Sashe 3
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
0️⃣2️⃣
Gabansa sai faduwa yake yi tamkar, 'yarsa ce ta fad'a hannun tantirin niga irin wannan. Sai dai kaşh sun yi masa nisa ba zai iya jiyo abinda suke cewa ba. Ya yi zuruf ya fito daga cikin motar ya rufe, sai ya yi tamkar sabgar gabansa yake yi kamar bai san abinda suke yi ba, ya na tafiya ya na wayencewa kamar bai san da su ba amma wajensu ya tunkara. Bai yi wahalar qarasawa inda suke ba ya fara jiyo abinda suke fada tar a kunnuwansa. Sai kuwa ya ci sa'a akwai wani qaramin masallaci da famfo a wajen. Ya qarasa wajen famfon ya bude ya dinga kurbar ruwa yana wanke fuskarsa, ya kasa kunnuwansa sai ya ji yana jiyo komai ba tare da sun gane su yake saurara ba. Sunan daya ta ambata shi ne Abdul majid shi kuma ya ambaci sunanta Sajida.
Abdulmajid ya ce da Sajida 'ni ba bawanki ba ne, kuma ba direbanki ba ne da zan yi miki waya fiye da awa daya sai yanzu ki ka fito. Daga an yi magana sai ki ce Baba da Umma ne suka hana ni fitowa. Ai babbar matsalar iyaye 'yan gargajiya kenan komai sai ace addini kuma addinin na su duk kame-kame ne, sun hana yaransu shakatawa a banza. Wallahi ba dan Allah Ya jarrabe ni da sonki ba da tuni na rabu da ke, tun sanda tsohonki ya hana ni zuwa qofar gidanku, har yanzu ina jin zafi da quna irin wulakancin da tsohon nan ya shuka min a gaban mutane har yanzu bai bar zuciyata ba. Ke ana son a wayar dake a kwatar miki 'yancinki amma kin k'i yarda, kin zauna ki na bin dokar 'yan gidanku gidadawa. Wai ku ustazai, malamai kuma almajirai."
Babu abinda Sajida take yi sai karkarwar jiki, babu furucin da yake fita daga bakinta sai " Abdul majid kayi hakuri, dan Allah dan Annabi ka yi hakuri."
Abdul majid ya yi mata wani kallo na wulakanci ya zare bakin glashin dake fuskarsa ya tabe baki.
Ya ce "ki na nufin da wadannan kayan na jikinki za ki bi ni party? Ki na nufin da dogon wando da gyale zan shiga dake wajen hadadden party da hadaddun abokaina? Ke bakauyiya ce har yanzu kin kasa wayewa."
Sajida ta dubi jikinta sama da kasa ta rasa illar dake tattare da ita. Wandon jeans ne hadadde kuma matsatstse shine ma ya siyo mata daga America, haka itama rigar a matse take.
Tunanin da take yi ya katse ya ce "dole in kai ki wani kanti in siya miki kaya, mini skirt za'a saka iya cinya da zurmukeken takalmi mai tsini irin mai zif din nan har gwaiwa da riga shimi iya kirji wacce ba ta rufe cibiya ba, kuma babu ke ba zancen dankwali, kin ci sa'a ma ki na da gashi ba sai an qara miki ba."
Sajida ta zabura ta dubi Abdul Majid cike da fargaba ta ce "riga iya kirji?"
Ya daka mata tsawa ya ce "to meye, ki na nufin ba za ki iya sawa ba ne?"
Tsoransa take, sonsa ta ke don haka ba ta iya yi masa musu.
Ta ce "zan saka mana." Ta dubi agogon dake daure a hannunta daga dukkan alamu ta qagu ta koma gida don kada a nemeta. Wannan karon ma tsawa ya daka mata mai firgitar da wanda ke kusa da su, ba ma wacce aka yiwa ba. Nan da nan jikinta ya hau karkarwa.
Ya ce "duba agogon me kike yi, ko yau ma an baki lokacin da za ki komą gida ne?"
Sajida ta na karkarwa
ta ce "a'a ba duba agogo nake yi ba, yi hakuri."
Ya ce "to zagaya ki shiga mota mu tafi."
Sand'a ta ke kamar wacce kwai ya fashe ma ta a ciki, saboda ba ta son shiga motar amma tsoransa ta ke ta kasa ce masa ba za ta je ba.
Bakura ya dago da sauri zuciyarsa tamkar ta fashe, tashin hankali ya rufto masa lallai kuwa zai shiga wani mummunan hali idan har ya bari yaron nan ya fita da yarinyar nan ya je ya ba'ta mata rayuwa ba tare da sanin iyayenta ba. Tabbas abin zai dad'e bai fita daga cikin zuciyarsa ba zai ga kamar ya ci amanar musulumci da iyayenta da ita kanta.
"Tabbas yaron nan ya na niyyar ruguza tarbiyyar da iyayenta yarinyar nan su ka dade su na gina mata." Ya fada a ransa.
Sai ya ji wani hawaye mai zafi ya surnanu masa, yaransa ne kawai su ka fad'o ma sa a rai, gaba d'aya ya ji ya shiga zargi anya kuwa shima ba ci gaban mai haqar rijiya ya ke yi ba kuwa, kullum haqa ya ke amma ya na qara yin qasa. Anya kuwa ba tufka ya ke yi wani ya na warware masa a waje ba kuwa? Ya tuna hadisin da Manzon Annabi (S.A.W) ya koyar damu ce wa "idan ka ga ana aikata 6arna to ka hana da hannunka, idan ba za ka iya ba to ka gyara da bakinka, idan ba halin haka to ka qi abin a zuciyarka wannan shine mafi raunin imani."
Nan da nan ya ji a ransa zai iya zuwa ya hana da baki tunda bashi da ikon gyarawa da hannu. Ya zabura zai je wajensu kenan don ya ba ta shawara da baki ya ce kada ta bi shi. Sai ya ji Abdul Majid ya ce da ita "da fatan kin fad'a a gida cewar kwanaki biyu za ki yi ko?"
Gabanta ya fadi 'rass' ta dafe kirji ta tambaya cikin firgici "kwana biyu?"
Ya yi mata tsawa ya ce "toh meye abin fargabar, ban isa da ke ba ne? A Abuja Nicon Hotel za'a yi casun kuma sai qarfe d'aya na dare za'a fara dan haka daga nan ma Abuja za mu wuce.
Sajida ta zagayo da sauri in da yake ta tsugunna a gabansa ta fashe da kuka ta ce "Abdul majid ka taimake ni, ka rufa min asiri kada ka yi fushi da ni. Da ka san ta yadda aka yi na fito yanzu ma da sai ka tausaya min. Sai da na yi dubara da magiya Babana ya bari na fito da zummar zan je gidan su Asiya kawata in karbi qur'ani. Mintina talatin ya ba ni kasancewar gidan babu nisa ya na gida ya na jirana. My dear, idan na bi ka Abuja har kwana biyu kashe ni ne kawai ba za' a yi a gidanmu ba, ka rufa min asiri. Ina sonka Abdul Majid fiye da yadda na ke son rayuwata."KAI KA FI CANCANTA 1
JUT
Jamila umar tanko