Sashe 11
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Malam Yakubu ya gallawa Yahuza harara ya fada cikin tsawa "tashi ka shiga gida. Waye ya ce ka zo ka zauna anan?"
Sum-sum Yahuza ya miqe har ya wuce zaure ya fito da sauri
Ya ce "ah Baba na manta Sajida ta ce ka ba ni kudin igiyar leko(mosquito coil) in siyo ma ta."
"Malam Yakubu ya b'ata rai kai ka ce ruwan zafi aka watsa masa.
Ya ce "ba zan siya ba, ai na fada ma ta jiya, igiyar lokon kwana biyu ne, domin guda biyu na ba ta amma ta qi ji ta kunna dukka biyun jiya, daya a wajen kanta wata a wajen qafarta wai ita isasshiya. Igiyar lekon biyu naira goma sau biyu a rana daya sai ka ce buga kudin nake yi. Dama guda shida na siyo jiya na miqawa Sajida biyu, na ce ma ta jiya daya yau daya.
Na miqa ma ka guda biyu, na kai biyu dakinmu mu ka kunna daya, yau zamu kunna daya. Ko kaima dukka biyun ka kunna jiya?"
Yahuza ya zabura. Ya ce "a'a ni saura daya da rabi da asuba na tashi na kashe dan kar ta qare."
Malam yayi murmushin jin dadi. Ya ce "yauwa ka ji yaro mai tattali haka ake so ka ga kai kwana hudu za ka yi kana kunnawa, ita kuwa Sajida yau idan za ta mutu don cizon sauro babu mai ba ta maganin sauro a gidan nan. Ka je ka ce ma ta ba zan siya ba, ai ta kwana biyu na ba ta kuma kar ta sake damuna."
Bakura ya ciro kudi naira dubu zai bawa Yahuza malam ya hana. Ya shiga roqar Malam, ya na yi masa magiya ya taimaka ya bari Yahuza ya siyo shaltos, malam ya fisge kudin daga hannun Bakura ya tura masa a aljihun gaban rigarsa.
Ya ce "Bakura ba za mu yi musu da kai ba ko jayayya tunda na ce ka bari ka bari, Sajida zuma ce sai da wuta ta na da taurin kai da rashin jin magana. Kuma laifin mahaifiyarta ne, ita ta shagwabata ba'a kwabarta, ada muna ganin kamar yarinta ce sai da ta girma na ga tsiwar ta yi yawa sannan na tabbatar tantiriya ce sannan na fara saka mata takunkumi."
Bakura ya yi shiru kawai zuba tagumi."
Malam ya dubi Yahuza ya daka masa tsawa. Ya ce "tsayuwar me kake yi ne har yanzu? Na ce ka je ka fada ma ta ba zan siya ba."
Yahuza ya shiga gida da sauri.
Malam ya ce "shi kuma Yahuza bashi da matsalar rashin jin magana amma fa akwai shi da kwadayi da son kudi kamar wani quda idan ya ga koko haka ya ke wajen kwadayi."
Bakura ya kwashe da dariya ya ce "haka yara suke a ko' ina ma, sai dai fatan Allah Ya shirya mana zuriyarmu baki daya."
Malam ya ce "amin summa amin."
"Bakura bismillah ga abinci fa an fito mana da shi, tun jiya na ce daga yau abincin mutum biyu za'a dinga zubawa ni da kai." Malam ne ya fada.
Bakura ba zai iya cin abincin gidan Malam ba, ga kunyar malam da nauyinsa yana ji.
Malam ya jawo farantin abinci ya bude tuwon dawa ne da miyar kuka ta sha daddawa da wake amma ba nama. Babu shakka Bakura ma'abucin son miyar kuka ne, to amma tambayar ita ce ta yaya aka sarrafa miyar shine bai yarda ba, ma'ana tsaftar mai girkin, da tukunyar miyar da ruwan da aka dafa miyar, da tsaftar dan aiken da ya siyo kayan hada miyar shine babban tashin hankalinsa. Domin Bakura mutum ne mai tsaftar gaske ga yawan tsantsani. Sannan miyar kukar da ake yi masa a gidansa ta sha bamban da irin wannan kasancewar sai an jefa kaji biyu ko uku a cikin ruwan miyar sun dahu luguf, qashin ya sallube sannan atsame qashin sai a kada kukar a kai.
Malam ya sake maimaitawa "Bismillah Bakura ga abinci, kuma kar ka ce min ka qoshi domin anan mu ka yi magriba ka ga kenan ba ka ci abinci a gida ba. Sai dai idan ba za ka iya cin abincin almajirai ba marar kaji da naman talo-talo."
Bakura ya yi dariya ya ce "haba malam miyar almajirai, nima ai almajiri ne sai dai kawai na ci abinci da yamman nan na qoshi."
Malam yayi turus da alama bai ji dadi ba. Ya ce "bari na kira Yahuza ya karbo ma ka balangun naira dari a zuba maka a miyar ko dan ka ga babu nama shiyasa ba za ka ci ba."
Bakura ya zubura ya ce "a'a malam ka bari kawai, ba dan rashin nama ba ne." Gaban Bakura yayi mummunan faduwa saboda har ga Allah ko ba'a bude kwanon abincin ba ya san ba zai iya ci ba.
Ya ci gaba da cewa "wallahi ba rashin nama ba ne.Ni waye da zance dole sai da nama a abinci zan ci, nawa rayuwar duniyar take? Na qoshi ne kawai."
Malam ya yi zugum kamar mai tunani da alama bai ji dadin qin cin abincin da Bakura ya yi ba. Can ya dubi Bakura.
Ya ce "ba zan boye maka ba d'ana, amma ban ji dadin qin cin abincin nan da ka yi ba, ai sai ka saka albarka ko ba za ka ci da yawa ba. Ni da na ke ganin ka zama dan gida, zá ka iya zuwa ka ce min Malam yau abu kaza nake so a dafa min, in saka Sajida ta dafa maka ko menene ma."
Bakura ya tambaya cike da zumudi."Sajida ta iya girki ne?"
Malam ya ce "ai fiye da shekara biyar Sajida ta hutar da mahaifiyarta, girkin dare da rana, safe da yamma ita take yi sai dai idan ta tafi makaranta a lokacin da take zuwa makaranta kafin a cire ta. Ita mahaifiyarta ta na fama da abincin siyarwa yaushe za ta samu damar dafa mana abincin gida. kwalla-kwallar kunu da daro-daron dan wanke take dafawa ta sayar a rana."
Babu abinda Bakura ya tuna da aka ce masa Sajida ce ta dafa sai lokacin da Zuhuriyyarsa take dafa masa tuwo miyar kuka sai yaji kamshin miyar kuka iri daya da na Zuhuriyya. Bai san sanda ya sa hannu suka fara cin tuwon ba, a idonsa ya na tuna yadda Zuhuriyya take kada miyar komai a cikin tsafta don haka bai sake jin kyamar miyar da yake ci ba. Malam ya ji dadin ganin yadda Bakura ya ke loma ba tare da kyama ba. Sai ci suke har sai da su ka kusa cinyewa. Sannan Bakura ya cire hannunsa.
Malam ya cinye tas ya sude kwanon sannan su ka wànke hannu, bayan sun taba 'yar hira Bakura ya ce da Malam zai koma gida sai küma gobe idan Allah ya kaimu.