Sashe 52
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya fusata ya ce "To ki je police station ki yi qarana da kan ki kafin ya warke ya sa a nemo mu, don na fada masa ko mu su waye, kuma na haska masa fuskata tangararai ya ganni, kuma zai shaida ni. Tunda kina sonsa kada ki qara kirana a waya." Ya yi tsaki ya kashe wayar, Sajida ta dade zaune tana ta tunani tana zullumin abinda zai je ya dawo. Hakika har cikin ranta ba ta ji dadin abinda Abdulmajid da abokansa suka aikatawa Bakura ba. Don haka babu irin kiran da Abdul majid bai yi mata ba a cikin daren nan Sajida ta qi amşa wayarsa, daga qarshe ma ta kashe wayar gaba dạya ta yi kwanciyarta. Tana jiyo motsin dawowar su Samira har da Bakura, amma ko leqowa qofar dakinta ba ta yi ba, balle ta yi masa sannu. Haka washe gari Bakura ko falo bai fito ba, yana dakinsa a kwance ya hana Samira ta fadawa kowa cewar bashi da lafiya, don haka masu aiki ma ba dukkansu ba ne suka san Bakura na kwance ba lafiya ba. Wannan al'amari na Sajida ya yi matukar batawa Samira da 'ya'yanta rai, sai shige da fice take tsakanin dakinta, falo zuwa kicin tana nuna halin ko in kula bai dame ni ba. Rashin lafiyarsa ku ta dama ba ni ba. A fusace Samira ta zo shiga kicin yayin da a fusace Sajida ta zo fitowa daga kicin suka bangaji juna a bakin qofar kicin, Sajida dauke take da qatan kwalin juice da kofi a hannunta. Samira ta ce, "Mutum ko dabba ne ai ya san mai ba shi abinci, don haka baya samun sukuni idan ya ga kwana biyu bai ga mutumin nan ba. Ma'ana shi mai ciyar da ke, mai tufatar da ke, mai siyo wannan juice din da ki ke yini kina sha, ba shi da lafiya a ce ko Sannu, yaya mai jiki baki iya ba. Duk rashin tarbiyyarki ai kya tausayawa rai, saboda idan mutumin nan ya fadi ya mutu, sai dai fa ki koma gargajiya zancen juice ya kare." Sajida ta yi wurgi da kwalin juice din hannunta, gami da rada kofin tangaran a qasa ya ragargaje. Samira ta ce "Dole ki fasa min kofi, saboda ba ku taba sanin yadda ake siyan kayan gado ba balle kayan kicin." Sajida ta fusata ta cakumi kwalar Samira. Ta ce, "Ke dakata kada ki fada min magapar banza akan wani banzan mijinki. Bakura har mutum ne da zan yi kishi a kansa? Ko an ce miki na zo da niyyar aure har da-zan shigo da kayan daki, shi ya ce ya ji ya gani, shi ya maqale ya nace ya raba ni da wanda nake qauna, ya kawo ni gidansa ba dan ina qaunarsa daidai da kwayar zarra ba." "Sakar min kwalar riga kafin in wanka miki mari." In ji Samira. Zahra ta fito daga dakinta da gudu, don ta jiyo hayaniya, haka qannenta suka fito daga falo a guje, don su ganewa idanuwansu abinda ke faruwa. Cikin fushi Zahra ta zo ta fusge hannun Sajida daga wuyan mahaifiyarta ta daki kirjin Sajida da hannayenta biyu ta shiga tsakanin Samira da Sajida. Ta ce, "Mama koma daki ki zauna ki bar ni da ita, ni ce sa'arta ba ke ba." Mamaki ya hana Sajida magana, har murmushi take na hamdala daman tana neman irin wannan rana da za su gwabzu da Zahra, saboda haushinta da take ji tuntuni. Zahra ta ce, "Sajida yau ne rana ta farko da zan yi fada a rayuwata, yau ce rana ta farko da zan tabbatarwa mahaifiyata ta iya haihuwa ba ta sha wuyar banza ba. Yau ita ce rana ta farko da zan nuna miki ba na tsoronki, shiru-shiru ba tsoro ba ne. Ke ba ajina ba ce, domin halinki irin na 'yan matan da ba su taba zuwa makaranta ba ne sai talla a titi. Ba ki da tarbiyya, ba ki sami tarbiyya ba a matsayinki na 'ya mace. Ba kya jin maganar iyayenki, hakan ne ya jawo miki yin aure da wuri maimakon karatu. Kin amsa sunanki na kwaryar tsakar gida mai gagari, ke ba kwarya ta gari ba ce, wacce aka saqale a ragaya don yin ado da ita ba." Wannan kalamai na Zahra ya yi matukar burge Samira, Zahra ta ba ta mamakin yadda wadannan kalamai suka fito daga bakinta. Yayin da ita kuma Sajida ta qufula, ta fusata, ta sake tabbatarwa wannan kalmar mahaifinta ce, don haka bakinsu daya komai a shirye suka hada mata don su raba ta da Abdul majid . A fusacc Sajida ta kaiwa Zahra mari, Zahra ta riki hannun Sajida, yayin da ita ta kai mata mari har sai Sajida ta ga hasken wuta. Zahra ta ce, "A da kin fasa min kai, kin ji dadi, kar ki sake tunanin za ki iya cin galaba a kaina kuma. Sai dambe ya hautsine tsakanin Zahra da Sajida, Abubakar, da Umar sai suka shiga fadan, qafar Sajida kawai suka kwaso sai ga ta a qasa, yayin da suka