← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 64

Sashe 46

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*** *** ***
A daidai wannan lokacin Samira da tawagarta na can su na ta su walimar. Samira ta dage ta cije ta danne tsananin kishinta ta shiga cikin 'yan uwa da qawayenta su na taya Bakura farin cikin aurensa. Don haka an zuba kujeru a farfajiyar gidan, an yi dafe-dafe, an hado kayan maqulashe, mata ne zalla suka taru. Wata Malama ce mai suna Malama Jamila take wa'azi, tana tunasar da mata darajar miji a wajen matarsa. Ta na fadakar da mata su cire zafin kishi a ransu su zauna da kishiyoyinsu lafiya. Daga qarshe ta fadakar da mata da su kula da tarbiyyar 'ya'yansu, musamman 'ya'ya mata.
Daga dukkan alamu wa'azin yana ratsa zuciyar Samira, ta yi shiru tana sauraro. Cancandi! Amma fa Samira ta zuba kyau, kai ka ce ita ce amaryar idan ka duba tsadaddiyar material da ke jikinta, sai walkiya take gata da iya kwalliya. Sai dai duba daya za ka yiwa Samira ka tabbatar ta rame, tana cikin damuwa. Haka 'yarta Zahra ta yi tsuru ita da qawayenta a gefe da alamar damuwa a tare da ita.
Tun qarfe takwas na dare Alh. Bakura ya tura motocinsa kakaf dana abokansa gidansu Sajida don dauko amarya da masu rakiyarta. Amma ba a samu an fito da amarya ba sai qarfe goma na dare, saboda gwagwarmayar da ake ta yi da amarya, ta bujere ta ce ba za a kai ta ba. Ihu take tana bori, tana faduwa tana burgima a qasa. Hankalin kowa ya tashi, babu wanda bai zo ya tsaya akan Sajimajid ya yi mata nasiha ba.
Malam da kansa ya shigo ya tashi Sajida tsaye, ya goge mata hawaye, ya dau lokaci mai tsawo yana ba ta haquri, sannan ya shiga yi mata nasihohi masu ratsa jiki, gami da jawo mata manya-manyan ayoyin Kur'ani mai girma, wadanda suka yi magana akan bin iyaye da bin miji. Daga qarshe ya yi mata magiya da roqo akan ta rufa masa asiri ta shiga mota a kai ta gidan mijinta, kada ta ba shi kunya idan ta je kuma ta zauna lafiya da kowa. Ya yi mata addu'a, gami da fatan alkhairi ya dora da godiya. Domin ya ga jikinta ya yi sanyi, tana hawaye kanta a sunkuye a qasa.
Ta dauko gyalenta ta yafa, ta dauko dankwalinta ta karkade ta daura ta sharbe wani zazzafan hawaye ta fara tafiya a hankali kai ka ce kwai ne ya fashe mata a ciki, ta nufi qofar fita ba tare da ta cewa kowa komai ba. Duuuuu'!! Haka mata suke biye da ita har qofar gida inda motoci suke.
Galla-gallen motoci ne duma-duma masu sanyin A.C da sautin kida reras a qofar gidansu Sajida. Wacce ta fi kyau da tsada ita ce aka Kawowa amarya gabanta aka yi mata tayi ta zo ta shiga gidan baya, amma ta qi shiga. Daga qarshe aka ba ta zabi ta shiga duk wacce take so, Sajida tsaye take qiqam ta qi motsawa.
Ijiyayye awartaq ce ta zo ta rada mata wata magana a kunne ko sakon daya Sajida ba ta qara ba aka ga ita Ijiyayyen sun nufi wata jifgegiyar mota qatuwa a cikin jerin motocin da suke laye. Sajida ta bude gidan gaba ta zauna, yayin da Ijiyayye ta shiga baya.
Umma Furare ta yi sauri ta ce da wasu tsofaffi biyu yayyanta su je su shiga motar da Sajida ta shiga, don ba ta yarda da wannan radar da aka yi ba. Haka kuwa aka yi, zuruf su Sajida suka ga tsofaffi biyu sun fado cikin motar sun zauna. Babu wanda ya ce da kowa komai. Sai diddika ake cikin motoci, duk motar da ka leqa mata ne jingim da 'ya'yansu wasu kan wasu. Haka suma 'yan mata sun cika motoci da yawa ana ta falli ko Allah zai sa daga cikin abokan ango daya zai dasa. Duk yawan motocin nan sai da aka bar wasu a qasa, saboda yawan mata, wasu ma 'yan gayyar sodi ne sun zo su ga qwakwab.
Umma Furera na küka tana dagawa Sajida hannu, haka shi ma Malam kwalla yake yana tsaye a gcfe, har motocin suka ja suka tafi a laye.
Motar da amarya ke ciki tana tsakiya, suka hau titi dodar aka nufi gidan Bakura. Sajida ta juya gefenta ta dubi direban da yake tukawa sanye yake da rawani ya rufe fuskarsa Idanuwansa kadai ne a waje, shi ma ya dube ta ya yi murmushi. Cikin harshen turanci Sajida ta yi magana, saboda tana gudun kada tsofaffin nan su ji abinda a suke cewa.
Ta ce "Who are you?"
Ya lankwashe murya ya ce, "Sajimajid."
Haqiqa wannan muryar tayi kama da muryar abin qaunarta Abdul majid. Kan ka ce kwabo Sajida ta saki ranta farin ciki ya gauraye zuciyarta. Ta waiwayo da sauri ta dubi Iyayye wacce its ce umul aba'isin da ta hada wannan tuggun tayi yadda ta yi ta hado Sajida da Abdul majid har sai da suka hadu suka ga juna. Su na hada ido suka yi wa juna dariayar farin ciki.
Ya saka hannu ya zame rawanin da ya nada don yin badda kama ya dubi Sajida duba na so da qauna cikin harshen Turanci.
Ya ce, "Kin rame, kin kode, kin lalace, iyayenki su na cutarki baby."
Ta yi naira-nairai da ido hawaye ya kwararo ta sunkuyar da kai qasa ta ce, "Yaya zan yi? Yaya ka ke tunanin rayuwata zata kasance idan ka bar ni a cikin wannan halin? Don haka yanzu ba zan bari ka tafi ka barni ba sai dai ka Juya kan motar nan mu gudu a neme mu a rasa."
Saboda dimaucewa bai san sanda ya taka burki gaba daya suka kusa buga baki da gaban mota, sannan ya ci gaba dà tafiya.
Ya ce Baby, ya ya zan yi da tsofaffin nan da suke kallona tsuru-tsuru?"
Sajida ta juya ta dube su cike da takaici ta galla musu wata uwar harara Kai ka fi cancanta
Chapter 46 · 0% Book details