← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 64

Sashe 61

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba ya ce dai ta bar masa gidansa. Mu ka tafi Cinkilawa da Magaruba, saboda tsoron Innono sai muka qi zuwa gidan muka kwana a gidan wata qawar Zuhuriya mai suna Tabawa. Washe gari muka kama haya a nan Cinkilawa. kan kace kwabo Innono ta ji labari, ta diro mana.Ta yi ta fada ta shaidawa Zuhuriya cewa marmaza-marmaza ta shirya ta koma gidanta, don mijinta ya aiko 'yan uwansa biko, amma kada ta sake komawa gidan da ni. Zuhuriya ta ce ta amince za ta koma, amma sal hutuna ya qare na koma makaranta, sannan zata koma. Innono ta ce ba zai yiwu ba ta yarda in koma gidanta in qarasa hutun ita kuma ta koma. Daga yadda Innono ta ga na yi ta san ban amince ba. Haka ita ma Zuhuriya ta dai amsa mata ne kawai, sannan Innono ta tafi. Ai kuwa bata koma ba har sai da hutuna ya qare ta harhada min komai na koma makaranta, sannan ita ma ta koma gidanta kasancewar mijin kullum sai ya zo bada hakuri. Na koma makaranta ina ta karatu, har shakuwarmu ta sake kulluwa tsakanina da principal da iyalansa. Har sai da sauran daliban makarantar suke tunanin ashe daman mu 'yan uwa ne. A gidan nake yin week end haka komai dare Aunty Asiya take aiko maigadinsu ya kawo min abinci har hostel. Ina jin dadin rayuwar makaranta, amma jikina ya kan yi sanyi, kwalla ta cika min ido idan na tuno halin da na baro Zuhuriyata. Na qagu in gama makaranta in fara aiki a local goverment dinmu in gina mata gidan siminti, in dinga ajiye mata buhun-buhunan abinci, in dinga dinka mata suturu kala-kala, ita ma ta huta wahala. Burina kacokan a kan Zuhuriya duk da ina tuno mahaifana da qannena na Mangono. Aka yi hutu, don haka na koma staff quarters gidan principal, amma da kyar ya bar ni na zauna saboda gudun abinda ya faru wancan hutun. Na sake ba shi labarin abinda ya faru bayan Zuhuriya ta zo ta dauke ni. Ina kuka ina shaida masa cewar ba na so in sake kashe mata aure. Tausayina yasa dole ya kyale ni.Kamar kullum na bawa abokina wasiqa ya kaiwa Zuhuriya, tasa ya karanta mata. Ta ji irin magiyar da na yi mata cewar kada ta damu, kada ta biyo ni makaranta ina nan cikin qoshin lafiya. Kuma idan hutu ya kusa qarewa zan zo in yini sai in dawo makaranta. Abokina ya shaida min cewa yana gama karanta mata sai ta rushe da kuka ta tashi ta shiga dakinta." Bakura ya matse hawaye yayin da tausayinsa ya rufe masu sauraronsu. Da yawa daga cikinsu suma kwalla suke. Ya girgiza kai yayin da ya cije baki ya damqe tsakiyar kirjinsa, saboda zugi da radadin da zuciyar ke yi masa. Ya ci gaba da cewa "Da wayo, da dabara nake ficewa daga gida in shiga cikin garin Wudil ina yi aikin qarfi ina samun kudi mai yawa sai in boye kafin rana ta fadi sai in dawo gida. Idan suka tambaye ni sai in ce ina bakin get wajen masu gadi ina hira, saboda na san Malam Abbas Shagari ba zai bar ni ba, abin kunya ne a wajensa a ce dalibinsa na dako, sara itace, diban ruwa da dai sauransu, musamman ma ni da kowa ya dauka dan uwansa ne. A haka na tara kudi mai yawa ba tare da kowa ya sani ba. Sai da hutu ya rage kwana biyu na shirya na shaidwa Malam Abbas cewa zan je in ga Zuhuriya. Ya dauko kudin motar zuwa da dawowa ya ba ni na tafl na shiga mota na tafi kai tsaye garin 'Yan lanya na nufa wajen Zuhuriya. Hankalina ya tashi da na ga halin da take ciki daga dukkan alamu kishiyoyin nan nata sun hada kai su na wahalar da ita. Ta rame, ta yi baqi da alamar rashin cikakkiyar lafiya a jikinta. Mace ce mai fara'a da hira, ga zaqin murya, amma da kyar kake jiyo abun da take fada idan tana magana. Gashi yanzu ba ta sana'ar komai, jarin ya qare. Sai ta yi matuqar yin farin ciki da mamakin da ganin irin kudin da na tule mata a gabanta. Ta riqe baki don mamaki ta tambaye ni. "Bakura ina ka samo kudi haka?" Na ba ta labarin duk yadda aka yi, sai ta fashe da kuka ta shaida min cewa daman tana rashin kudi ga bashi a kanta dankar. Su suke siyan omo, sabulu, kudin kitso, ga cikon kudin cefane idan ya ba su tsabar gero, dawa ko masara shi kenan ya gama. Su za su surfa su daka har ya zama gari, sannan su nemo abin kada miya. Na sake tausaya mata, sannan kuma na sake kudirar niyyar zagewa in yi aikatau in samo kudi in ba ta idan an yi wani hutun. Ta raba kudin gida biyu ta miqo min rabi ta ce in yi sayayyar makaranta daman ta hada zannuwanta za ta siyar ta aika min kudin. Na ce ta bar