← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 64

Sashe 18

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*** *** ***
Washe gari da sassafe Sajida ta fito tsakar gida tana mika game da doguwar hamma, ta cije baki ta matsa gabobin hannayenta ta danna doron bayanta, saboda ciwon da suke yi mata a sanadiyyar bugun da ta sha.jiya. Umma Furera kuwa tunda Asuba kiran fari ta hau hidimar dora ruwan koko da wainar geron da take yi da safe ta siyarwa, dan haka tana gindi murhu a tsakar gida.
Malam kuwa tun kafin kiran fari na asuba ya yi alwala ya fice, sai kuma da hantsi zai shigo gida.
Yahuza ne ya shigo cikin gida cike da fara'a da farin ciki. Wata qaramar baqar leda ce a hannunsa. Ya dubi mahaifiyarsa ya juya ya dubi Sajida bai kula da kibiyoyin harare-hararen da suke harbo masa ba.
Yayi dariya ya ce, "Kun san meye a cikin ledar nan kuwa? Soyayyan dankalin turawa ne da kwai, na bi almajirai bara cikin Badawa layout gidan da Abashe yake aiki aka ba mu sadaka. Ashe almajiran nan dadi suke ci. Nima daga yau idan zasu je sai na bi su. Wallahi attajirai nan wayo suke yi mana dadi suke ci. Idan Baba baya nan almajiran nan zan dinga bi bara. Haka jiya shinkafa da kaji muka ci a qofar gida. Muzanbilu ne ya samo mana."
Umma Furera ta daka masa tsawa, ta ce "rufe min baki munafuki, kai za ka yi laifi a rufa maka asiri, amma kai ka kwashi maganar da ba a saka a ciki ba ka je ka yi gulma. Yau sai na fasa maka baki. Bari Malam ya shigo, sai na fada masa ashe har yanzu ka na zuwa
bara."
Sajida ta fisgo ledar dankalin da ke hannunsa ta zazzage a cikin bokitin sharar da ke kusa da ita, tasa tsinke ta daddanna ta cakuda da bolar. Yahuza ya ji tamkar 'ya'yan hanjin cikinsa ta yi wa haka. Don a
halin yanzu ya fi son dankalin nan akan rayuwarsa. Ya kwalla wani ihu kai ka ce ransa ake kokarin fitar masa.
Ihu yake ya na kiran
"Wayyo dankalina, na shiga uku na lalace. Wallahi sai na fadawa Baba."
Sajida ta ce, "Ka fadawa Baba ka tonawa kanka asiri, daman ai ya hana ka zuwa bara."
Sajida ta jawo shi ta durkusar a gabanta, sannan ta kwaye masa riga ta bayansa, sai ga doron bayansa muraran ta dauko takalmin danko ta yi ta lafta masa, ya na ihu ya na tambayar abin da ya yi mata. Kamar yadda lokacin da Malam ya dinga nadarta ba ji ba gani, har sai da ya gaji haka ita ma ta lode shi har Sai da ta gaji da kanta, ta sake shi. Bayan da ta tabbatar bayansa ya dau shaida kamar yadda na ta ya dauka, wannan tabon in ba sa'a ta ci ba har mutuwarta ba zai bace ba kuwa.
Umma Furera na can ta na saka gayan koko fadi take, "Bar shi haka, ai ya daku."
Yahuza ya laftu a qasa ya na narkar kuka gami da gungunin da ba a fahimtar abin da yake cewa ba. Amma idan kunnuwansu ba su yi kuskure ji ba sun jiyo musu yana cewa, "Haka kawai dan cin zali ki yi ta dukana babu abin da na yi miki."
Umma Furera ta fada cikin daga murya ta ce, "Ka san abin da ka yi mana. Idan ba ka san abin da ka yi ba yaya za a yi daga fara dukan Sajida za kä arce waje ba ka sake shigo ba sai yau."
