Sashe 15
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Zahra ta bude baki tana kallon Sajida cike da mamaki, yayin da kalmar saurayi take yi mata reto a kwakwalwa. Furera ta tsaya tsai daga zuba kunun da take yi. Ta ce "Wayar ce dubu shida ko kudin cikin wayar? Sajida ta ce, "Umma! kudin cikin wayar ne dubu shida, wayar kuma ai sai dubu hamsin." Furcra ta gyada kai ta fada a hankali, "Cafdijam dan qarawa mai karfi-karfi za a ce in zuba ma ta kunu kyauta." Sajida ta ce "To kawata dan ba ni áron wayar ta ki in ci ko dubu daya ne." Zahra ta bude jaka ta dauko wayarta tsaleliya kirar N85 ta miqa mata. Sajida ta latsa wasu lambobi kan a jima network ya hada ta da abin kaunarta Abdulmajid. Ta fada cikin lallausar murya. "Hello darling Abdulmajid, Sajimajid ce, kar ka damu ba flashing nake ba wallahi wayar wata girl ce 'yar gidan masu naira. Ka san nawa ne a cikin wayar? Naira dubu shida, ka ga za mu iya kaiwa tsakar dare muna magana." Furera ta dubi Sajida ta ce, "Shegiyar yarinya. marar jin magana, ai sai ki shiga daki ki yi wayar kafin Malam ya shigo ya hada mu dukka ya zage." Sajida ta ce, "Umma ba abin da nake fada muku kenan ba, ga Zahra nan ita iyayenta sun yarda ta kula samari, na tabbata saurayinta ne ya hada mata wayar nan, yake zuba mata kudi." Furera ta ce, "A to 'ya'yan masu hali ma kenan balle mu 'yan Allah Ya baku ku ba mu. Laifin mahaifinki ne da ya hana." Abdulmajid da yake kan layi har yanzu yana jin abin da Sajida da mahaifiyarta su ke fada. Ya yi murmushi ya ce, "Ki ce kina magana a wayar big girl, wanne irin model ce." Sajid ta ce, "N85 ce." Ya ce, "Lallai babbar harka take yi. Ya ya sunanta ko Allah zai sa wani lokaci in kira layin kuna tare ta ba ni ke mu yi magana?" Sajida ta ce, "Ina jin Zahra sunanta, but l'am not Sure, kar ka damu ta zo ne za ta tafi ba lallai ne mu sake haduwa ba, mu yi maganarmu kawai." Sajida ta dubi Zahra, ta juya ta dubi mahaifiyarta sai ta ga gaba daya sun zura mata ido su na kallonta su na sauraronta. Sai ta ji kunya ta tashi ta shiga daki ta cigaba da yaryada masa zakakan kalamai na so da Kauna. Malam ya turo Yahuza fiye da sau biyar kiran Zahra ta fito za su tafi, babanta ya gaji da jira. Ba Zahra, ba dalilinta, domin har yanzu Sajida ba ta gama da wayar ba. Ita kuma nauyi da kunya ya hana ta je cikin daki ta sami Sajida ta karbi wayarta. Sai da Malam ya shigo da kansa ya sami Zahra a zaune a inda ya barta ya dube ya yi dariya. Ya ce, "Zahra hira ta yi dadi ko? Abbanki ya ce ki zo ku tafi, nayi-nayi ma ya barki ki kwana ya ce gobe da safe akwai makarantar boko:" Zahra ta sunkuyar da kai kasa ta ce, "Baba yanzu zan fito Sajida nake jira tana daki tana..." Furera ta katse ta ta yi sauri ta mike tsaye ta ga asiri zai tonu. Ta ce "Sajida take jira ta fito ta raka ta, ka san har sun zama kawaye, wato dai yau rakiyar kura za a yi idan ta raka ta ita ma sai kaga ta rako ta. Bari in kira Sajidar a daki ina ga kuka ma take yi na rabuwa da zahra in ce ta zo ta rakata." Malam ya ce, "Kai rakiyar meye za a yi ta yi mu tafi kawai." Zahra ta mike ta bi Malam a baya suka nufi qofar waje. Har sun kai zaure sai ta ji Umma Furera ta jawo hannunta ta cikin hijabi ta sunna mata wayar a hannunta, gami da yi mata rada a kunne. Ta ce, "Yarinya kar ki fadawa Malam ko mahaifinki sai ya yi fada." Zahra ta gyada kai ta duqa ta ce, "Na gode." Malam ya waiwayo a fusace ya ce da Furera. "Me ye kuma kike yi ma ta rada?" Umma Furcra ta yi sauri ta ce, "Lah! Ba komai kudin mota na ba ta." Sai ta tuna da mota suka zo sai ta ce, "Au! Kudin da za ta sayi 'yar alewa ta kaiwa Kannenta." Malam ya yi murmushin jin dadī ya ce, "Madalla Allah ya saka da alkhairi, to ki koma ciki rakiyarta isa." Mamaki marar musaltuwa ya rufe zuciyar Zahra da ta ga babba tana karya. Furera ta dade a zaure tana leken Zahra da mahaifinta har suka shiga mota suka tafi. Zahra ta na zama a cikin mota ta dubi mahaifinta. Ta ce "Abba ka yi hakuri na dade." Ya girgiza kai ya ci gaba da tuki. Ya ce, "Ba damuwa. Ina fatan kin ji dadin ziyarar da kika kai?" Ta ce "Eh, to gani nan dai, na yi farin ciki ban yi farin ciki ba." Bakura ya waigo da sauri ya dubi Zahra yayin da ya ji zuciyarsa na bugawa, don fargaba. Ya tambaya ya ce, "Me yasa kika fadi haka MamaKai ka fi cancanta