shi pricnipal ya gama siya min komai. Ba ta ji dadi ba da na ce yau zan koma ba zan kwana ba. Kuka take, ni ma ina kuka muka rabu. In takaice muku kowanne hutu haka ake yi har na gama aji biyar (Ss2), muka fara rubuta jarrabawar fita don haka na dade banzo ba. Kowa ya yi hutu ban da masu zana jarrabawar fita, sai dai aka yi mana taron iyayen yara. Ranar taron iyayen yara(visiting) ban sa rai ba, ko a mafarki ba na tunanin zan ga iyayena. Don haka ban ma tunkari cikin Hall ba na sami bishiya na zauna ina karatun littafina. Kamar daga sama na ga Jamilu abokina ya nufo ni a guje yana shaida min ga mahaifiyata ta zo min. Na dube shi a shelake na ce "Karya ne." Ya yi min rantsuwa gami da rike hannuna ya ja ni har karkashin bishiyar da Zuhuriya take tsaye.Hakika ita ce a rakabe a jikin bishiya da kwanon abinci akanta. Yayin da manja ya yi kaca-kaca da kayan jikinta, musamman farin mayafinta, da alamar gajiya da wahala a tattare da ita. Na qaraso da sauri cike da gigita na sauke kwanon da ke kanta na zaunar da ita qasa ta miqe qafafuwanta da suka kukkumbura suntum, kasancewar tsohon cikin dana gani a jikinta. Idanuwanta a kumbure, leben bakinta a suntume ga bushewa kayau-kayau saboda yunwa da kishirwa, kamanninta ya canja kamar ba ita ba. Na rasa abun da yake yi min dadi na ruga da gudu gidan Malam Abbas Shagari na karbo ruwan sanyi a firji na kawo mata ta sha, na bude kwanon na ga wata cakudaddīyar shinkafa da miya ce wacce ta sha wuya. Na tura kwanon gabanta na ce ta ci. Ta girgiza kai ta ce "Kai na kawowa Bakura ka ci." Ta shaida min cewar Babar Jamilu ce ta shaida mata za a yi wa yara taron ziyara za su jewa Jamilu idan zan zo wajenka in shirya. Tunda Asuba suka fara soye-soyen kaji, cincin, naman rago da dai sauransu." Zuhuriya ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa "Ba ni da kudi, bare in sayi kaji, ba ni da kudin da zan yi cincin, na aika ko'ina a samo min bashi ba a samo ba. Da kyar na ranto shinkafa gwangwani biyu da kaza daya na dafa maka. Kudin motata bai cika ba na qaraso da qafa." Bakura ya fashe da kuka ya ci gaba da cewa "Na sa hannu a kwanan abincin ina ci ba don ina so na ci ba sai don ta yarda ta ci itama. Sannan tasa hannu muka ci shinkafar nan a karkashin bishiya, cusawa nake yayin da zuciya ke cike da tausayinta kwalla ce ke cikowa daga idanuwana ina damben mayar da ita don kada Zuhuriya ta gane. Na dube ta na ce Zuhuriya ciki gare ki ne na ga cikinki babba kafarki a kunbure? Ta langwabar da kai tasa gefen gyalenta ta share hawaye ta ce shi yasa ka ji ni shiru, tun sanda na sami cikin ba ni da lafiya. Ban taba lafiya ba tunda na sami cikin nan ga mugayen mafarkai Allah dai yasa in haifi cikin nan lafiya." Na goge mata hawaye yayin da na fara farin ciki ina murmushi na ce da ita za ki haihu lafiya da izinin Ubangiji, amma na fi son ki haifi mace in dinga siya mata ribon." Ta yi dariya ta ce "namiji dai ka sami abokin shawara ko bana raye idan na haifi mace kuwa mata na haifa maka." Na tambaya cike da mamaki na ce "mata kin manta ni yayanta ne wa yana auren qanwarsa ne?" Ta yi dariya ta dafa kafadata ta ce "idan ba su sha nono daya ba zai iya aurenta tunda ba uwarsu daya ba." Na girgiza kai na ce na fi son ki haifi mace in dinga yi mata wasa ina goya ta a bayan keke." Zuhuriya ta saki jikinta muka dinga hira cikin farin ciki har rana ta fadi, sannan na tuna ashe ba ta da kudin mota, kuma ba za ta taba fada min cewar bata da kudi ba tafiya zata yi tayi da qafa har ta isa garinmu, don haka na shiga zulumi ina tunanin yadda zan samo mata kudin mota ko rance ne. Don haka na shiga hostel wajen abokaina da kyar na samo rance na kawo mata, ta qi karba da farko sai da ta ga raina ya 6aci sannan ta karba. Na rakata har get tana daga min hannu, ina daga mata hannu, ashe mun yi sallamar qarshe kenan har abada." Bakura ya rushe da kuka mai tsanani, yayin da Innono ta dau kuka mai ruri har da dora hannu aka. Gaba daya suka dafe kirji suka tambaya "mutuwa ta yi a hanya?" Bakura ya girgiza kai ya ce "ta isa gida lafiya. Bayan zuwanta da kwana biyu ta haihu." Samira ta tambaya cikin damuwa hade da qaguwa, "Da ta haihu me ya faru?" Bakura ya ce "Allah shi Ya barwa kan Sa sani har yau ban sami wanda ya fada min gaskiyar al'amarin ba." Sai ya sake rushewa da kuka. "Kamar yaya ba ka san gaskiyar abun da ya faru ba?" Malam ne ya tambaya. Bakura ya
Chapter 61 · 0% Book details