Sashe 59
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan an tashi da rana sai mu doro daron d'an wakenmu aka mu koma garinmu Cinkilawa. Innono ta huta ciyar da mu yanzu, muna da sana'armu don haka rigimar ta dan lafa, ba ma yini a gidan ma balle a ce mun yi laifi. Abu kamar wasa Malam Isa ya ce yana so ya auri Zuhuriya su zauna a Jalawa, saboda mu huta zirga- Zirga kullum, gidansa ba nisa da makaranta ya yarda zai riqe ni, zai kuma bar ta ta dinga zuwa tana sayar da danwakenta. Ta amince suka yi aure, muka dawo Jalawa da zama. Lallai mun sami ci gaba, saboda gidan Malam isa na siminti ne, ga shi da babur dinsa na hawa. Yana da mata daya mai suna Sahura da 'ya'ya biyar. Ko ban fada muku ba, kun san za a yi dauki ba dadi a gidan nan. Inda aka sami saukin rigimar Sahura na tsoron Zuhuriya, dan sun goga ta ji karon bai yi mata da dadi ba. Zuhuriya ta iya tsiwa bakinta caicai baya mutuwa, damara take ci a yi ta fada ga ta ba ta da kiba, amma ko a dambe ba a kayar da ita. Ta kwatar min 'yancina, duk da ni ba dan gida ba ne amma ba ta yarda wani ya takura min ba. Dole Sahura da 'ya'yanta suka daga min qafa na miqe qafata na yi dayday a gidan kamar gidan ubana. Karatu nake tukuru ba na fashi har Allah yasa na Kai primary 4. Kokari da cancanta aka saka ni a cikin masu daukar jarawar tafiya sakandire na zana. Allah CIkin ikonsa na ci, na sami tafīya makarantar 'yan maza ta Wudil. Malam Isa ya taimaka min wajen karbo min akwati, katifa da bokiti daga qaramar hukuma, amma sauran siyayyar Zuhuriya ce ta quge 'yan kudadenta ta siya min duk abin da zan buqata. Duk da a lokacin ba a matsalar abinci a makarantu. Na je makarantar kwana na dace da abokai na gari na ci sa'a shugaban makarantarmu (pricipal) mai suna Malam Abbas Shagari yana sona, saboda qokarina. Aka yi jarrabawa na zo na daya, aka ba mu hutu, local government dinmu ta kai mota aka kwaso mu. Ina isowa gidan Malam isa na iske shi a qofar gidansa yana zaune a kan tabarma. Da murnata na qaraso wajensa na duqa na gaishe shi na zaro report card dina na miqa masa cike da murna. Ya yi dususu kamar bai sanni ba, ya duba galala ya miqo min abu na. Sai mamaki ya rufe ni saboda a zatona zai yi farin ciki da ganin sakamakona, shi yake koda ni yana yabon qoqarina har hakan tasa nake qara dagewa ina karatu sosai. Saboda shi ne ma yasa na dage ba dare, ba rana ina ta karatu har sai da na fi kowa cin jarrabawa a ajinmu. Na tashi jikina a sanyaye na dauki buhun kayana na shiga gida farin ciki ya rufe ni ina murna saboda zan ga Zuhuriya na sha wahalar rashin ganinta da kyar na daina kukan rashinta a makaranta, ba mu taba rabuwa daidai da kwana daya tun daga sanda muka hadu. Ina shiga na iske dakinta a bude na fara washe baki na san tana ganina za ta rugo da gudu ta rungume ni. Na yi sallama na bude labule na tura kai zan shiga sai na ji an hankado ni waje, na yi tagal-tagal zan fadi a baya. Sahura na gani ta fito daga dakin ta ce da ni "Kai mahaukacin ina ne da za ka fado min har cikin daki?" Wannan maganr ta ba ni mamaki, saboda dakin Zuhuriya nè. Yaranta suka yi caa suka fito daga dakinsu suka zagaye ni. Wasu na yi min gwalo, wasu na yi min daquwa su na tsokana ta. Abin da suke fada shi ne an saki Babata ta koma Cinkilawa. Gabana ya yanke ya fadi sai na fara kuka. Na ce musu to bari in dauko sauran kayana a dakin yara. Nan ma suka hana ni shiga suka ce ta kwashe kayanmu kacokan babu ko tsinke nawa, dan haka in tafi in ba su waje. Na dora buhuna aka, ga tsananin yunwa da kishirwa ga doguwar tafiyar qafa daga Jalawa zuwa Cinkilawa, na fito jikina a sanyaye. Duba daya Malam Isa ya yi min ya dauke kai, na dube shi duba na takaici da tsantsar tsana tunda ya kori Zuhuriya sai na ji ba na sonsa, na wuce na kama hanyar Cinkilawa. Ban isa garin ba sai daf da Magruba. Ina isa tsakar gida na wurgar da buhun da ke kaina na fadi yararaf a qasa. Innono ce a bakin murhu tana tuqa tuwo ta dau salati ta kwallawa Zuhuriya kira ta taho da gudu daga daki, don ta ga abinda ya gigita Innono har take kwalla mata wannan kira haka. Ta na ganina a kwance ta rafsa ihu ta riqo ni ta tashe ni zaune tana tambayata lafiya. Na ce yunwa da kishirwa, a guje ta shiga daki ta dauko min langa a cike da alala na fara ci, kamar ban taba cin abinci ba haka nake turawa a cikina,ta ba ni ruwa