Sashe 10
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
*** **** ***
Washegari asabar da yamma Bakura da Samira matarsa ne su ke zaune a kan dogowar kujerar babban, falonsu su na kallon wani dadadden bidiyo casset na da can wato wakokin Dan anace wanda ya yiwa Shago.
Yara gaba daya su na makarantar islamaiyya. Domin idan ka ga Bakura ya zauna ya na kallo to ka tabbatar wakokin shata, dan kwairo, Dan anace, Dan maraya, Haruna uji, Garba 'Super, Sani Aliyu Dan dawo, Barmana coge, Uwaliya mai amada ne. Ma' ana wakokin 'yan dambe, 'yan farauta, 'yan tauri da dai sauran finafinan al'adunmu na Hausa wanda gargajiya ce tsagwaro babu kwaikwayon turawa a ciki. Da Samira ta san da haka sai ta bazama ta shiga nemowa maigidanta abinda za ta ja hanklinsa, ta Siyo masa su kala-kala. Na, bidiyo, na CD da na radio, ta zuba masa a mota, wasu a dakinsa, wasu a afalonsa Don haka duk lokacin da Bakura ya ke gida ya na zama tare da iyalinsa su yi ta kallo cikin nishadi annashuwa.
Waqoqin su kan tunawa Bakura labarai na can-can shekarun baya sanda ya ke yaro qarami.
Bakura ya dubi Samira duba irin na jin dadin Ya ce "Gimbiya, da ace ni shugaban qasar Nageria ne da na rusa duk wani qyale-qyale da kwaikwayon al'adun turawa, ana ganin shine wayewa alhalin ba wayewa ba ce ci baya ne. Duk wani dan Nigeria mata, yara da manya dole atamfa za su dinga sakawa, kar kice atamfar za su yi dinkin da suke so ko matsatstsan siket da matsatstsiyar riga, a 'a wadatacciyar riga da mayafin atamfa ma'ana falle biyu irin na da, da ake yi riga da zani da mayafi a samo dan kwali daban a daura. Maza kuma yara da manya sai sun saka riga da wando da babbar riga da hula, kowa a qasar nan shigar da zai yi kenan. Saina hana saka mini siket, shirt, jeans, short kneekers, 3 duater, suits da dai sauransu."
Samira ta kwashe da dariya ta ce "haba Sweety, babbar riga fa ka ce? Yanzu ko ma su aikin a bankuna da likitoci babbar riga zasu dinga sawa, ai sai ta hana su aikin."
Ya yi dariya ya ce "to na yarda su cire idan Likitoci za su yi operation, ma su aikin Bakin su cire su ajiye a gefe su na gama kirga kudin sai su mayar da ita."
Ta gyara zama ta ce "yanzu tsakani da Allah yaya za'ayi ka hada Inyamurai da Yarbawa da mayafin atamfa?"
Ya ce "ai har yanzu Matan Inyamurai su na dinkin zannuwa biyu sai dai ba sa yafawa Sai su daura daya akan daya kin ga idan na saka dokar daukar dayan kawai za su yi su yafa a jikinsu."
Su dukka su ka kwashe da dariya.
Samira ta ce in laifin ka ce mata suyi shigar abaya doguwar riga bawa mai dankwali ko hijab. Maze kuma doguwar riga fara da hirami, irin na Saudia ina ganin ai sun dan fi rashin nauyi."
Bakura ya girgiza kai ya ce "na yarda shigar larabawa shiga ce mai kyau itace shigar musulunci, amma al'adar Hausa na ke so in farfado da ita saboda al'adar Hausa al'ada ce mai kyau wacce ke tafiya da Addinin Musulunci."
Samira ta riqe haba ta ce "wai, wa ya ga ka zama shugaban qasar Nigeria 'yan Nigeria sun hadu da doka."
