← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 64

Sashe 17

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*** *** ****
Malam ya shigo cikin gida ya iske Umma Furera da yaranta su na zaune a tsakar gida. Bayan ya yi sallama bai ce komai ba, sai kawai su ka ga ya tunkari Sajida ya zakulo wata qatuwar bulala dorina mai baki biyu daga cikin aljihunsa ya fara shadada mata a doron bayanta.
Ta na ihu saboda azaba, amma ta kasa gudu a sanadiyar cukuikuye kanta da ya yi a cikin burgujejen hijabin da ta zunbula.
Umma Furera ta zaburo da gudu za ta kwace ta sai ta ga alamunsa ya na niyyar zanbada ma ta, idan ta kuskure ta qaraso inda yake.
Sai ta daka tsalle gefe ta na kwakwazo ta na cewa
"Malam me ta yi maka? Kar ka kashe ta fa."
Malam ya daki Sajida har ya gaji liqis yayin da ya tabbatar ya farfasa ma ta baya, sannan ya rabu da ita.
Tun muryar Sajida na fitowa ta na ihu har sai da ta dishashe kamar mai mura. Ta fadi a q qasa ta yi shame-shame ta na nishi mai hade da kuka.
Yahuza kuwa tuni ya arta waje da gudu a tunaninsa dukan kan mai uwa da wabi ake yi duk wanda aka samu zaa daka.
Malam ya dubi Umma Furera ya juya ya dubi Sajida ya ce "Wannan somun tabi ne, kadan ku ka gani. Ni da ku mu zuba a cikin gidan nan. Ni da Abdulmajid zan ga wa za ku zaba, idan na jinyata ki ko na tsiyaye miki ido ai kun ga Abdulmajid zai guje ki don daman ba son Allah ya ke yi miki ba.
"Umma Furera ta zabura ta ce,"Wanne rin Abdulmajid kuma? Tsohon zance, yaushe rabon Sajida da maganar wani Abdulmajid? Ai tunda ka kwace wayarta zance ya wuce."
Malam ya daka mata tsawa ya ce "rufe min baki maci amana, ba a gabanki take hawa katanga ta ke karbar aron waya ta na yi wa dan iskan yaron nan
Abdulmajid waya ba. To zamanku ku dukka ya kusa qarewa a gidan nan, don wallahi idan na sake jin wata magana game da Abdulmajid sai na kore ku daga gidana, sai dai ku koma gidan Abdulmajid din."
Ya fice qofar gida a fusace ya na huci.
Umma Furera ta qaraso wajen Sajida a guje, ta tashe ta zaune gami da yaye hijabin da ke jikinta ta wurgar gefe. Ta kwaye rigar don ta ga irin raunin da ya ji mata a bayanta, sai ga shatin bulala sharba-sharba fatar duk ta farfashe ga jini.
Umma Furera ta dau kukan mutuwa ta na cewa
"na shiga uku, wannan wacce irin kiyayya Malam ya ke yi wa Abdulmajid haka ne. Akan Abdulmajid ya na qoqarin ya kashe 'yarsa ta cikinsa. Wannan wanne munafukin ne ya ke bibiyarmu, duk abin da mu ka yi akan idonsa ya kwashe ya fadawa Malam?"
Cikin sheshsheqar kuka Sajida ta ce, "na san Yahuza ne, gashi nan ya ruga da gudu daga gani an fara dukana."
Umma Furera ta ce, wallahi kuwa shi ne zai fada masa. Idan ba shi ba to waye a cikin gidan nan? Lallai yau Yahuza sai ya yabawa aya zaqinta, sai ya gwammace bai barka ni ya fito daga cikin cikina ba, domin ni ba zan haifi dan da zai jawo a tozarta ni a duniya ba.
Tozartawa mana idan muka sake Malam ya kore mu daga gidan nan, sai dai mu koma ruga mu yi tallar nono mu da muka saba zama a burni. Mu sha lafiyayyan kunu, ga dan wake har da albasa da salad, tuwan masara da na dawa sai wanda muka zaba. A sati mu ci shinkafa sau biyu. Naira biyar dinka ta isa ka sha pure water mai sanyi. A ruga a ina za mu ga firji?"
Wani qululun bakin ciki ne ya tokare wuyan Sajida game da maganganun mahaifiyarta.
Ta fada a fusace
"Umma ke ta ruwan sanyi da shinkafa kike, ni ta Abdulmajid nake. Yanzu duk motsin da na yi tare da Abdulmajid sai an fadawa Baba ya dake ni. Ba ni da wata hanya da zan ji muryar Abdulmajid kuma a rayuwata bayan haramta min ganinsa da aka yi kwata-kwata. Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai Baba ya kore mu ai gara mu koma rugar kin ga Abdulmajid zai dinga zuwa ya na ganina, idan aka daura mana aure sai in tafi da ku gidana shi kenan mu rabu da Baba."
