sun ganta ba. Malam ya hana kowacce qawa ta tako gidan Sajida ba, ko danginsu ma ya hana su zo. Ya ce abar ta sai ta shekara ta cire duk wani baqin rai, sannan a je a ganta sannan ita ma ta zo a gaisa. Yamma sakaliya Bakura ya dira a kofar gidan Malam. Malam ya yi marhaba da ganin Bakura, domin sun dade ba su hadu ba. Bayan an dau karatu, an yi sallar Magriba jama'a sun watse sai Bakura da Malam ne suke hira. Can Malam ya ce, "Af, na manta ban fada maka ba, Baquwa muka yi daga nesa kuwa take. Wata kakar Sajida ce, wacce ba su taba ganin juna ba tunda suke a duniya.Ta niko gari tun daga Gashuwa ta zo ganin Sajida ta sami labarin auren ta, duk da bata samu ta zo ba amma an kai mata kayan biki da atamfar da aka rarrabawa kakanni da iyaye, daga cikin atamfofin da ka ce a rabawa dangi sai yanzu ta sami damar zuwa." Bakura ya gyara zama, gami da cewa, "Allah sarki, tun daga Gashuwa ta zo ba ta samu ta zo bikin ba kenan?" Malam ya ce, "Ai ta tsufa ga ciwon qafa, shi yasa ba ta zo ba." Bakura ya ce, "Amma na ji ka ce ba su taba ganin Juna ita da Sajida ba. Baku ta6a tunanin kai ta ba duk tsawon shekarun nan? Ko dangantakar da nisa ne?" Malam ya ce "Wallahi dangantakar ta kusa ce, jini daya. Ka san kowa da halinsa, Furera wata irin mata ce ba ta da zumunci sosai, ba ta mayar da kai ta kaita Gashuwa ba." Bakura ya ce "Kakarta ta wajen dangin uwa kenan?" Malam ya ce "Kwarai, ta bangaren Furera suka hadu." Bakura ya ce "Idan na je wa zance mata sunanta, ko yanzu zan tafi da ita can su kwana su na hira?" Malam ya ce "Gobe da safe dai za su taho ita da Furera, don a yi mata bayani tunda ba ta san ta ba. Idan na fada mata sunanta ba za ta gane ba, amma ka ce mata kakarta Iya Azumi ta zo daga Gashuwa za ta zo gobe su gaisa." Bakura ya ce "Insha Allah zan fada mata, Allah ya kai mu goben, ni ma za su same ni a gidan, don ba na fita da wuri har sai wajen sha biyun rana nake fita." A haka Bakura suka yi sallama da Malam ya shiga motarsa ya tafi gida. A masallacin qofar gidansa ya jima yana tattaunawa da liman akan abinda masallaci yake buqata, sannan ya shiga gida. Bayan ya yi wanka ya ci abinci, sai ya tura qofar dakin Sajida ya shiga da yake yau ita ce da kwana, Samira tuni ta shige dakinta ta rufe. Kamar kullum, kamar yadda suka saba sai dai Bakura ya shiga dakinta, iyakacinsa kan kujera ya tsura mata ido yana kallonta, ita kuwa tana ganinsa sai ta danno lambar Abdulmajid dinta don ta ba shi haushi. Da alama ba ya jin haushin don har yau bai taba bata rai idan tana waya ba. Bai kuma daina kara mata recharg card ba, idan kudin wayarsu ya qare. Sajida ce a kwance a kan gado, ba tare da ta ji motsin shigowa ba ta ga Bakura a tsaye a kanta. Ta fada cikin tsiwa, "Malam ya aka yi ne ka shigo min har cikin daki ba izini, lafiya?" Ya yi murmushi ya ce, "Lafiya ranki ya dade, sako na zo in isar miki." Ta maimaita "Saqo, wanne iri?" Ya ce "Baba ya ce in sanar miki gobe da safe Umma Furera da wata kakarki its Azumi daga Gashuwa ta zo za su zo su ganki." Ta tabe baki ta ce "Duk danginmu babu Azumi, haka ba mu da dangi a Gashuwa, ka (tuno dai wajen wacçe aka ba ka sako, amma ba ni ba." Bakura yana niyyar magana sai Sajida ta jawo wayarta ta matso sunan Abdulmajid ta kashe murya ta ce, "Hello darling, ka kwanta ne?" Bakura ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar da zai bata ba. Ya tabbatar korarsa take so ta yi, don ba ta Son ganinsa. Ya wuce dakinsa ya kwanta yana juyi a gado ya rasa yadda aka yi rayuwa ta zame masa haka. Don haka yau bai ga ta zama ba, alwala ya dauro ya dauko jarbi mai dubu ya fara kiyamullaili yana tasbihi yana roqo, ya na hawaye a gaban Ubangiji da Ya yaye masa duk wata damuwa, hargitsi da sarkakiyar da take a tsakanin shi da Sajdia. Domin Sajida ta zame masa tamkar qadangaren bakin tulu, idan ya jefe shi ya fasa tulun, ko ya fada ruwa, ruwan ya lalace. Haka ya kai Asuba bai rintsa ba har sai da ya yi sallar Asuba ya je ya tashi iyalansa sallah, sannan ya dawo ya kwanta. Barci mai dadi ne ya sure shi mai hade da kyawawan mafarkai. Abun mamaki sai ya yi mafarkin Sajida da Zuhuriyya su na tare. Wannan mafarki ya bawa Bakura mamaki matuka, tun daga cikin barci har ya bude ido yana mamaki. Samira ya gani a tsaye akansa,ya sake gwale ido don ya tabbatar ita din ce kuwa? Kai ka fi cancanta
Chapter 53 · 0% Book details