Sashe 32
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Bakura ya yi ajiyar zuciya, ya ce "ta fadi gulmar da Zahra ta yi mata, har ta kai su ga batawa?"
Malam ya ce, "Abin da na fahimta, zancen nan ne dai da Sajida ke aron waya a makwabta ta buga masa, wanda Zahra ta fada maka, kai kuma ka fada min, ni kuma na dake ta.shine take ganin babu wanda ya san ta ari waya sai Zahra ta zargin ta yi mata gulma."
Bakura ya ji tausayin Zahra ya kama shi, ya jawo an fasa mata kai a banza, ba tare da hakkinta ba.
Malam ne ya katse dogon tunanin da Bakura ya tsunduma ya ce, "Bakura, zan je in sallami Sama'ila kamar yadda ka shawarce ni, kuma zan yi tunani zuwa kwana biyu idan na rasa mafita, zan sake kirawo Sama'ila in fada masa bukatata. Amma duk shawarwarin da zan je in yi, da wacce za ka yi akan wannan magana ba zai kai wacce nake kwatantowa a raina ba. Bakura KAI KA FI CANCANTA ka samarwa Sajida miji."
Wata hanta ce ta yi girgiza daga cikin cikin Bakura, ya fada cikin wata gigitácciyar murya mai kama da rawar nanaye, dan dimauta ya ce, "Na'am, na'am."
Malam ya nanata ya ce, "Babu abin da hankalina ya fi kwantawa illa in aurar da ita, kuma KAI KA FI CANCANTA ka taya ni zabar mata miji saboda illiminka, na yarda da tarbiyar gidanka, da tsananin tsaron gidanka. Ka yi tunani ka samo måna mafita, nima zan je in yi tunani."
Malam ya kashe waya ya bar Bakura nanike da waya a kunne, tamkar gunki. Ya kasa ajiye hannunsa qasa, don kidimewa da tsananin tashin hankali. Babu abin da yake masa yawo a cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa, sai kalmar Malam KAI KA FI CANCANTA ka aurar da Sajida! KAI KA FI CANCANTA ka samo mata miji!"
"Cafdi jam! Abun da kamar wuya." In ji Bakura.
Bakura ya ji a ransa shi ya fi CANCANTA ya auri Sajida amma rana quna, inuwa quna, shi da wanne ido zai kalli Samira ya ce zai auro Sajida? Irin wannan falli da ta fara tayarwa tun kafin ta gano gaskiyar magana? Ko kuwa da wanne ido zai dubi 'yarsa Zahra ya ce zai auro yarinyar da ta so ta nakasta ta? Da wanne ido zai dubi Sajida ya ce ya zo
neman aurenta, shi da ta furta masa da bakinta ta tsane shi? A wacce hujja yana ji yana gani zai je ya jajobo fitsarartiyar yarinyar da ba ta jin maganar kowa, sai ta saurayinta? Ko da wanne ido zai dube ta ya ce ta rabu da rabin ranta ta zo su zauna? Sannan da wanne ido zai dubi Malam ya qi share masa hawayen da yake zuba saboda ya rasa yadda zai yi da 'yarsa a matsayinsa na Malaminsa tamkar mahaifinsa ya dauke shi? Daga qarshe kuma Bakura yake tambayar zuciyarsa wanne tsautsayin ne zai sa yana ji yana gani ya rabu da mai kama da Zuhuriyyarsa sak bayan duk sanda yake son farin ciki a rayuwarsa to sai ya hasko rayuwarsa da Zuhuriyya. Sai ya hasko kamanninta zuciyarsa, sannan yake jin sanyi a ransa. A yanzu haka fuskar Sajida, muryarta da siffar jikinta ce ta maye kamannin Zuhuriyyarsa.
"Ya ya zan yi?" Bakura ya tambayi zuciyarsa.