Sashe 19
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** **** **** Da daddare misalin qarfe goma, bayan Zahra ta yi sallama da mahaifanta t shiga kwanciyar barci. Ta cikin falonta ta wuce kai tsaye zuwa dakin da gadonta yake. Shigarta ke da wuya sai ta zarce bandaki don ta watsa ruwa. Ta fito ta wuce kai tsaye durowar da ta jera rigunan bacci kawai kala-kala wanda a kalla sun fi kala hamsin. Riga da wando, riga da siket, doguwar riga ba masu santsi da masu laushi (cotton). Ta zabi wata 'Yar yaloluwar riga iya gwiwa ta saka, ta zo ta shiga bargo. Bayan ta gama addu'o'in kwanciya barci ta shafe jikinta tun daga kanta har kafafunta. Ta lumshe ido yayin da sanyin split A.C da ke kunne a dakin yake bi sanka-sanka yana ratsa hudojin jikinta. Ba ta ankara ba sai ta ji wata muguwar girgiza a qarqashin filonta, a tunaninta garin ne gaba daya yake girgiza. Ta tashi zaune gami da daga filon da sauri ta son ta ga abin da ke ciki ashe wayarta ce ta manta ba ta kashe ba, ashe wayar a ta vibration take. Ta yi wata ajiyar zuciya domin tuni numfashinta ya qauracewa huhunta, saboda tsorata. Ta miqa hannu ta dauki wayar ta duba sunan Hassana Ummi Sulaiman ne ya fito dara-dara. Ta yi mumushi gami da farin cikin jin kira daga kawarta, aminiyarta, makarantarsu ta boko wato PRIME COLLAGE, haka Islamiyyarsu daya Hassan Gwarzo islamiyya dake Sulaimanu Cresent. Ta fada cikin tsokana. Ummi 'yar autar Mama ya kike? Ya gari? Ya aka yi kika kai goma da rabi baki kwanta ba, don na ji hayaniyar Nura, Sulaima da Faruk?" Ummi ta yi dariya ta ce, "albishir na kira in miki. Ashe gobe mid-term break ne babu makaranta har muke damun kanmu da karatun test mun manta, sai yanzu Khadija Rabi'u Gumel ta kira ta tuna min." Zahra ta kama kai ta tsuke fuska ta ce, "Oh God! na manta, amma ban ji dadi ba wallahi na karantu sosai. Don dazu bayan na dawo gida daga makaranta da yake babu Islamiyya, Na kira Abbana a waya ya zo ya kaini Kano State Library mu ka yi ta karatu da shi. Ya sake koya min Physics sosai sai qarfe shida muka dawo gida. Shi ma ya manta gobe ba makaranta yanzu ya gama cewa in zo in kwanta, saboda gobe in tashi da wuri. To bari in bar wayana a kunne idan Mama ta tashe ni da Asuba, in ce mata ta yi kwanciyarta gobe hutu ne. Thank you very much Hassana Ummi kin taimaka da kika tuna min. Ki gaida gaida su Mama dan Allah." Hassana Ummi ta ce "Za su ji insha Allah. Good night partiner." Su ka kashe waya a lokaci guda, Zahra ta mayar da waya qarqashin filo ta kwanta tana tunano hirar da suka yi da kawarta wacce koda yaushe Su na tare a wani 6angaren kuma rashi yin makarantar taimaka mata aka yi da aka fasa yin test din saboda yau ta karantu idanuwanta har ja suka yi saboda barci. Ai ko ba komai ta san za ta bar kwakwalwarta ta huta, kafin ranar jarabawar. Sai ta ji wayarta ta sake daukar qara wannan karon mamaki ne ya rufe Zahra. Sai ta ce a ranta, "Na san Sadiya Idris ce ko Bilkisu Hamisu za su fada min gobe ba makaranta, ba su san Hassana Ummi ta riga su ba." Tana duba wayar, sai ta ga lamba ce ba suna, don haka ba su ba ne, amma zai yiwu su din ne ko wayarsu ba kudi suka yi amfani da ta 'yan gidansu. Kamar yadda a da kafin a hada mata waya take amfani da wayar Mamarta wajen kiransu. Ta danna wayar cikin farin ciki gami da cewa. To Hassana Ummi ta riga ku, na sani gobe mid-term break babu makaranta, don haka babu test." Sai ta ji an yi wani lallausan murmushi an ce, "Hello, dan Allah Zahra ce akan layi?" Gabanta ya yanke ya fadi ragagagasss!!!! Domin muryar namiji ce. Tunanin da ya fado mata shi ne, to tunda ba Babanta ba ne yake kira tabbas Baban daya daga cikin kawayenta ne. Abin da ta dauka wata kawarta ce marar waya ta roqi Babanta ya kira mata qawarta shi ne ta ji muryar namiji. Nan da nan Zahra , ta gyara zama ta duka ta gaishe shi cikin ladabi. Ta cigaba da sauraron abin da zai fada mata. Ya na magana cikin sanyayyar murya, nutsatstsiya. Ko wanene wannan mai maganar hakika ya san darajar bil'adama. Tunanin Zahra sai ya fara banbanta da manufar wannan mai wayar, ma'ana ba ta ji ya ce ma ta ga kawarta ba wance. Bayani kawai yake yi mata akan ya yi matukar farin ciki da jin muryarta. Ta gigice yayin da hankalinta gaba daya ya tashi. Ta tambaya cikin wata hardaddiyar murya mai rawar disko, saboda gigicewa. Ta ce, "Malam ko ka yi kuskure ne ka bugo ba ni Zahrar ka ke nema ba?" Ya yi murmushi mai fitar da sigar muradi ya ce, "Ban yi