Ya ce lallai kuwa zan takura musu da dokoki kuma kowa sai ya bi. Dole ne ayi da' a, dole ne ayi aiki,dole ne ayi tsafta, babu zalunci. Na qasa dole ne ya yiwa na samansa biyayya, shugaba dole ya biya na qasa hakkinsa da dai sauran matsaloli dake buwayarmu 'yan Nigeria."
Ya sake kishingida kansa akan hannun kujera ya dube ta ya ce "Gimbiya ina cikin wani hali wanda yake rikirkitacce mai daure kai, mai tsoratarwa matuqa."
Ta gyara zama ta ce "me ya faru? Wani abu aka ce maka ya na faruwa a cikin gidan nan, a kaina ko a kan yara ko kuma a cikin masu aiki ne?"
Bakura ya girgiza kai ya ce "ko daya, babu komai game da cikin gidan nan. A can wata unguwa ne da ake kira Kawo."
Samira ta maimaita "kawo? Na san unguwar Kawo me ke faruwa?"
Yayin da ta dafe kirji zuciyarta na bugun uku-uku.
Ya dube ta ya yi murmushi. Ya ce "kwantar da hankalinki ba wata matsala ba ce uwar tsoro."
Su dukka su ka kwashe da dariya.Tabbas kishiya ce ta fara fado mata a ranta.
Ya sosa qeya ya gyara zama. Ya ce "Na ga wata yarinya budurwa matashiya wacce shekarunta ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba."
Tuni hawaye ya cika idanuwan Samira domin ta san qarshen maganar.
Ta fashe da kuka ta dube shi. Ta ce "Abban Zahra, meye hadinka da yarinyar har ka zo ka ke bani labarinta?"
Bakaru ya girgiza saboda har ya ji ransa ya baci, ya dubi agogo ya juya ya dubi teburin da ke gefansa sai ya suri mukullin motarsa ya dora hularsa akai ya miqe tsaye. Ya dubeta duba na takaici Ya ce "babbar matsalata da ke kenan, ba ki da matsala wajen ladabi da biyayyar aure, ba ki da matsala wajen tarairayar miji, ba ki da matsala wajen koyawa yara tarbiyya, ba ki da matsala wajen iya girki da tsaftace gida. Babbar matsalarki itace mummunan tunani da tabarbarewar fahaimta akan kishiya, shi yasa hira ta da ke ba ta dadewa domin daga an fara labari sai ki fara maganganu ki na koke-koke dan haka ni yanzu zan bar miki gidan idan kin gama kukan can bayan sallar isha'i zan dawo."
Ya juya zai fita, ta sake zubo da hawaye.
Ta ce "ashe daman zance ka fara zuwa shiyasa jiya ba ka yi sallar magaruba da isha'i a masallacin qofar gida ba? ka je ka dawo da wata shadda ashe ita ta ba ka. Ai ba a nan kasar ka ke siyan shaddar da ka ke sawa ba."
Tsawa ya daka mata wacce ta razanar da ita ko tari ba ta sake yi ba, ya fara magana cikin fushi. Ya ce "ya ishe ni haka, ba na son ki qara daga wannan maganar, labarin da na ke niyyar baki na fasa kuma kar ki sake tambayata."
Ya juya a fusace ya fice, ya zabi dankareriyar mota wacce ba ta jiya ba ya shiga ya tafi. Bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan malam Yakubu. Kamar jiya yauma anan suka yi Sallar magaruba suka yi karatu sannan su ka yi sallar isha'i sannan kowa ya watse. Sai Malam da Bakura su na ta zuba hira.
Yahuza ne ya fito dauke da farantin abinci ya ajiye a gabansu, languna ne na tuwo da miya, Yahuza ya durqusa ya gaishe da Bakura cike da fara'a da tsananin saka ran yau ma zai sami wata dari biyar din. Ya sami gefe ya zauna ya ci gabaKai ka fi cancanta 1
Na
Jut
0️⃣8️⃣