← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 64

Sashe 26

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*** *** ***
Washegari da yamma Bakura ya koma daukar karatu gidan Malam, har suka yi hira suka gama babu wanda a cikinsu yayi maganar Sajida. Sai dai sun sha hirarsu har Bakura ya shaidawa Malam cewar sati na sama ba zai sami damar zuwa ba saboda zai je Abuja kuma a qalla zai yi kwanaki goma a can. Malam yayi addu'ar Allah ya kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya ya samo abinda ya je nema.
Bakura ya gyara zama ya ce "Malam ka san ina harkar man fetir, ina da gidajen mai kala-kala a garin nan da super market wato ZUHURIYYA STORE da ZUHURIYYA PETROLIEUM STATION. Shekaru biyu da suka wuce na bude branch a Kaduna, yanzu kuma uwargidana Samira na ginawa babbar plaza a Abuja. A unguwar gwarumpa mai suna ZUHURIYYA PLAZA. To shine zan je ayi bikin budewa."
Malam ya gyada kai ya ce "au kai ne mai gidan man nan zuhuriyya? Yanzu zaka bude a Abuja kuma?
Bakura ya ce "Eh, plaza ce, ma'ana qatan gini ne mai hawa-hawa har hawa hudu kowanne hawa akwai kantina manya-manya guda hamsim ka ga kantina dari biyu da hamsin kenan. Kantina hamsim na kasa duk ni zan zuba kaya amma hawa na daya zuwa na hudu dukka haya zan bayar shine zan je ayi bikin budewa."
Malam ya gyada kai ya ce "wane mutum, ikon Allah. Kantina maka-maka har guda dari biyu da hamsim a waje daya wannan ai itace kasuwar duniya."
Bakura ya bushe da dariya ya ce "haba kasuwar duniya, sai dai kasuwar uguwar dai."
Malam ya ce "wanne irin bikin budewa kuma za'ayi?"
Bakura ya ce "ni da matata da ya'yana da abokaina da matansu da 'ya'yansu ne zamu hadu mu je wani hotel mai tsada mu ci abinci a yanka kek."
Malam yayi dariya ya ce "ka ga turawa 'yan boko. yanzu meye amfanin a yanka kek ayi tafi ayi dogon turanci, ina albarka take? Shawarar da zan baka
Bakura shine kar ka tara jama'a ana wani yanke-yanken kek bai yi tsari ba ace ka hada matarka ta aure da wasu mazan ana cin abinci ga 'yarka baliga a cikin maza, abokanka ba muharramansu ba ne. ka kalli matar wani a kalli matarka wanda yake haramun ne. Me zai hana ka dibi mahaddatan alkur'ani daga masallacinka su bazu cikin shagunan su sassauke kur'anai a ciki da zummar Allah Ya kawo ciniki, da kariya daga sharrin 6arayi da 'yan damfara. Matarka kuwa da 'ya'yanka ba'a hanasu su taya ka murna ba sai suyi tasu liyafar a cikin gida iyakacinsu mata kadai su gaiyaci 'yan'uwa da abokan arziki su zo su ci, su sha, ayi karatun kur'ani. Ka dauko mace tayi musu wa'azi a cikin gida. Haka bai fi ba?"
Bakura ya gyada kai ya ce "gaskiya ne Malam, tabbas na yarda cewa abinda da babba ya hango daga zaune yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Sai dai ina neman wata alfarma a wajenka Malam. Babu wanda ya fi cancanta ya je. ayi saukar nan sai kai da almajiranka."
Malam ya girgiza kai ya ce "a'a tunda ka na da naka malaman da almajiran ai su suka fi cancanta su je ba ni ba. Ni fa ban taba zuwa Abuja ba, idan aka ce za'a kashe ni akan sai na nuna hanyar Abuja to sai dai a kashe ni ban san inda take ba. Ga tsufa ina zan iya jure zaman mota daga Kano zuwa Abuja?"
Bakura ya ce "zaman mota ba matsala ba ne daman da jirgi zamu tafi. Zancen cancanta kuwa KAI KA FI CANCANTA ka yi min saukar kur'ani saboda bajintar da ke tsakanin mu. Zan iya samun daci da quna a cikin zuciyata idan ka bijirewa bukata."
Malam yayi shiru ya na dan murmushin jin dadi ya nisa sannan ya ce "Bakura babu wata buqata da zaka nema in qi yi maka ita.Ba damuwa zan baka yardaddun almajiraina dana yarda da qwazonsu su je suyi maka sauka ko ta kwana nawa ce sai dai ina so in ja hakalinka karka biya su kudin aikin da suka yi maka, Baya da ci da sha ba na buqatar ka basu wasu kudi na daban domin tsakanina da kai babu wannan."
Bakura yayi murmushi ya ce "Malam har yanzu baka yi min abinda nake so ba, zan so tafiyar
nan a tafi da kai don kasa min albarka da bakinka."
Malam yayi dariya ya ce "to shikenan Bakura ba zan qi zuwa ba tunda zuwan zai qara maka farin ciki."
Bakura ya ji dadi sosai ya tsayar da ranar tafiya, nan da kwanaki uku su shirya zai sa a zo a dauke su zuwa filin jirgin sama zasu acan Abujar zasu same shi don shi washegari zai tafi.
Kamar yadda Malam ya bashi shawara haka Bakura ya umarci iyalansa su aiwatar, wato su hada walimarsu a gida mata kadai ba sai sun bi shi Abuja ba.
Ya bawa Samira da yaransa izinin su je Zuhuriyya super market dinsa su dibi duk abinda suke buqata komai yawansa, komin tsadarsa daga naira daya zuwa naira million daya ya yarda su kashe. Su gayyaci kowa da kowa daga kan masu kudi zuwa talakawa a dangi da makwabta. Ya umarce su da su ware abinci tukunya daban wacce za'a tara almajirai a qofar gida a rabar sadaka saboda Allah. Sannan Bakura ya tafi Abuja, bayan tafiyarsa da kwana biyu yayi waya Kano ya ce direbansa ya kwaso Malam yakubu da almajiransa guda goma zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu
Kano suka hau jirgi zuwa birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda aka yi a kano a Abuja ma Bakura yana da gida da direbobinsa don haka tun kafin su Malam su sauka daga jirgi direbansa ya zo yana jiransu.
Su na sauka daga jirgi ya kwaso su ya kawo su gida. Bayan sun gama hutawa a kwana daya washegari suka kama karatu a cikin plaza, suka yi ta saukewa qur'ani su na maimaitawa.
Chapter 26 · 0% Book details