a qwarya na sha. Haushi da takaici ya rufe Innono ta ce Bakura, ka zayyano min da bakinka aure nawa ka kashewa Zuhuriya?" Na zabura na ce "Innono wannan karon bana nan aka yi sakin." Ta ce "Ai a dalilinka aka yi rigimar har aka sake ta." Na shiga rudani hade da fargaba. Zuhuriya na zaune ba ta ce komai ba sai hawaye take sharaf-sharaf. lnnono ta zaiyano min duk abinda ya faru daga qarshe ta ce to an yi na qarshe tunda na girma dole in koma garinmu idan ma zan yi karatun anan in je makaranta ana yin hutu in hau motar garinmu Mangono. Hankalina ya tashi, domin ba na son a ambaci sunan garinmu ballantana a kai ni." Bakura ya zubo da hawayen da ya addabi idonsa. Malam ya girgiza kai ya ce "Lallai ka dandana maraici da wahala a rayuwarka." Cikin kuka Zahra ta ce "Abba, menene dalilin rabuwar lya Zuhuriya da Malam Isah?" Bakura ya ci gaba da magana cikin marainiyar murya "Wai ashe Sahura ta kullace ni, haushi take ji danta-bai ci jarrabawar tafiya sakandire ba, ni kuma na ci na tafi. Ina tafiya ta je ta hada mana munafunci." Abubakar ya tambaya, "Abba, wanne irin munafunci?" Bakura ya yi murmushin qarfin hali ya ce "Zuwa wajen mahaifin Malam Isa ta yi ta dinga kuka tana cewa wai bai kamata a ce ina kwana a cikin gidan nan ba, tare da yaranta dakinmu daya akwai mata, tunda na je sakandire yanzu na girma dole a mayar da ni gidanmu. Daman dakunan gidan uku ne. Daya na Sahura, daya na Zuhuriya, daya namu ni da 'ya'yanta. Shi mai gidan ba shi da daki, dakunan matan yake bi. Iyayyen Malam Isah suka kira shi, suka shaida masa cewar dole ya fadawa Zuhuriya ta fitar da yaron nan daga gidan. Dole ya sami Zuhuriya ya sanar mata halin da ake ciki, Da ya zo ya fada mata buqatar iyayensa sai ta ce muddin tana raye to tana tare da danta ta yarda za ta dauke ni daga ckin ya'yan Sahura, sai in dawo dakinta da kwana, In ya so ta hakura da mijin ya dinga kwana a dakin Sahura kullum. Malam Isah ya hau fada ya ce bai yarda ba sai na bar gidan. Ita kuma ta ce sai dai mu bar gidan tare, sai ya sake ta tun kafin in dawo. To wannan shi ne silar rabuwarsu. Na fara wayo, na fara sanin zafin magana, dan haka na shiga damuwa. Na fara tunanin yadda zan yi da rayuwata, don in daina jawowa Zuhuriya mutuwar aure, don an fara qirga mata yawan mazan da ta aura an mata shaidar ba ta zaman aure kowa ya san ni ne sila. A lokacin alalar gwangwani Zuhuriya take siyarwa da rana har gida ake shigowa ana siya. Ni da ita muke wanke wake in kai markade in kawo ta hada mu zuzzuba a gwangwanaye mu dora akan wuta. Idan ta dahu ni ne mai zubawa ina miqawa kofar gida. Mu ka tara kudi sosai a cikin hutun nan. Zuhuriya ta lalashe ni ta lallaba ni har sai da na yarda zan bi ta Mangono wajen danginmu. Domin ba na son zuwa gani nake idan ta kai ni ba za ta dawo da ni ba, kamar yadda Innono take fada kułum tun ba na fahimta har na gane cewar nan ba gidanmu ba ne, iyayena na can kuma can din ukuba ne tunda sai na yi laifi ake cewa a kai ni.." Umma Furera ta sharce hawaye ta ce "Ka san ba ita ta haife ka ba kenan?" Bakura ya nisa ya ce Eh, na sani dan na ji ana fada, amma ban damu ba, na sa a raina Zuhuriyą, ce uwata ita ce ubana don ita kadai na budi ido na gani babu mai sona mai wahala da ni sai ita. Dan a lokacin da aka fara kai ni makaranta dakyar na yarda Malam Isa ya saka min Bakura Usman Mangono dan ni tuburewa na yi na ce Bakura Zuhuriya sunana. Saboda duk sanda na yi laifi Innono tana cewa a mayar da ni Mangono na tabbatar babu alkhairi a tattare da Mangono tunda sai na yi laifi za a kai ni, don haka na ji na tsani garin duk da ban san shi ba. Zuhuriya kadai na şani a rayuwata, ita ce mai share min hawayena, idan ina cikin damuwa da ita nake so in kasance har karshen rayuwata." Sai yanzu Umar ya yi magana dan tunda ya zauna- yake kallon mahaifinsa yana sauraron wannan abun al'ajabi. Ya ce "Abba, ka yarda kun je Mangono a lokacin'?" Bakura ya ce "Mun je har da Innono ma tare muka je da ita. A wannan lokacin ne na fara ganin mahaitiyata, na ga mahaifina, dan a lokacin da na baro su ina qarami sosai ba zan iya tuno su ba. Har na ga qannena guda biyu da aka sake haifa. Babban namiji ne su na kiransa Babagana, qaramar da aka yaye kuma su na kiranta Yaana." Abubakar ya tambaya cike da mamaki "Uncle Babagana da Aunty Yaana kake nufi?" Bakura ya gyada