Umma Furera ta daka tsalle ta dafe kirji da hannu biyu ta zazzare ido ta ce, "rufa ni ki saya ni 'yar nan, kar ki min sakiyar da babu ruwa. Yaushe za a yi wannan danyen aikin da ni? Ai kuwa in ba ki rabu da Abdulmajid ba za mu raba hanya. Yaron mayaudari. Aka ce miki aurenki zai yi? Ai ni tunda na rabu da ruga fulani insha Allah ko gawata anan birni za a bunne ni. Wannan wasiya ce na bar miki. Haka idan Malam ya shigo zan bar ma sa wannan wasiyyar. Kuma zan shiga maqwabtan idan Malam baya nan, sai na ja kunnen Iyayye da take miqo miki aron waya in kada ta sake baki. Ahirr dinta kar in ji kar in gani. Ko Abdulmajid din ne ya bugo ya ce a baki ta ce
mahaifinki ya hana ku yi magana. Ke in ki na da zuciya ma har za ki tsaya ki na shan duka akan dan iskan nan Abdulmajid, yaron da ya ke shigowa har zaure ya na zagin mu ya na kiranmu mutsiyata. Idan da gaske yake son naki ba lalata yake nema ba, ai ko boye zai ringa ambulo miki kudi, amma ni dai ko sisinsa ban taba ci ba sai alewa cakulet mai zaqi da askirim babu abin da su ke qara min illa su sagar min da hakora. Ni ba atamfa ko leshi yake aiko min ba. Idan ya yi tafiya ne yake ciko leda da riga da skirt da wanduna ya ce ga nawa ga naki. Dan iskanci ya dube ni ya aiko min da jeans da T-shirt. Har da suyo tafka-tafka wanduna wato daidai jikina in tsuke in fita qofar gida cikin almajirai mu yi wakar Micheal Jackson kenan, ko mu yi rawar nanaye."
Sajida ta fusata ta miqe da sauri ta na buga qafa, ta shiga cikin daki ta na cewa "To wallahi tunda takura min za'a yi, cikin dare zan hada kayana a neme ni a rasa tunda abin haka ne."
Umma Furera ma ta na ta babbamin fadanta a gindin murhu inda ta kunna itace ta dora ruwan zafi cikin qatuwar tukunya don gasawa Sajida jikinta don duk ya farfashe.
Bayan Umma Furera ta gamawa Sajida gashin baya da tsumma da ruwan dumi, ta umarci Sajida ta daure ta shiga bandaki ta yi wanka da zazzafan ruwa, saboda ciwon jiki. Bayan Sajida fito daga wanka suka dasa kujerar zama su na jiran shigowar Yahuza, domin su dauki fansa akan masifar da ya jawo mu su a sanadiyyar gulma, munafunci da tsegumi dukka ya iya.
Shiru-shiru Yahuza bai shigo gidan ba, dare ya fara nutsawa, goma tayi har Malam ya shigo ya shiga daki ya kwanta babu Yahuza, babu dalilinsa. Daga nan su ka gasgata zargin da suke yi wa Yahuza cewar shi ya aikata, don haka ya qi dawowa. Ba su damu su dauki gyalensu su fita nemansa ba, haka ba su damu su fadawa Malam cewar har yanzu Yahuza bai shigo gida ba. Daman ya saba idan ya ga dama ya kwana a qofar gida cikin almajirai. Idan ya so ya kwana da almajiran zaure, haka idan ya so ya shigo cikin dakinsa ya kwana. Daman ba rufe gida ake yi ba qofar daki ake sakayawa. Don haka Yahuza bai dawo ba su ka gaji da jira sai suka yankewa kansu shawara su tafi su kwanta.Allah ya kai su gobe ai dole zai shigo da safe daukar kayan makaranta a dakinsa, to anan sai su yi caraf su damke shi. Umma Furera ta shiga dakinta, Sajida ma ta shiga na ta akurkin. Kowa ya jawo bushashshen katakon da aka laqabawa da suna qofa ya rufc. Sabanin Umma Furera Wacce tana shiga daki minti biyar ya yi yawa ka fara jin jiniyar munsharinta na tashi, amma Sajida fiye da awa biyar bacci ya yi wa idanuwanta yajin aiki. Juyi take akan 'yar kațifarta yaloluwa irin ta 'yan makaranta, ta kasa bacci saboda tsananin takaici da tashin hankali. Sai a lokacin ne ma ta yi kukan dukan da aka yi mata, don dazu azaba ta hana ta kuka. Sheshsheqa take tana ajiyar zuciya, fadi take bayyane.
"Wayyo Majid dina."
Kaico! Soyayya gamon jini, ko shi Abdulmaji din da ake yi dominsa a wanne hali yake a daidai wannan lokaci? Ohoooooo!!! Asubah ta gari SajiMajid.
Chapter 17 · 0% Book details