Sashe 56
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
WACECE ZUHURIYA? Bakura ya gyada kai ya sharce hawaye da bayan hannunsa ya sunkuyar da kai qasa kamar mai tunani, ya dago ya dubi jama'ar da ke zaune a falon. Ya ce "Zuhuriya ita ce uwata, ita ce ubana, ita ce yayata, ita ce qawata. Ba ni da kowa a duniya sai Zuhuriya. Allah shi ne gatan bawanSa sannan Zuhuriyya ita ce gatana. Ban san kowa a rayuwata ba sai Zuhuriya, tun daga yarinta har izuwa girmana." Daga dukkan alamu ba su fahimci abin da Bakura yake nufi da wadannan kalamai da ya fassara Zuhuriya da su ba. Akwai alamar daure kai da zuzurfan tunani a zuciyoyinsu. Zahra ta ce "Abba, da farko ka ce kana da iyaye har kuna bara tare sannan ka ce Zuhuriya ce uwa ita ce uba? lyayenka sun rasu ne?" Bakura ya yi murmushin qarfin hali ya girgiza kai ya ce "Alhamdulillah, da kika yi min wannan tambayar, Mahaifana ba su rasu ba. Na kira Zūhuriya da wannan Sunan na uwata kuma Ubana, saboda wasu dalilai masu yawa. Kamar yadda na fada muku a cikin kasuwar garinmu Mangono muke yini a cikin kasuwar ma a bakin bola muke zaune. Tun daga safe har dare, wata rana mu kwana a nan idan kuma an koro mu daga cikin kasuwar mu fito waje mu kwana a waje ko mu je bakin tasha mu kwana in da mahaifina yake bara." Kuka ya kecewa Zahra don tausayi, yayin da idanuwan Samira ya cika taf da hawaye. Abubakar kuwa tuni ya shiga wani hali na daurewar kai, duban mahaifinsa yake ta yi, tamkar hoto, domin bai zaci mahaifinsa ya san wani abu mai su na talauci a rayuwarsa. Malam kuwa ya shiga rudani yana zuci-zuci ya ji qarashen labarin da yadda aka yi Bakura ya san lya Azumi. Sajida kuwa gaba daya qwaqwalwarta ta rikice, domin ta ji labarin Bakura bai shafe ta ba, to me yasa Umma Furera ta ambaci sunanta a waya'? Me yasa Iya Azumi ta ce ta tambayi Bakura shi ya fi kowa sanin ta? Ta ina Bakura ya santa har ya fi kowa saninta? Wannan al'amari ya razana zuciyar Sajida. Babu yadda za ta iya katse shi, dole ta ci gaba da sauraron Bakura, amma ta qagu ta ji qarshen labarin. Bakura ya ci gaba da cewa "Na hadu da Zuhuriyya a cikin kasuwar garinmu Mangono, a daidai inda nake kiransa da gidanmu wato bakin bola, ita kuma sun zo wani shago siyayya, shagon yana daf da bolarmu. A lokacin ina da shekaru uku, Zuhuriya na da shekaru goma sha hudu a duniya. Amma a lokacin an dade da yi mata aure har ta haifi da kafin a yi suna ya rasu. Sun zo Mangono ne ita da mahaifiyarta ganin danginsu. Domin mahaifin Ummata Zuhuriya Alh Umar dan asalin garin Mangono ne, kuma ma dan sarauta ne a lokacin ya rasu sai Yayansa shine hakimin garinmu haka aka ba ni tarihi." Samira ta buga tagumi tana duban Bakura, duba cike da tausayi tana mamakin duk wannan shaquwar da suka yi amma bai taba zama ya faiyace mata irin wannan tarihin rayuwarsa ba sai yau da yake fada take ji. Ta tambaye shi "daga nan ya aka yi?" Bakura ya yi shiru, saboda tsananin zafin da zuciyarsa