Sashe 16
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Na
👇🏻👇🏻👇🏻
Ta yi dan murmushi ta ce "Abba Sajida da Umma Zuhuriyya ta yi kama ko Mamarta Furera?"
Bakura ya yi shiru na dan wani lokaci sannab ya ce "Sajida da mahaifiyarta Furera su na kama ne?"
Zahra ta girgiza kai
Ta ce "Ba sa kama kwata-kwata. Mamar Sajida fara ce sol, amma duk fuskartka tsage-tsage irin na Fulani kuma ita mai qiba ce sosai. Hancinsu ba iri daya ba, bakinsu, idonsu, kafarsu, qirar jikinsu, duk daban-daban ko kadan ba su yi kama ba. Sajida tana da kyau sosai ta fi mahaifanta da wannan qanin nata Yahuza kyau."
Bakura ya yi shiru yayin da tsananin rudanin da yake ciki ya sake linkuwa a zuciyarsa. Ya dade ya na tunani a ransa. Ya na kuma tambayar kansa da kansa, "Shin ya ya aka yi haka? Ta ina Sajida ta samo kamanninta, tunda ba ta yi kama da mahaifinta ko mahaifiyarta ko qanninta Yahuza ba? Ita kadai kamarta daban, kuma sak kamar Zuhuriyata. Qalu innalillahi wa'inna ilaihir raju'un."
Kamar daga sama ya ji Zahra ta ba shi amsar duk wadannan tambayoyin da ya jero a cikin zuciyarsa.
Ta ce "Abba, ikon Allah ya wuce haka. Allah Ya na tsara halittarsa yadda ya nufa. Zai iya halittar d'a bai yi kama da uwa ko uba ba, a can cikin dangi sai ya yi kama da wani d'orin d'osano. Ko kuma ma sai su yi kama babu danganta ko daya."
Ya gyada kai ya ce " zai iya faruwa kadan daga cikin ikon Allah."
Zahra ta gyara zama ta ce " bana son Sajidar nan don bata da tarbiyya bata jin maganar iyayenta kuma mamarta ke taya ta."
Wannan karon kallonta ya yi da sauri cike da mamaki har da bude baki.
Cikin rawar murya ya tambaya " me ta yi ?"
Zahra ta tabe baki ta ce " da alama Babanta ya hana yin waya da samari sai ta taka turmi ta leqe maqwabta ta ari waya ta yi masa."
A tsakiyar titi ya taka burki ya tsaya Allah Ya sa babu mota a daf da shi da an buga masa. Zahra ta firgita matuqa ganin yadda ya razana abin har ya bata tsoro.
Da kyar ya dawo hayyacinsa sannan ya gangara gefen hanya ya tsaya. Zahra tana jero masa tambayoyin da ya gagara bata amsa mata. " Abba me ya faru? Me ya as ka taka burki? Me ya as muka tsaya?"
Ya dade a kishingide a jikin kujera ya rufe ido ya dago ya gyara zama muryarsa na rawa ya ce " bank labarin abinda ya faru dalla dalla."
Zahra ta bashi labarin komai amma bata ce an karbi aron wayarta ba, dan kada ya huce akanta yadda ta ga ya hasala yana cije baki.
Ya daki sitiyarin motar da qarfi ya na magana cikin jin kakkausar murya da fusata.
" daga yau babu ke babu Sajida, kada ki sake cewa in kai ki ki ga me kama da Zuhuriyya. Na yi kuskure, na yi nadama, daman ban kawo ki ba."
Haka yake fada yana nanatawa kamar karatu. Ya tashi mota ya fisga kamar zasu tashi sama.
Zahra ma ta yi nadamar zuwanta gidan su Sajida da kuma bawa mahaifinta labarin abinda ya faru. A lokacin fadan yin samari a boye ya taso har suka isa gida gargadi ya ke yi mata akan kada ta biyewa qawaye masu yin samari kada itama ta ce za ta yi saurayi ko a makaranta kada ya ji ko ya gani. Duk ranar da ya kamata da maganar saurayi sai na lahira ya fi ta jin dadi.
Da alama Bakura ya kwana bai yi baccin kirki ba, walwalarsa ta ragu kowa ya kasa gane kansa. Zahra ce kadai ta sani ita kuwa ba zaa ji mutuwar sarki a bakinta ba.
Aiki ya shawa Bakura kai bai samu ya je wajen Malam Yakubu daukar karatu ba sai bayan kwanaki hudu. Ranar da ya je kuwa ko karatun bai tsaya ya dauka ba sai da ya fayyacewa Malam komai akan halinda Sajida take aikatawa a cikin gida. Ya fada ne dan tausayin Malam Yakubu ya na qoqarin yin tarbiyya amma ana ruguza masa.
Yadda ya ga hankalin Malam ya tashi sai Bakura ya shi ga lallashi akan ya kwantar da hankalinsa ya bi abin a hankali. Ya qara saka ido kuma yayi mata nasiha da addua .
Malam ya amsawa Bakura da "insha Allah ba zai aikata wani abu marar dadi cikin fushi ba, zai bi abin a hankali."
Anan suka yi sallama Bakura ya juya ya tafi gida.