Sajida ta zo ta murde masa kunne ta ce, "To bari in karanto maka abin da muke nufi. An yi walkiya mun ganka munafuki asha kai ne ka ke zagayewa ka ke fadawa Baba maganar Abdul majid. Ka dade ka na hada min tuggu, kasa na bata da mutane da yawa, wadanda kake cewa sune suke fadawa Baba in an ganni da Abdul majid. Musamman na rannan da na fita karbo littafi a gidan su Asiya na hadu da Abdulmajid ina dawowa gida Baba ya shigo ya yi min duka har ka ke ce min wani mutum ne ya zo a mota qofar gida shine ya fadawa Baba har da cewa za ka nuna min mutumin.Ashe babu wani mutum kai ne munafukina. Idan rannan ka ce wani mutum ne ya ganni a waje ya zo ya fada, a cikin gidan nan da nake hawa katanga ina karbar aron waya ina kiran Abdulmajid waye ya shigo ya ganni, shi ma munafukin mai motar ne ya zo ya fada?"
Umma Furera ta ce, "Ke kike biye masa ma, kike maganar wani mai mota, wanne mai mota ne ya zo ya fada? Wanne babban mutum ne mai mota wanda ba shi da ailkin yi har zai zo ya ce ya ganki da Abdulmajid? Yaushe wani mai mota ya sanki har ya san gidanku, har ya san a gidanku an raba ki da Abdulmajid kin ki ji?
'Yan unguwar nan ne kawai suka sanki, suka san Malam ya raba ki da Abdulmajid su ne suka sha kawo gulma, kuma babu wani mai mota a cikinsu. In har da gaske ne ka fadi sunan mai motar mana, ai kai ne idon gari babu wanda baka san shi a cikin unguwar Kawon nan ba, har unguwar Giginyu shiga ka ke ka nemo labari."
Sajida ta ce, "Ga gaskiya ma ta fito abu a cikin gida akan katanga har Malam ya sani na san da Iyayye ba za ta fada ba ta ce ita take ba ni aron waya in yi, idan ta fada ma ta tonawa kanta asiri, don sai Malam ya shiga har gida ya zane ta. Babanta ma idan ya ji sai ya kwace wayar. Waye zai fada in ba kai ba"
Yahuza ya zabura ya miqe tsaye cikin kuka yana cewa, "Wallahi ban taba fadawa Baba ki na aron waya ta katanga ki na yi wa Abdulmajid waya ba. Saboda na san irin dukan da yake yi miki. Ni kuma tunda ku ka ce ni na fada masa, Baban ya zo nan gani, ga shi, ga ku a tambaye shi idan na fada masa wata magana. Yaushe ma muke zama da Baba mu yi hira shi da yake da baqi ko da yaushe kora ta yake ko na zauna a cikinsu."
Yahuza ya fice da sauri ya na kuka sharkab. Sajida da Umma Furera suka bi shi su na kwalla kiran sunansa, amma abu ya ci tura. Tuni Yahuza ya keta zaure, ya wuce dandamalin qofar gida, ya tsallake kwata, ya bi ta kan bola ya tunkarí masallaci. Bai dire a ko'ina ba sai a lungun liman a gaban mahaifinsa. Yahuza. magana take amma ba'a fahimtar abin da yake fada wani tsatstsaman kuka da yake tasowa daga can cikin zuciyarsa a inda jiyiyoyin idanuwansa suke zuqo wani ruwa mai dumin gaske su na fesarwa saboda tafarfasar da zuciyarsa ke yi da tsananin quna da soyuwa.
Malam ya dade ya na tambayarsa haka Yahuza ya dade ya na bada amsa, amma ganewa ta ci tura, saboda hayaqin da bakinsa yake na takaici. Malam ya kamo hannun dansa, abin qaunarsa Yahuza ya nufo gida don jin ba'asi.
Sajida tsaye take a tsakar gida ta na kai kawo cikin zulumi da fargabar abin da zai je ya zo.
Fada take, "Umma, kar fa yaron nan ya je ya hada min tuggu, Baba ya zo ya sake yi min duka irin na jiya."
Ta na rufe bakin sai ta ji sallamar mahaifinta ya danno kai cikin gida riqe da hannun Yahuza. Ta zabura ta daka tsalle sai ga ta a bayan Umma Furera ta buya.