ke yi. can ya ci gaba da cewa."Ina qarami sosai, amma mahaifñyata tana dukana, dukan da ko wani qato ake yi wa sai ya kwanta jinya, amma ba laifinta ba ne kamar yadda na fada muku a baya tana da tabin hankali. A daidai lokacin da Ummata Zuhuriya da mahaifiyarta da kuma qanwar mahaifin Zuhuriya suke cikin shago su na siyayya ni kuma na tafi yawo cikin kasuwa. Mahaifiyata ta kamo ni ta kawo ni bakin bola ta jibge ni yayin da ta samo bulala ta yi ta duka kamar ta sami casar gero. Bulala ta kakkarye tasa hannu ta daka har ta gaji sannan ta saka haqoranta ta cije ni bakina ya fashe, goshina ya yi loti, yayin da bayana da duk ilahirin jikina ya daddare ya yi shatin duka. Tana dukana tana fada tana cewa, "Indara na'aduwa kozina famdime." Malam ya ce "Me take cewa kenan?" Zahra ce ta fassara musu domin ta fi sauran qannenta jin yaren. Ta ce "Abin da take cewa shine ina kake da shi, inda ya fi nan bakin bola?" Iya Azumi ta ce "Haka aka yi kuwa, hankalinmu ya tashi, musamman Zuhuriya har kuka take saboda tausayin yaron nan, abin ka da mai son yara domin Zuhuriya Allah Ya yi mata son yara." Gaba daya suka juyo su na kallon Iya Azumi, duba na mamaki. Sajida ta tambaya cike da mamaki "lya Azumi, ya aka yi ki ka sani kina wajen ne?" Iya Azumi ta gyada kai ta ce "Ina wajen, ai muna tare da Zuhuriya a cikin kantin." Bakura ya ce "lya Azumi ita ce mahaifiyar Zuhuriya, wacce ta haife ta." Kamar an tsikara musu allura haka kowa ya zabura ya waiga yana duban Iya Azumi. Daidai lokacin kowa ya gyara zaman don jin labari, don labari ma yanzu aka fara. Sajida ta ce a ranta "Kenan idan Iya Azumi kaka ce a wajena, ashe ina da dangantaka da Zuhuriya. Ashe Zuhuriya 'yar uwar Umma Furera ce kenan?" Iya Azumi ta ci gaba da cewa "Zuhuriya ta tambayi mai shagon da muke siyayya a shagonsa. me yasa take dukan dan qaramin yaron nan da bai wuce shan nono ba?" Mai shagon ya yi murmushi ya ce, "Ai tana da tabin hankali. Dukan yau ma kadan ne ai, wata ran tana yi masa wanda ya fi haka." Zuhuriya ta fashe da kuka tana. Ta ce masa "Me yasa bakwa kwatarsa idan tana dukansa?" Ya ce, "Ai babu mai iya zuwa kusa da ita idan tana dukansa, zafin rai ne da ita idan ka je sai ta hada da kai." Zuhuriya ta sake tambayarsa "Ina Baban yaron, ai da an kwace shi daga hannunta, don kar ta kashe shi." Mai kanti ya ba ta amsa, "Baban yaron makaho ne, shi ma almajiri ne, bara yake." Ta ce" ko a dangi ba za'a sami mai daukarsa ba?" Ya ce, "Ina ji babu, amma wasu sun so su dauka ta hana su. Ai ba za ku tausayawa yaron nan ba sai idan uban ya kai shi wajen wanzami ya yi masa aski kwalkwal. Yini take tana dukan kan yaron nan, wai sai ta ci ladan aski. Duk juyin da ta yi sai ka ji raff-raff ta dalla masa duka a kai, sai ka ji ya dau kuka. Yini suke 'ana abu daya har sai gashi ya fito akan sannan yake hutawa." Bakura ya kwashe da dariya, sannan kuma ya fashe da kuka ya girgiza kai alamar tausayawa kansa da