hau ciccibarta wai za su fitar da ita daga gidansu. Samira ta ga abin yana kokarin lalacewa sai ta shiga rabiya tana jan 'ya'yanta tana cewa, "Ku sake ta, ku kyale ta haka." Duk wannan abu da ake Bakura na jiyo hayaniya daga dakinsa, tun yana zaune yana kwalla kiran Samira, har ya daure ya sauko daga kan gado yana dingishi ya fito, ga tsananin ciwon da kansa yake yi masa saboda raunin da ke gefen idonsa ya kumbura ya aune. Ya na fitowa ya ji hankalinsa ya tashi, ganin yadda 'ya'yansa ke cali-cali da Sajida a qasa. Ya rafsa ihu, kai ka ce bindiga aka burma masa ya danno da gudu yana kurma salati, har da tuntu6e saura kiris ya fadi qasa. "Me zan gani? Samira me ki ke nufi da za ki sa 'ya'yanki su daki matata? ku sake ta kafin in kakkarya ku." Su ka watse gaba dayansu suka gudu gefe sai huci suke. Ya taho da sauri ya tashi Sajida tsaye yana karkade mata jiki, fadi yake, Yi hakuri Sajida, kwantar da hankalinki zan rama miki." Ta rushe da kuka ta fizge jikinta daga gare shi ta ce, "Wallahi zamana ya qare a gidan nan yau, ko awa daya ba zan qara ba tafiya zan yi. Zahra sai na nuna nıiki ko ni wacece, sai kin gwammace baki dora hannunki a kaina ba." Bakura ya juya ya dubi Samira da 'ya'yanta ya ce "Ki shirya ke da 'ya'yanki ku bar min gidana." Gaba daya suka bude baki don mamaki ko a mafarki ba su zata akwai ranar da Bakura zai iya furta wannan kalma ba komai girman laifin da suka yi masa ba, balle a kan Sajida. Sajida ta yi murmushi ta goge hawaye ta kalle su sama da kasa ta ce "A qara gaba ko, ni dai kun ga shiga ta daki, kada ku yi addu'ar inyi arangamata da ku a kashi na biyu dan haduwata da ku ba zatayi kyau ba." Ta shige dakinta ta datse. Zahra cikin kuka ta ce "Abba, yanzu akan Sajida za ka kore mu? A kan matarka za ka rabu da uwar 'ya'yanka?" Samira ta dakawa Zahra tsawa ta ce, "Ki rufe min baki, don me za ki dinga roqarsa? Ki bar shi ya zauna da Sajida. Kowannenku ya je ya dauko kayansa ku zo mu tafi ba za mu kwana a titi ba, Allah yasa ina da iyaye da gatana." Yara har murna suke suka shiga dakunansu su na hada kaya. Haka Samira ta wuce zuwa dakinta da sauri har karkarwa take tana hado kayanta. Zahra ce ke shar6ar kuka tana tafiya tamkar babu laka a jikinta ta wuce zuwa dakinta, ta fara hada kayanta. Bakura ya dora hannu aka kira yake, "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Ya fice da sauri wajen masu gadi ya ce su daddatse kowacce qofa da mukulli, su ba shi 'yan mukullan, yau ba shiga ba fita duk wanda ya zo kar a bude masa, haka duk wanda zai fita kada a bude masa Ya zuba mukullai a aljihu ya shiga gida. Ya ci karo da su kowannensu yana jan akwatuna riki-riki. Ya dakawa yara tsawa "Ku koma da kayan nan ciki kada in ga qafar wani a waje!" Usman dan auta ya ce "Abba kai fa ka ce mu tafi mu mun fi so mu tafi." Umar ya ce "Tunda Aunty Sajida ta zo gidan ba dadi, gara mu koma Yakasai mu zauna mu bar mata gidan." Abubakar ya ce "Gaskiya Abba mu tafiya za mu yi, tunda ka ce mu tafi." A fusace Bakura ya yo kansu kamar zai dake shi yana fadin, "Ku kwashi kayan nan ku koma da su daki." Jikinsu na rawa suka dinga juyawa da akwatinansu ciki gida. Zahra ba ta ce uffan ba ta ja akwatinta ta nufi dakinta sai sharbar kuka take. Samira ta ci gaba da jan tata akwatin ta nufi kofar fita fadi take, "Idan ka hana 'yaranka tafiya daman ba da su na zo ba. Ni kuwa babu abinda zai sa in qara sakon daya a cikin gidan nan. Na tafi na tafi kenan ba zan dawo ba." Bakura ya rike akwatin gam yana ja tana ja. Samira ta ce "Ka sakar min akwatina tafiya zan yi. Zamana da kai ya qare." Ya durkusa gwiwoyinsa guda biyu a qasa yana mai tsananin nuna nadama da bada hakuri. VYa amsa da bakinsa, "Na yi kuskure da na furta wannan kalma, na yi dana sani dana yanke hukunci cikin fushi. Ki rufa min asiri kada ki fita da kayanki, saboda masu aiki da masu gadi za su ganki. Ko da kin je get ba su da mukullan da za su bude miki get ga mukullan a aljihuna. Samira, ba zan iya rabuwa da ke ba, kin zama ni, na zama ke. Ranar rabuwarmu sai ranar da aka saka min likkafani aka kai ni kabarina aka binne, ko ranar da aka saka miki likkafani aka kai ki kabari aka binne. Babu yadda za a yi daya ya bi daya kabarinsa, saboda Allah bai halatta mana yin hakan ba da ba za mu rabu ba. Ki yafe min, na yi kuskure. " Hawayen Bakura shi ya sa Samira rushewa