Sashe 49
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a waje ko yana barci sai ta jira shi ya zo sun ci tare tun sanda suka yi aure. Sun fara cin abincin kenan, sai Samira ta dube shi ta yi gatsine. Ta ce "Af, ya za a yi ka zo ka zauna kana cusawa cikinka abinci, ba ka damu da amaryarka ba, yaya ta kwana, ko me ta ci, ko me za ta ci?" Bakura ya yi dariya ya ce, "Ai bakuwarki ce, na san ba za ki bar ta da yunwa ba." Takaici gami da daci ne ya dasu a zuciyar Samira. Ta tabe baki ta ce, ai gara aje a kira ta ta zo mu hadu mu karya tare ka ga sai ka fi jin dadin cin abinci kana yi kana kallonta, don na ga alamar har wata nutsuwa ka ke idan a gabanta ka ke." Bakura ya kwashe da dariya Ya ce, "Kishi, kishi, Samira kishi sunanki daga yau. Yaushe aka kawo Sajidar da har ki ka lura ina nutsuwa idan a gabanta ne? Jiya-jiya ne fa." Haka dai suka dinga fafatawa har suka gama cin abinci. Bakura ya yi zunbur ya mike, gami da duba agogo. Ya ce, "Kaduna nake so in je akan maganar wadannan motocin da nace an turo min daga America sun zo, sai kin zaba kin darje kafin kowa ya zaba, saboda ke ce gimbiyar gidan." Ta harare shi, ta ce, "Ka ce dai ka yi sauti a siyowa amaryarka mota ba ni ba." Ya kwashe da dariya ya suri mukullin mota yana shirin ficewa. Ta sa hannu ta kamo hannunsa, ta ce, "Ka fita ka je ina? Ai dole ka shiga kaga lafiyar abar qaunarka, kafin ka fice tunda ba ita ta kawo kanta ba, kai ka ajiye ta." Bakura ya yi dariya ya ce, "Kai! Kai! Nima na jawowa kaina, na zama kamar waina sai juya ni ake ta ko'ina. To mu je ki raka ni dakin." Samira na gaba yana biye da ita har falon Sajida. Sajida na ganin su ta daina fara'a ta dauke kai ta juya musu keya. Sai kawayen ne suka gaishe su. Su Kuma su Samira suka gaishe da tsohuwa. Tsohuwa ta amsa, gami da cewa "mu yanzu za mu koma gida, ga Sajida nan amana, kuma ku yi hakuri da halinta, har Allah Ya sa ta gane." Samira ta danne zuciyarta ta kalli Sajida ta ce, "Amarya ina kwana. Ko ba ki gaisa da ni ba kya gaisa da angonki ai ko." Sajida ta yatsune fuska ta tabe baki ta amsa gaisuwa a ciki-ciki. Bakura kuwa ba a raba shi da qurawa Sajida ido. Ya tafi can wata duniyar tunani yana tuno kamannin Zuhuriyya, yana hadawa da abinda idanuwansa suke gane masa. Kamar daga sama yaji muryar Samira ta katse masa tunaninsa da yake. Ta ce "Sai ka sa direba ya kai su gida, kuma ka kawo kudin budar bakin amarya a bawa qawayenta su raba." Nan da nan qawayen amarya suka warware kowacce fadi take, "A ba mu kudin siyan bakin amarya." Bakura ya yi dariya ya ce, "To zan bawa Samira za ta sallame ku." Ya juya ya fice, Samira na biyo da shi su na tafe Su na kallon dakwalkwalallen darning table din Sajida kaca-kaca da abinci da kwanukan da suka ci. Kowanne a watse ba tare da an kinkintsa wajen ba, balle a kwasa a kai kicin. Kowacce da ta gama ci sai ta koma Kan kujera ta nade. Don haka Samira na fita ta kira Grace ta ce ta shiga ta kwaso mata kwanukanta ta gyara musu kan tebur. Bakura da Samida suka dinguma wajen motoci, ya zabi wacce yake so ya shiga, ta zo ta dafa murfin mota. Ta ce, "Kawo kudin 'yan mata da ka yi alkawari." Ya ce, 'Ke za ki sallame su ba ni ba, tunda baqinki ne." Kafin ta ce wani abu ya jawo kofar motarsa ya rufe ya ja dogon ribas yana sheka mata dariya. Ta tsaya tana kallonsa kawai tana takaicin wannan al'amari, domin ita tafi jin haushin kanta da take shiga safgarsa da amaryarsa, ga shi ta zame masa abar tsokana tamkar wata kakarsa. Ta gyada kai ta yi qwafa, gami da cije baki alamar za ka dawo ka same ni. Ta na shiga falo ta yi kicibus da qawayen amarya da tsohuwa sun fito za su tafi. Cikin fara'a take yi musu magana. "Ba dai har kun fito ba, ba za ku yinin mata ba har ta sake warwarewa ba?" Su ka amsa cike da murmushi, "A'a daga gida aka yi waya aka ce mu dawo." Samira ta ce, "To ku jira ni ina zuwa." Ta shiga dakinta zuwa wani dan lokaci ta fito dauke da kudi, gami da wata leda a shaqe da sabulai kala-kala. Ta miqa musu ta ce "Ga shi dubu ashirin ce yace a baku, wannan kuma sabulai ne kwa yi wanka ni na baku." Suka ji wani tsagoron farin ciki ya rufę su, sai suka zube su na godiya. iyayye ta lankwashe murya ta ce, "Hajiya Samira, gaskiya ba zan 6oye miki ba ko a bayan idonki za mu fada kina da kirki, kuma samun mace kamar ki sai an tona a cikin mata." Samira ta yi dariya ta ce, "Ba komai ai mun zama daya. Ku je bakin get ku tambayi Lurwanu direba ku ce na ce ya kai ku gida da mukullin mota a hannunsa." Haka tsohuwar nan ta dinga shi wa Samira albarka, har suka fice. Samira ta dawo ta zauna a falo tana huci, tana fitar da zazzafar iskar da ta mamaye huhunta. Saboda ba karamin karfin hali ta yi ba wajen danne kishinta, duk wannan kissar da kisisinar ba ta kai zuci ba. Zuciyarta tafasa take tamkar ruwa akan wuta. Daman Sajida jira take kowa ya watse, Allah- Allah take duk su tafi su barta ta kunna sabuwar wayar da Abdulmajid ya aiko mata, don su yi magana. Fitar su iyayye ke da wuya ta dauko wayar ta saka a caji, ba tare da ta bari cajin ya cika ba ta kunna, gami da saka sabon layi da recharge card ta matso lambarsa wacce daman tuni ta haddace ta akai. Koda kuwa daga barci aka tashe ta za ta karanto lambar a Kwakwalwarta. Bugu daya ya dauka, duk da bai gane kowace ce ba, Kai ka fi cancanta