Sashe 2
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Akan Titin Lamido cresent ya ke tafiya da zummar zai tafi masallacin Sheik Aminuddin don daukar karatun yamma da na bayan magruba kamar yadda ya saba zuwa duk ranar jumaa da ranar asabar.
Tafiya yake yana bin waqa wacce baitocinta ke burge shi saboda an zuba hikima da habaici da zambo. Kamar daga sama ya ga wata budurwa ta tsallako ba tare da ta duba titi kafin ta tsallako ba. Saura qiris ya buge ta sai da ya yi da gaske sannan ya iya taka burki gami da yin sauri ya dauke kan motar, saura kadan ya afka cikin kwalbatin da ke gefen hanyar. Irin qaran da burkin ya yi, hayaqi da warin taya kai ka ce gagarumin hadari aka yi Allah Ya sa babu mota a bayansa.
Ya jima a zaune a cikin mota zuciyarsa na bugawa ba tare da ya san abinda zai yi ba kuma amma ya ji dadi matuqa da ya ga yarinyar a tsaye ba ta fadi ba dan haka ya tabbatar bai taba ta ba. Ya ci gaba da yiwa Allah godiya a bayyane.
Abin mamaki yarinyar ba ta firgita ba ko kadan ta juyo ta dube shi a fusace ta harare shi ta yi tsaki ta ce " ka je a koya maka tuqi, banza kawai." Ta tsallaka da sauri ta ci gaba da tafiya har tuntube take yi, kallo daya za ka yi ma ta ka tabbatar a gigice take. Daga nan ya tabbatar abinda ya biyo ta ya fi kadewar mota firgici.
Ya ji kalamanta tamkar a mafarki yadda yarinya qarama 'yar cikinsa ta tsaya ta zage shi bayan laifinta ne ma.Ya ji zafin zagin nan sosai, ya tabbatar ba ta da tarbiyya. Amma bai gama yanke hukunci gaba daya ba don ta burge shi kasancewar sanye take da dogon hijabi tun daga kanta har idon sawun kafarta, ya na yi mata kyakykywan zaton ba rashin tarbiyya ba ne firgicine kawai ya sa ta zage shi. Ya bi ta da kallo ya na mamakin irin sauri da ta ke yi. Tana tafe tana ta waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya har. Ya ji a jikinsa in bai bi bayan yarinyar nan ya bincike ta ba bai yiwa kansa adalci ba. Ya juya kan motarsa da sauri ya fara bin ta a hankali. Wani lungu ta shige, tun kafin ta shiga ya hango ta yaye burgujejen hijabin nan da yake burge shi ta cusa a leda, sai ga mace cikin matsatstsun kaya ta bayyana. Babu jimawa ta fito sanye da riga da wando da wata 'yar jaka da takalmi mai tsini, wani dan yalolon gyale ne ta yafa akanta ana hango gashin kanta gara ma ace babu gyalen.
Ya ji gabansa ya yanke ya fadi daga nan ya fara jin sanyin zagin da ta yi masa tunda ya tabbatar ba mutuniyar kirki ba ce, za ta yi abin da ya fi haka ma. Ya yi sauri ya d'aga gilasan motar dan kada ta gane shi. Tagumi ya yi kawai yana kallonta nan da nan ya fita daga cikin hayyacinsa ganin halin da yarinyar nan ta shiga, yayi matukar tayar masa da hankali.
Yarinyar ta dubi motar Bakura duba sosai don ta gani ko akwai mutum a ciki ya na kallonta ko kuwa parking kawai a kayi ba kowa. Amma ta kasa gane inuwar mutum kasancewar ba farin gilashi ba ne ya na da dan duhu, na ciki na ganin na waje na waje baya ganin na ciki .
Sai hankalinta ya kwanta ta wuce ta na rangwada ta nufi wajen wata farar mota kirar AUDI A4 4dr dake can gefe guda a ajiye.
Babu alama mutum a ciki kasancewar gilashin motar bakikirin ne.Ta tsaya a jikin motar a daidai wundon direba ta na kwankwasawa, fiye da mintuna biyar ba'a bude ba, sai daga baya aka bude kofar motar. Sai ga wani dogon saurayi wankan tarwada mai dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, ya bayyana, ya fito ya tsaya a gabnta.
Hakika saurayin ya hadu yana da kyau wanda duk wata mace za ta so shi a matsayin saurayinta, sai dai kyawun d'an miciji ne idan ka zauna da shi za ka san bashi da tarbiyya gara ma ka zauna da kumurcin miciji akan ka zauna da mai irin halayensa.
Sanye yake da bakin wando jeans da farar riga matsatstsiya 'yar qarama mai dan qaramin hannu, fuskarsa cike da wani kwabcecen gilas baqi qirin.
Takalmin qafarsa kuwa wani danqareran kambas ne tattaura mai launin fari da baqi irin na samarin zamani, wanda idan aka jefe ka da shi ko aka taka ka da shi ka tabbatar gadon asibiti zai yi bakuncinka. Yatsun hannayensa dukka goma zobbuna ne rangada rangada. Askin kansa kuwa kai kace shataletalan titi ne (round about) da rassan titina guda hudu gabas da yamma kudu da arewa, wanda duk ta inda aka bullo za'a hadu a tsakiya.
Bakura ya na zaune a cikin motarsa ta mudubin saman gilashin gaba ya na hango bayansa ya na dubanşu tsaf cike da takaici ya rasa da lilian da ya sa zuciyar ta ke bugawa dan fargaba da b'acin rai.
KAI KA FI CANCANTA 1