← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 64

Sashe 48

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Usman ma a layi suka zo suka tafa. Zahra ta taso ta dubi mahaifinta a sanyaye ta ce, "Congratulations Abba, ina muku fatan alkhairi." Sai qannenta duka suka hada baki, "Congratulations Abba." Mamaki ya kama Bakura ya tabbatar Zahra tana taya mahaifiyarta kishi ba kuma kishin kadai take taya ta ba, wacce ya auro ita ce damuwarta. Da a ce wata ya auro ba Sajida ba, ya san Zahra za ta bi bayansa ba za ta bi bayan mahaifiyarta ba, saboda Zahra tafi son abun da mahaifinta ke so. Yaran ne suka katse masa tunaninsa suka hada baki, "Good night Abba, Good night Mama." "Good night children. " Samira da maigidanta suka fada cike da fara'a. Yara suka nufi dakunansu ba tare da su na jin dadin zuciyoyinsu ba. Bakura ya matso kusa da Samira ya zauna ya dube ta ya yi murmushi ya fada cikin wata 'yar siririyar murya. Ya ce, "Samira, kin yi kyau, kamar ke ce amaryar, har kin fi amaryar." Hohoho! Idan ka tona zuciyar Samira za ka yi mamakin irin baqin da ta yi, don takaici. Ta bata rai, gami da daga hannu ta dakatar da shi. Ta ce, "Ba na so, kar ma ka fara wannan zancen. Ni a suwa? Ka tashi mu je in rakaka dakin wacce yau za ta ji dadin kalamanka, amma ba ni ba." Ta mike tsaye zumbur ta rike kugu tana girgiza kamar mai shirin dambe, sai huci take tamkar kasa. Ba musu Bakura ya mike bakinsa cike da magana, haka dariya take son kufce masa, amma yana tsoron furtawa. Su na isa kofar dakin Sajida sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi. Samira ta daga hannu za ta murda kofar ta bude, sai Bakura ya rike hannunta. Ya ce, "Kar ki bude, mu je dakina ki taya ni kwana, ni ba sai na ganta ba." Haushinsa ya sake rufe zuciyarta, ta fusge hannunta ta murda kofa ta tura kai cikin dakin, gamị da kwada sallama. Sun yi dayday a falo su duka kowacce ta lumtsuma cikin kujera mai laushi, sai lumshe ido suke yi. Ga A.C na ratsa sassan jikinsu, ga talabijin su na kallo. Lokaci guda suka dago da idanuwansu suna kallon Samira, ta waiwaya bayanta ta tsuke fuska ta ce da Bakura. "Shigo mana." Ya shigo cikin falon, yayin da idanuwansa suka dira akan Sajida kiri-kiri yana kallonta, kasancewar haske tar gashi ba ta bunjima hijabin nan na ta ba. Ba mayafi, ba dankwali tana zaune ta harde kafa tana saqe-saqen tuggu a zuciyarta. Kan ka ce kwabo Sajida ta murtuke fuska ta fara harbo masa kibiyoyin harara. "Wai wannan yarinyar wacce irin kama su ka yi da Zuhurriyya haka kamar an tsaga kara ?" Bakura ya fada a zuciyarsa. Ya yi karfin hali ya durkusa ya gaishe da tsohowar nan, yayin da su iyayye ma suka gaishe shi, ya amsa cike da fara'a, gami da cewa. "Me ku ke bukata a kawo muku?" Su duka suka hada baki, "Babu komai." Samira ta yatsune fuska ta ce, "To amarya ga angonki na kawo miki, babu abinda zan ce sai addu'a, Allah ya bada zaman lafiya, ya kawo kazantar daki. Sai ku dunguma ki bishi dakinsa ni dai na tafi sai da safe." Samira ta juya za ta fita Bakura ya yi zuruf ya bi ta a baya, suka fice. Sajida ta ja wani dogon tsaki ta murguda baki ta ce, "Wa ya ga amarya, amma kuwa kin yi batan kai da ki ka shigo min da wannan mutumin dakina." Caraf Iyayye ta yi sauri ta toshewa Sajida baki, don kada su Samira su juyo ta. Nan fa suka hau rokar Sajida akan ta tashi ta shirya ta je dakin ango. Saboda takaici ko kallonsu ba ta yi ba ta tashi ta shige uwar daki ta kwanta kan gado ko kayan jikinta ba ta cire ba. A kofar dakin Samira suka tsaya suka dauki lokaci mai tsawo su na tataburza har da kokaye-kokaye. Bakura zai shiga dakinta, ita kuma ta ce ba zai shigar mata daki ba sai dai ya tafi dakinsa don ta san in anjima amaryarsa za ta je ta same shi. Kalmar da ta fito daga bakin Bakura ita ta bawa Samira mamaki da ya ce "Ko Kur'ani ki ka ba ni zan dafa cewar Sajida ba za ta zo inda nake ba, saboda ba ta sona." Wani kallo na takaici, gami da karka raina min hankali mana, haka Samira ta kalle shi ta tabe baki. Ta ce, "Ai kai kana sonta, tunda ka auro ta sai ku je can ku karata." Ta yi wuf ta shige dakinta ta datse ta bar shi anan a tsaye. Ya yi shiru yana tunani, ya kalli kofar dakin Sajida, ya juya ya dubi dakin Samira sai ya girgiza kai ya yi murmushi, ya juya ya nufi dakinsa. Yana shiga dakinsa ya tura qofa ya rufe yasa hannu a aljihunsa ya zaro wasu hotuna guda biyu ya ajiye a tsakiyar gadonsa. Hotunan Sajida ne, wanda aka dauke ta a tsakar gidansu dazu da yamma a wajen yinin bikinta. Daya kafin ta yi wanka aka