Sashe 20
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta danna ma'ana wajen amsa waya, ta fada cikin dakakkiyar zuciya, domin tsananin tsoron da take ji ya fita yanzu, fatanta ta kwaci kanta. Ta ce, "What do you want from me?" A wannan karon shi kuma tasa muryar ce take karkarwa. Ya ce, "Zahra ki saurare ni mana ina sonki ne, na yi miki alkawari zan canja miki rayuwarki. I will do anything for you." Ta fada cikin fushi, "Kamar ya ya?" Ya ce, 'Waya mai tsada, in zuba miki kudi a ciki account babu adadi, English wears kala-kala. Ke zan iya siya miki mota saboda ina sonki, ki rabu da sauran samarinki..." Ta daka tsawa ta katse shi ta ce, " enough is enough, ka sanni kuwa? Ka san yaya nake? I'am a small girl, I am just 15yrs ya za ka dinga kirawo min sunan samari? Ya za ka ce za ka siya min mota? Me ye Abbana ba shi da shi da kake so ka nuna min kudi? Abdulmajid please I beg you ka rabu da ni kana so ka jawo min matsala infact ka jawo abin da Abbana zai aikata kisan gilla a kaina ko a kanka. Akwai manyan 'yan mata a gari ka je ka tsara su ka rabu da ni please. Yaushe ka san ni? A ina ka sami number na for God sake, za ka jawo min problem." Sai ta fashe da kuka. Abdul majid ya fada cikin nadama da tausayawa "Oh God baby don't cry. Ni mai sonki ne zan kawo miki farin ciki ba zan jawo miki problem ba. Na sami number a dalilin wata sister ta Sajida." Zahra ta dakata da kukan ta maimaita sunan "Sajida, Sajida, Sajida." Har sau uku a inda kwakwalwarta take kai kawo tana so ta tuna inda ta taba jin mai suna Sajida ta na ta kokarin tuna a duniyar da ta taba haduwa da mai suna Sajida a rayuwarta. Abdul majid ya ci gaba da cewa, "Ba kawarki ba ce Sajida? Ai ta taba kiraną da wannan lambar anan na sami lambarki, ta fada min sunanki Zahra." Zahra ta sake maimaitawa, "Kawata Sajida, a ina nake da qawa Sajida? Ni gidan wacce kawa ake barina in je?" Abdul majid ya ce, "Common baby, ki tuna mana a cikin satin nan Sajida ta kira ni da wannan lambar da yamma. Baki tuno Sajida Yakub Kawo ba?" Sai a lokacin computer kwakwalwarta ta fito mata da Sajida muraran ta gane wacce yake nufi, sai ta ji wani sanyi a ranta, ta fada cike da murna. "Okay na gane Sajida a Kawo ka kira ne a bata waya, ai bama tare. Ko ba SajiAbdulmajid ba budurwarka. Ai Sajida aminiyata ce duk sanda mu ka hadu zan kira ka in ba ta waya saboda haka ba sai ka qara kira ba." Abdulmajid ya yi dariya ya ce, "Kina da wayo da yawa Zahra. Tunda kin fahimci Sajida budurwata ce, no need in boye miki harma kin riqe sunan da ta hada Sajimajid. Abdulmajid so yake yanzu in zama na an hada mana SAJI-ZAH-MAJID ma'ana Zahran Abdulmajid." Zahra ta tsuke fuska yayin da wani mummunan sabon tashin hankali ya far mata. Ta mike tsaye a fusace. Ta ce "Kai ba zai yiwu ba, ba zan iya ba, ba zai yuwuwa ba. Gara ka rabu da ni tunda wuri kafin mahaifina ya sani. Kar ka kara kirana. Ka zama mai bata tarbiyyar da iyaye suka yi wa ya'yansu. Mace kwarya ce me kyau wacce iyayenta suka adana ta suka saqale ta a ragaya, don karta fito tsakar gida a yi amfani da ita ta yi datti. Amma kai ka zuga kwaryar an mai kyau take ballowa daga ragaya take fita titi tana tunbele kana garari da ita, har sai da ta baci, sannan ta zagayo ta haye ragaya kamar ba ta yi datti ba a tunanin Iyayenta, kwaryar nan ta su tana nan da kyawunta," Ta ci gaba da cewa "Abdulmajid, Abbana ya ce ni kwaryarsa ce mai kyau, ya saqale ni a ragaya don kada in yi datti ya ce min yana fatan wannan kwaryar tasa ba ta fakon idonsa tana ballowa tana fita ta yi yawan garari ta yi baki ta zo ta d'ane a ragaya, kamar wata kwarya ta gari kamar yadda Sajida ke yi." Zahra ta na gama fada sai ta murtsike wayar gaba daya ta kashe. Yayin da take murza idanuwanta ta ji ko mafarki take a cikin barci. Ta ga daram ba mafarki ba ne, ido biyu ne. Babu abin da take hangowa a cikin idanuwanta sai lokacin da suke tafe da mahaifinta a mota bayan sun taho daga gidan su Sajida sanda ta yi masa zancen Sajida ta na lekawa katanga ta ari waya su yi magana da saurayi. Hankaiinsa ya yi matukar tashi kamar zai jawo ya dake ta ita mai ba shi labarin. Ina ga idan ya ji ita ce take zance da saurayi a waya? Jikinta na karkarwa ta koma kan doguwar kujera ta takure yayin da wannan dare ya zame mata shine daren farkon da ta taba haduwa da irin wannan gagarumin tashin hankali a rayuwarta ta duniya, tun da Allah ya halicce ta. Dan haka yau ne dare na farko da