kansa. Iya Azumi ta ci gaba da cewa "Tun a lokacin Zuhuriya ta je wajen yaron ta goge masa hawaye ta ba shi alewa, ya yi shiru ya daina kuka. Ta bawa mahaifiyarsa sadaka, sannan ta dawo shagon da muke zaune. Ta dube ni ta ce da ni, "Innono (sunan da suke kirana kenan) ina son yaron nan, ina so in dauke shi in riqe shi kamar dana tun da yaron da na haifa ya mutu." Ni kuma na zazzage ta na ce kada ta sake cewa za ta dauki wani yaro don ta rike. Dalilina kuwa shi ne daga nesa muka zo baqunta tafiya za mu yi, idan muka tafi kuwa a shekara biyar ba za mu dawo ba don jifa-jifa muke zuwa, saboda nisa ga tsadar kudin mota bamu da hali da kyar muka hada wannan kudin motar da muka zo da dan abin tsaraba. Gashi mahaifin Zuhuriya ya dade da rasuwa na yi wani auren a Cinkilawa can qaramar hukumar Warawa dake kusa da lahadin makoli a hanyar Wudil cikin jihar Kano. Da Zuhuriya na je garin a matsayin agola, saboda ita kadai ce 'yata a duniya na wi yarda dangin mahaifinta su karbe ta a Mangono. Ita ma Allah cikin ikonsa ta sami miji a Cinkilawar na aurar da ita tana da shekaru goma sha daya a duniya. Ta samu ciki ta haihu kafin a yi suna yaron ya rasu. Bayan ta yi arba'in ne na ce to ta shirya in kawo ta Mangono ta gaishe da dangin Babanta saboda sun dade ba su hadu ba ko bikinta ma ban samu na fada musu ba, mijina ne ya wakilce su. Dan haka sai naga ta ina? Ta ya ya za mu dauki wata dawainiyar bayan muma muna ta kanmu a can, don haka na hana ta. Ta yi ta kuka tana yi min magiya har muka isa gida. Kowa ya fara tambaya me aka yi wa Yagana take kuka, domin su a can dangin uban Yagana suke kiranta. Ni da ita babu wanda ya fada musu abinda ya faru. Kamar yadda Bakura ya shaida muku a baya yayan Babanta shi ne hakimin Mangono, don haka hakimi da kansa ya kira ta, don yana jiyo hayaniyar mata a tsakar gida su na yi da bakin su su na tambayarta dalilin kukan da take. Ya tambaye ta sannan ta fada masa abun da take so, da yake qaramin gari ne kowa ya san kowa sai ya yi dariya. Ya ce "Wannan ba wata matsala b8 ce, in har za ki iya riqe shi a dalilina za a baki shi. Daman ya kamata a ceto rayuwar yaron nan yana shan wuya a wajen mahaifiyarsa. Sai dai sai kin daure, za ki dinga kawo shi lokaci-lokaci ana ganinsa yana ganin iyayensa." Hakimi ya shaidawa Zuhuriya ai su na da alaqa ta jini da mahaifiyar Bakura, don haka dangimsu sun san komai. Washe gari ba tare da kowa ya sani ba Zuhuriya ta dauki abincinta na safe koko da qosai ta tafi bakin kasuwa ta kaiwa Bakura da mahaifiyarsa suka ci. Kan ka ce kwabo hira ta gauraye tsakanin mahaifiyar Bakura da Zuhuriya. Bakura kuwa tuni ya haye cinyar Zuhuriya kamar ya sami wata uwar. Da rana ma ta dibi abinci ta kai musu, bata tashi dawowa ba sai daf da magariba, sai ga ta goye da Bakura a bayanta, mahaifiyarsa na biye da ita ta ce mata ta zo Hakimi yana kiranta. Cikin dabara da wayo hakimi yake yi wa Fatukamba bayanin cewa Zuhuriya za