kuskure ba, ke Zahra nake nema, domin lambarki ko daga barci aka tashe ni zan kawo ta." Saboda tsabar firgicewa sai tasa hannu ta katse wayar jikinta ya dau karkarwa tamkar mai jin sanyi.Matukar mamaki ya rufe ta. Ta ina wannan mutumin ya sami lambarta? Me yasa ya kira ta'? Me yake nema a wajen ta'? Babu amsar wadannan tambayoyi na ta.Tana cikin wannan hali sai kuwa ta ji wayarta na girgiza ta sura da sauri ta duba lambar dazu ce, don haka sai ta ki dauka yayin da kuka ya fara rufto mata, tsoro ya addabi zuciyarta ta rasa abin da yake yi mata dadi. A zaune take akan gado ta yi quri, domin kwanciya ta gagari hakarkarinta. Mutumin nan dai bai hakura ba, kira yake sake yi tsakaninsa da Allah. Ta miqa hannu ta danna kai ka ce kashi ne a jikin wayar yadda take kyamar wayar. Ba tare da ta bari ya yi magana ba ta fada cikin kuka da rawar murya. "Malam waye kai? Me kake nema a wajena?" Ya yi murmushi ya fada cikin lallausar murya ya ce "Zahra cool do down my dear, Za ki ji ko ni waye, kuma da kuma dalilin da yasa na bugo miki." Ya yi ajiyar zuciya mai hade da murmushi ya ce "Na san baki sanni ba, kuma za ki yi mamaki da na kira ki, actullaly my name Is Abdulmajid El-Museh ina kira daga Bampai quaters." Zahra ta maimaita sunan, "Abdulmajid El-Museh ban sanka ba, ban taba jin sunan nan ba." Ya yi dariya, "Allah sarki daman na san ba za ki sanni ba. Sai dai ina fatan ki san ni nan gaba," Zahra ta fada cikin fushi, gami da daga murya, "Me yasa ka kira ni, me kake nema?" Ya sake lanqwasa murya ya ce, "Haba baby me yasa kike tayar da hankalinki, ko ban ganki ba daga ji muryarki na san kina da kyau. Ba'a son mace me kyau ta dinga wahala cool down." Zahra ta ji wani dacin takaici yana qokarin shaqe mata wuya, sai wani hawaye mai dumi ne ya ke zubo mata. Hankalinta gaba daya ya tashi, abin da take ji wai-wai-wai a gari ya iso gare ta. Ya katse mata tunaninta ya ci gaba da cewa, Zahra gaskiya abin da ke tafe da ni alkhairi ne, babu komai a ciki sai tsananin so da qauna. Kin fahimce ni ko? I love u so much Zahra." Yayin da Zahra ta dafe qirji, domin ta ji wani abu daga cikin kirjinta ya na zillo zai fado qasa, don a fargaba. Ba tare da ta iya cewa komai ba, ta katse wayar. Daga nan ta tabbata lallai wannan bawan Allah ya dauko hanyar da zai rugurguza Zaman lafiya a gidan nan. Ba ita kadai ba har mahaifiyarta kashinta ya bushe daga lokacin da mahaifinta ya san abin da yake faruwa. Kuma nan da nan Bakura Zai Iya ganewa saboda duk sanda za ta tafi makaranta ya kan karbi wayar ya riqe har sai ta dawo sannan zai ba ta. Haka kuma duk bayan wata yana karbar wayarta data mahaifiyarta ya fita da ita ya sako musu credit. Ya na yawan bincike wayar har wani lokaci ya yi game. Bakura yana yawan ja mata kunne cewar ta kiyaye kada ta sake ta kira saurayi ko wani ya kirata. Ya hada mata waya don ya dinga tashinta da Asuba ko idan ta fita unguwa a kira aji in ta isa lafiya, sai kuma don ta dinga hira da kawayenta mata. Kuka mai yawa ya karu. Ta fito falonta ta zauna a kan kujera yayin da ta dora kafafunta biyu akan kujera tasa hannayenta biyu ta matse kafafuwanta tana mai karanto, "Inna illlahi wa'inna ilaihir raji'un." Wayarta ce a gefenta ta sake daukar ruri, ma'ana waya na shigowa. Ta juya fuskarta a hankali tana duban wayar, saboda tsabar tashin hankali, lambar Abdul majid ce ke shigowa don haka sai ta qi amsawa. Matukar mamaki ya rufe zuciyarta, ta na tunanowa a duniya a ina ma ta ta6a jin mai su Abdulmajid. Don ita ba ta taba hulda ko a danginta na wajen uwa da ba kacokan babu mai irin wannan suna Abdulmajid, sai kira yake tun karfi. Ya kira ta yi ringing har ta gama Zahra ta qi ta amsa. Sai ta ji massage ya shigo. Cikin rawar hannu ta dauki wayar ta bude sakon, ta ga dai har yanzu Abdul majid ne abin da ya rubuta kuwa shi ne kamar haka: Hi sweety, answer my calls. I will explain pls. Ma'ana ya abar zazzaqar kauna ki amsa wayata žan yi miki bayani." Firgita kan firgicewa yayin da ta kwatanto a zuciyarta ace mahaifinta ne ya bude sakon nan wayar na hannunsa, ya ya za ta yi ai na lahira sai ya fita jin dadi in ji Bahaushe. Abdulmajid ya cigaba da kira, Zahra ta yanke hukunci mafi sauki akanta gara ta dinga amsa wayarsa akan ta qi amsawa idan ya ci gaba da turo mata irin wadannan sakonnin matsala ne. Amma in waya ce a gaban iyayenta ta iya dauka ta ce wrong number ta katse, amma idan a rubuce ne babu mai fitar da ita sai Allah. Zahra tasa hannu