barci ya kauacewa fatar idonta. Yadda ta ga rana, haka ta ga dare tana zaune tana tunani. Ba tare da tasan Asubah ta yi ba, Abbanta ya gwada kiran wayarta ya ji a kashe, don haka sai ya zo da kansa har kofar dakinta yana bugawa. Saboda tsabar ba'a cikin hayyacinta take ba, haka ta zurawa kofar ido tana kallo ta manta idan ka ji ana buga kofa budewa ake a ga ko wanene. Muryar mahaifinta ta ji ya ce "Yagana, bude kofa mana. Wanne irin bacci kike yi haka ne?" Sai ta yi firgigit ta tashi zaune daga kishingiden da take ta amsa cikin rawar murya. "Na'am." Ta yi duru-duru ta fisgo wani 'dogon hijab ta maqala ta bude kofar falon da sauri. Nan, aka hau kallon-kallo tsakanin Zahra da mahaifinta. Shi ya na kallonta saboda yadda yaga tana kallonsa galala tana zare ido kamar wata sabuwar tababbiya da alama idanuwanta su na tattare da barci mai yawa don sun yi luhu-luhu. Ita kuma tana ganin mahaifinta sai tsoro ya kamata don ta kwatanto irin tashin hankalin da za a yi duk lokacin da ya kama ta Abdulmajid ya bugo mata waya ko ya turo mata sako ta waya. Bakura ya fada cike da mamaki, "Mamana, lafiyarki kalau kuwa? Kin yi bacci yau ko karatun test din kike yi tun dare?" Zahra ta ji dan sanyi a ranta da ta ji ya fadi haka, ta amsa da sauri. "Eh karatu na kwana ina yi." Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci, sai ya girgiza kai. Ya ce "Ba kya jin magana, maimakon ki yi bacci yau ki tashi a nutse meye amfanin kin kwanciya ba ki yi barci ba, ki shiga dakin jarabawa kina gyangyadi? Ki shiga ki shirya ki je makaranta da wuri." Tana rawar jiki ta rufe kofar falonta, ta shiga ciki da gudu ta lalubo wayarta a karkashin filon kujera, hannunta na karkarwa ta kunna wayar cikin 'yan dakikai sai ga waya radau ta kunnu, yayin da kunnuwanta suke jiyo mata wani sauti daamm, daamm sakon text message yana shigowa, har guda uku.Wannan karon ma firgita ta sake yi tun kafin ta bude ta ga me aka rubuta babu tantama ta ji a jikinta Abdulmajid ne mai wannan danyen aikin. Ta bude sakon farko, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsantsar kaunar da yake yi mata. Sai ta ji kwallar takaici. Ta bude sako na biyu, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsananin begen da yake yi mata. Sai ta ji hawayen qunar rai. Ta bude sako na uku, sako ne daga Abdulmajid ya na bayyana mata tsagwaron halin da ya shiga a sanadiyar kin ba shi hadin kan data yi, ya baza hajarsa bai siyar ba ma'ana bata karbi soyayyarsa ba. Sai ta ji wuyanta ya hau makakin tashin hankali. Wannan ne karo na farko da Zahra ta ji ta fara tsanar rayuwarta. Bugun da ta ji ana yiwa kofar falonta ne ya zaburar da ita, ta cillar da wayar gefe ta mike tsaye tana muzurai, sai ta ji muryar mahaifinta yana kwalla kiran sunanta. Ta na karkarwa ta je ta bude sai ga mahaifinta da kaninta Abubakar a tsaye carko-carko sai zare ido take, ta kalli wannan ta juya ta kalli wancan. Bakura ya ce "Da gaske ne yau babu makaranta kun fara mid-term break?" Zahra ta fara gwagwarmaya da makoshinta. "Eh, eh, ashe haka ne na manta." Bakura ya tsuke fuska ya ce "Me yasa kika kashe wayarki? Na san kawayenki su Khadija Rabi'u za su kira su fada miki tunda ke kin manta. Ki na 'yar yarinyarki qarama kina matuwa, kamar wata tsohuwa? Ki je ki dauko wayar ki kunna ki kawo min in yi magana da principal. Ya za a yi a ce ana hutun mid-term ba'a ba ku a rubuce ba." Zahra ta na karkarwar jiki ta koma cikin falonta da sauri yayin da fargaba da tashin hankali suka qaru akan na da. Abubakar ya dubi mahaifinsa ya ce "Abba an bamu takarda a rubuce a cikin mota muka bar su, bari in je in duba." Ya nufi wajen mota kafin Bakura ya bude baki Zahra ta fito cikin muzurai da rawar jiki ta mikawa mahaifinta waya. Ya karba ya juya ya nufi dakinsa da wayar. Juyawarsa ke da wuya sai wavar ta yi qara alamar sako aka turo (Test massage). Bakura ya yi sauri ya tsaya Cak ya duba wayar bai yi wata-wata ba sai ya bude sakon ya karanta ya juyo da sauri ya dubi Zahra. Tuni numfashin Zahra ya fara tafiya kamar mai shirin tafiya barzahu. Ya dube ta, ta dube shi, sai taga ya gyada kai ya juya ya tafi. Ta sulale ta tsugunna don tsananin tashin hankali, ta san tabbas Abdulmajid ne, sakonnin kuma soyayya duk da ta goge wadancan na jiya kafin ta mika masa wayar. Ta irin matakin da mahaifinta zai dauka akanta, yanzu ta sake tsanar kanta, takaicin da dana sanin dama bata nace ta ce mahaifinta ya kai ta ta ga Sajida mai kama