Malam ya fada cikin sanyayyiyar murya, "Tsaya daina gudu, ba dukanki zan yi ba. Don me zan dinga dukanki kamar jaka? Ai bambancin dabba da mutum shine hankali shi ne tunani da jin magana. Me yake faruwa ne Yahuza ya je min da kuka?"
Da Yahuza ya ga sun fara hanya-hanya su na qoqarin baudewa su gyara magana, sai ya yi qoqarin kashe gobarar da take ci a makogaransa, don ya ceto muryarsa ta fito radau dan ta cece shi. Ya rangada bayani tas yadda aka yi tun daga farko har karshe. Kan ka ce kwabo idanuwan Malam sun ciko da hawaye, ya dubi Yahuza duba irin na tausayi. Ya sa hannu ya share masa hawaye.
Ya ce, "Allah sarki, sun dauki alhakinka, sun
zarge ka da laifin da ba ka aikata ba. Sun yi kuskure wajen yanke maka hukunci. Idan ba yafe musu ka yi ba, Allah sai ya kama su da hakkin zalumci. Ka je ka saka kayan makarantarka, ka karbi koko ka sha ka zo in raka ka makaranta, saboda sun sa ka makara."
Yahuza ya nufi dakinsa ya na goge hawaye yayin da zafin da ke qona zuciyarsa ya fara hucewa a sanadiyyar haqurin da mahaifinsa ya ba shi.
Malam ya juya ya dubi Sajida da mahaifiyarta wadanda kowannensu ya yi wuqi-wuqi da ido a lungu su na jiran hukunci a game da ta'addancin da su ka aikata da sanyin safiyar nan.
Ya ce, "Kun dauki alhakin yaron nan, ku nemi gatararsa wallahi Yahuza bai taba fada min wata magana game da Abdulmajid ba, sai dai ma ya dinga boye min abin da ke wakana don kada in doke ki. Kin manta irin tashin hanklin da yake shiga tun ya na yaro idan ina dukanki?Kin san dai ba na tsoronki kuma ba na mahaifiyarki, da har zan yi muku rantsuwa Alan dan kar ku qara dukan Yahuza. Ina da ikon da zan saka dokar kada a qara dukan Yahuza har ya girma, kuma dole a bi maganata. Dan haka kar in sake ji ko in gani an bakantawa yaro a bisa laifin da bai ji ba kuma bai gani ba. Ko yau kika kula Abdulmajid a fili ko a waya labari zai ruske ni, zan dauki mataki mafi tsaurin gaske akan ku, ku dukka."
Daidai lokacin Yahuza ya gama shan koko ya dauko jakar makarantarsa, Malam ya kama hannunsa suka fice ya raka shi har cikin Giginyu Primary.
Sajida ta sulale ta zaune gami da jan wata
doguwar ajiyar zuciya mai dauke da jimami hade da rudani. Haka Umma Furera ta shiga irin wannan hali ba shiri ta lalubo 'yar kujerarta ta zauna ta doka tagumi.
Lokaci mai tsawo aka dauka aka rasa wanda zai fara magana a junansu. Ba tare da Sajida ta yi niyyar furtawa ba bakinta ya yi caraf ya fitar da tambayoyin da suka addabi zuciyarta.
"Wannan wanne munafikin ne yake bibiyata akan Abdulmajid? Wallahi sai na gano munafukin nan da yake so ya raba ni da Abdulmajid, ko waye ko kuma ko wacece, duk tsufanta ko kuma duk tsufansa ko da
gemunsa ya na ja da qasa, sai na ci mutucinsa na tozarta su ko da yin haka zai jawo a raba ni da numfashina a duniya."
Umma Furera ta ce, "hakika na yarda ba Yahuza ba ne ya fada, don da Malam ba zai boye ba. Kuma duk abin da Malam ya yi rantsuwa gaskiyar ta kai gaskiya. Daman Yahuza ban san shi da gulma ba, shi dai a bar shi da kwadayi da roqo. Kash na dau alhakin d'ana."
Chapter 18 · 0% Book details