dauka, dayan kuma bayan ta yi wanka ta caba ado daidai lokacin da ta yi wannan murmushin nata aka dauka. Wato mai daukar hoton har ya wanko ya kawo masa shi ne ya bar sauran a mota ya zabo guda biyun nan wanda take ita kadai don ya tantance abinda ya ke so ya tantance. Ya shiga bandaki, ya dade yana kwara ruwa a jikinsa, saboda duk jikinsa danko yake yi masa. Yana fitowa daure da tawul, sai ya zura doguwar riga 'yar yaloluwa marar nauyi. Ya taka gado ya kinkimo wata 'yar akwati akan wadurof ya zo ya zauna akan gado, ya baje wasu hotuna a tsakiyar gadonsa. Ma'ana hotunan Zuhuriyyarsa ne ya hada da hotunan Sajidarsa, don ya ga ta inda suka bambanta. Ai kuwa sak kamarsu daya, kirar jikin ma daya, ga dariya da murmushinsu iri daya. Sai mamakinsa ya sake daduwa. Surutai yake shi kadai cikin dare, kamar tababbe. Hakika Bakura yana cikin wani hali domin akan ya san asalin wannan kama ya sa ya auro Sajida, amma har yanzu babu wata shaida da ta nuna masa alaka ko kadan tsakanin Sajida da Zuuriyya. Haka Bakura ya raba dare, sannan ya hakura ya kwanta. Gajiya, gami da dogon daren da ya raba bai yi barci ba basu hana shi tashi da Asuba ya je masallaci ba. Ya na dawowa ya bi dakunan gidan gaba daya yana bugawa har da dakin Sajida. Kowa ya tashi wuri-wuri ya shiga bandaki, don dauro alwala. Bakura kuwa da ya tabbatar kowa ya tashi sai ya shiga nasa dakin ya kwanta, saboda barcin da ya addabi idanuwansa ya sake kwanciya. Samira kuwa tana farkawa bayan ta yi sallah, sai ta shiga kicin ita da kukunta suka shiga shiryawa yara 'yan makaranta abinci. Haka abincin mai gidanta da na Sajida da 'yan uwanta daban. Yau Samira ta sake zagewa wajen qara qawata abinci fiye da kullum, saboda tana so ta nunawa su Sajida bakin rijiya ba wajen wasan yara ba ne. Ta na so Bakura ya san ba irinta ake aurowa kishiya ba, saboda babu abin da amaryar za ta fi ta. Bayan komai ya dahu, ta dauko tsala-tsalan food fasks hade da plates da cokula da saving spoons hadaddu wadanda ta suyo su daga Saudiya na sarakai ne, domin an diga ruwan gwal da azurfa a jiki. Burinta ta burge qauyawan nan da suka zo gidanta da sunan amarya da qawayenta. Ta kira masu aikinta guda biyu Hajara da Grace suka dinga diba su na shigarwa dakin Sajida su na jerawa akan Dining table, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar qawayen Sajida. Sai kalmar "Sannu, mun gode." Suke fadi, daidai lokacin Sajida ta fito falo das da ita, ta yi wanka ta caba ado da wata atamfarta Super Holand kalar kore da ruwan dorawa (Green and ycllow) wacce ta sha dinkin riga da zani daidai jikinta. Ta kuwa nada dauri cas da ita kai ka ce ango ta yi wa wannan ado. Sai kamshi ne ke biye da ita a sanadiyar feshe jikinta da ta yi da turare (Designers). Hakika yunwa ce taf a cike a cikin Sajida, kasancewar jiya ba ta ci abincin kirki ba. Dan yunwar dare ma ta so ta hana ta barci, bakin ciki ne ya hana ta tashi neman abinci cikin dare. Don haka ta yi farin cikin ganin wadannan galla-gallan warmers. Kai tsaye Sajida ta haye kan tebur ta kalli kawayenta. Ta ce, "Mai ci ta zo don ni ci zan yi, wanda ya ga bati ya kyale jahili ne. Wahalallun har sun gama abinci da sassafen nan, sai dai su dafa su ba ni dan ni babu wanda zan dafawa abinci a gidan nan, saboda ajiya aka kawo ni in ci in yi gaba." Suka taso kowacce ta sami tata kujerar ta zauna. Zainab ta dubi Sajida ta yi dariya.Ta ce "Sajida ba ki da mutunci." Tsohuwa ta ce, "Ba zan hau tebur ba kar in fado saboda dadi ku zubo min nawa a kasa zan ci." Tun kafin su Sajida su kai loma daya bakinsu suka fara santin kyawun cokulan da plates din nan. Ai da suka fara ci, sai suka ji cikin kunnuwansu ya dau kaikayi, saboda dadi. Tunda suke ba su taba cin abinci mai dadin irin wannan abincin ba. Wasu abubuwan cusawa suke ba tare da sun san sunansa ba. Kamar bangaren fruits irin su straw berry, inibi, duk sai dai su ganshi a talabijin ko a hoto ko kuwa su ga fukawar su. Misalin karfe goma sha daya, Bakura ya farka daga barcin da yake yi, ya yi wanka ya fito a shirye tsaf sanye da wata shadda shudiya (blue), wacce aka yi masa gajeren dinki iya gwiwa, wato (boda), ya dora shudiyar hula. Kamar wadanda suka hada baki Samira ya iske a falo ta ca6a ado da wani shudin leshi, sai walkiya take. Bayan ta gaishe shi sai ya shiga janta da wasa yana zolayarta, duk da ya san haushi yake bata shi kuwa dadin zolayar yake ji. Suka wuce kan tebur don karya kumallo, domin Samira ba ta iya cin abinci ita kadai, duk dadewar da Bakura zai yi
Chapter 48 · 0% Book details