Sashe 58
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
wani mai sauraro. Akwai hikima a wajen shi kansa mai bayar da Labarin. Babu abin da zuciyar Zahra ke aiyanawa sai sha'awa da marmarin ta je wadannan qauyukan ta dandana yadda suke rayuwa. Ji take dama ita marubuciya ce ta rubuta' labarin nan har take tunanin sakawa littafin su na LABARIN BAKURA. Bakura ya katse mata tunani ya ci gaba da cewa "Takaici ya qara rufe Innono. Ta ce "An sake ku ko? Ni kuma zan daure ku. Ka sake kashe mata auren ko? Za ku shigo ku same ni." Mu na bin katanga muna rabewa, ga yunwa da kishirwa. Can na sulale na zauna na fara gyangyadi. Da sauri Zuhuriya ta tashe ni ta kama hannuna muna sauri muka je gidan wata mai abincin siyarwa. Ta kwance gefen zaninta ta kwanto wasu 'yan kudadenta sulalla fa kwabbuna ta siya min tuwo malmala guda na cinye, ta bani ruwa na sha, ta kai ni bandaki na yi fitsari sai ta saba ni a baya na yi barci. Ban tashi farkawa ba sai da tsakar dare da na ji tururruwa ta baibaye ni tana cizona. Ashe zauren qofar gidan Innono ta shige ta labe bayan Malam Audu ya shigo gida ya rufe ba tare da ya san muna labe ba anan ta yi mana shimfida da zani muka kwanta, ashe da ramin tururuwa. Sunanta na kwallawa kira cikin kuka na ce wani abu yana cizo na ga tsananin duhu. Zuhuriya ta daka tsalle ta tashi ta ciccibe ni ta kade min jikina muka koma tsakar gida muka qarasa kwana. Da duku-duku gari bai waye ba Innono ta tsara mu a lungu. Zuhuriya ba ta bari dukan ya same ni sosai ba, karewa take yi tana fadin "Bakura yaro ne ni ki dake ni bai san komai ba." Sai Bakura ya surnano da hawaye zazzafa ya ce "Zuhuriya na sona a rayuwarta, haka nima nake matuqar qaunarta a rayuwata. Muna cikin wannan hali na tsangwama ga aiki, kamar bayi sai Zuhuriya ta ga gara ta sake aure ko gidan mijin zai fiye mana kwanciyar hankali. Ta auri wani tsohon malami don a lokacin ana ta surutun wai ta auri tsohon mutum tana yarinyarta son kowa qin wanda ya rasa, Malam yana da makarantar allo duk karkarar nan babu makaranta mai yawan almajiransa. Sunansa Malam Idi mahaddacin Kur'ani ne sosai matarsa daya ta rasu a shekarar da zai auri Zuhuriya. 'Ya'yansu kuwa sun yi aure har suma sun hayayyafa, don haka muka ji dadin zaman gidan ba mace, ba 'ya'ya. Alhamdulillahi, a wajen malam idi muka fara samun ilimin addini daga ni har Zuhuriya. Don idan aka fara karatu tun da Asuba har sai rana ta fito. Haka da yamma ma har sai Magaruba. Bayan sallar Isha'i kuma har kusan sha biyun dare ana karatu sannan mu kwanta. Ina cikin almajirai ina wadaqata ga abinci a gidan ba yankewa. Duk da dai dawa ce da masara sai gero kullum. Shckarar mu kusan uku a gidan malam ya rasu. kasancewar ba ta haihu da shi ba, bata da gadon komai dole muka tarkato kayanmu bayan ta gama takaba muka dawo Cinkilawa gidan Innono. Rayuwa ta dawo irin ta da, dole Zuhuriya ta fara sana'a tana danwake da safe mu dauka aka mu kai makarantar boko da ke Jalawa da qafa muke tafiya tunda ga Cinkilawa kullum. Idan an yi break 'yan makaranta su yi ta siya. Ni ba dan makaranta ba ne, amma ina jiyo abin da ake koyarwa caraf sai na riqe ABCD har zuwa Z. Akwai wani Malami mai suna Isa, dan asalin garin Jalawa ne sai ya nuna yana son Zuhuriya kullum sai ya sayi dan wakenta. Ya ba ta shawara mai zai hana ta saka ni a aji daya, nima in yi karatun maimakon zaman gindin bishiya muna jiran yara su fito, ai gara ni in dinga shiga aji. Sai ta jira a tashi mu tafi gida. Zuhuriya ta qi amincewa amma ni na ce ina so har da kukana. Malam Isa ya ce shi zai karbar min uniform lokacin komai kyauta ake bayarwa har littattafai. Sai ta yarda ta saka ni a makarantar tunda ta ga ina so. Har na zo na fi duk 'yan ajin qoqari. ldan mun fito break da gudu zan taho wajenta ta zuba min danwake har yara suke kirana dan gidan mai dan wake.Kai ka fi cancanta