Sashe 41
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce, "Sai mu zubar da a daji kawai. Ijiyayye ma kwakwalwar irin ta tsofaftin ce ba turanci, don haka su dukka sun yi turus suna kallon su Sajida, ba su san abinda ake shirin aikata musu ba. Abdulmajid ya girgiza kai. ya ce, "Ba zai yiwu ba baby, ki tafi kawai gidan mijinki, amma ki dinga bin duk wani abu da zan gindaya miki. Daddy na yana gari ya kira ni ya yi min fada cewar ya sami labarinki, don haka kada in sake in hana ki zaman aure. Idan ya ji mun gudu zai hukunta ni, koma ya kore ni daga gidansa. Mutum ne mai zafi, ga shi dan ka'ida , zai iya bi na da bindiga ya ce zai harbe ni." Sajida ta rushe da kuka ta ce, "ni fa ba zan sauka daga motar nan ba, bin ka zan yi, daman mutane suna cewa ba ka sona, ba ka damu da ni ba." Abdul majid ya yi ajiyar zuciya a bayyane ya tsuke fuska, yayin da ya fara magana cikin wata kakkausar murya mai nuni da bayar da umarni. Ya ce "Ki kula da abun da nake fada miki, kuma ki bi duk abun da nake fada miki. Ba zan gudu da ke ba, kuma ba za ki qi zuwa gidan mijinki ba, sai dai kada ki yarda wani abu ya shiga tsakaninku. Nan da wani dan lokaci idan na gama shirya abinda nake shiryawa zan san yadda zan fito da ke mu gudu a rasa mu. Kinaji na ko?" Sajida ta amsa cike da ladabi da tsananin tsoro. Ya ce, "Ki goge hawayenki ki daina kuka, ki dauka tamkar na kai ki ajiya ne nan da wani loakci zan zo in dau ajiyata." Su duka suka yi murmushi, Sajida ta goge hawayenta ta ci gaba da kallon abin kaunarta Sajimajid tana sauraron dadadan kalamansa. Daya daga cikin tsofaffin nan ce ta zuro da kanta tsakiyar Sajida da Abdul majid ta ce "Daman kin san dircban nan ne ku ke hira? Na ga alamar ma Buzu ne, don na ji kuna yaren Buzaye, daman kin iya yaren? Wacce irin hira ku ke yi idan kika yi kuka sai ki yi dariya kuma?" Haushi ya rufe Sajida da Abdul majid, har suka rasa abun da za su ce mata. iyayye ce ta ba ta amsa. Ta ce, "Iya, dan Allah ki gyara zamanki, ina ruwanki da hirarsu." Tsohuwa ta koma ta zauna. Ta ce "A'a, 'yar nan kar ki ga laifina, dole in tambaya, don in sani. Na sani ko wannan dan iskan ne Abdul majid da take so ya aiko Buzu ya sace ta." Daya tsohuwar ta ce, "Ai kuwa da mun cî ubansu, don idona idon Abdul majid sai na sharara masa mari, saboda wahalar damu da yake yi. Gaba daya ya hargitsawa yarinya lissafi, ya hanata zama lafiya, ga gidan arziki da wadata ta samu, amma ta qi kwantar da hankalinta. Ai shi ma Abdul majid din ko hauka yake ba zai fara tako qafarsa qofar gidanmu ba, ko ya turo a saçe ta ba." Sajida ta juyo ta dube su, duba na takaici da bacin rai sai ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe. Abdul majid kuwa mudubi ya seta baya yana kallon tsohuwar da take niyyar kwashe shi da mari, sai ya yi murmushi kawai. iyayye kuwa kunshe baki ta yi da gyalenta tana ta dariya a ciki-ciki. Daidai lokacin ne motocin da suke gaban su Abdul majid suka saka siginal din shiga wani katafaren gida. Nan da nan masu gadi suka wangale get a jere a layi motocin daukar amarya suka dinga kutsa kai su na shiga. Abdul majid ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa, sai idanuwansa ne kawai a fili, ya wangale idanuwan nan nasa kwala-kwala yana duban farfajiyar gidan. Ya gasgata, ya tabbatar Bakura ba sa'an yinsa ba ne ya cara masa wajen naira, sai dai su goga da babansa, koma Bakura ya fi Babansa kudi. Kalmar da yake ta fada kenan. "Wonderfiul, fantastic, beatiful. " Wata tsoka ce daga cikin qirjin Sajida ta yanke ta yi wani qarai, yayin da kuka ya tunkarowa kwayar idanuwanta. Ta dubi Abdulmajid ta fada cikin harshen turanci. "Ka kawo ni gidan wanda ba na kauna a rayuwata ka ajiye ni za ka tafi ka bar ni ko?" Ya cije baki ba tare da ya ba ta amsa ba. Ta sake cewa "in har kana sona ba za ka so in zauna da wani kato a gida daya ba da sunan mijina. Mai zai hana ka tunkari hatsari, wuya da duk wani wulakancin da za a yi mana kamar yadda na yarda zan gudu koda za a kashe ni." Ya sami waje ya tsaya ya zare mata jajayen idanuwansa da suka cika da hawaye ya ce, "Fita ki shiga gidan nan kafin wadanda suka sanni su zo su gane ni. Zan bawa iyayye sabon layi da wayar da na siya miki zata kawo miki, za mu dinga magana. Na fada miki ki daina kuka, kuma ina tare da ke a duk inda ki ke." Kaico! Soyayya gamon jini, sai Abdulmajid ya fashe da kuka . Cikin shashshekar kuka Sajida ta bude kofa da sauri ta fice tamkar ranta zai fice. iyayye da tsofaffi suka fita suma suka bi bayan Sajida. Duk wanda yake qoqarin ya riqe ta sai ta fusge. Babu yadda ba a yi ba akan ta sa mayafi ta rufe fuskarta amma ta qi, haka ta shiga gidan mayafinta a kafada, dauri a gaban goshi wato ture ka ga tsiya, ga wani kodadden idon da ya sha koke-koke. A babban falo suka iske Samira da 'yan uwanta da makwabta jingim suna jiran isowar amarya. Bayan 'yan uwan Sajida sun yi sallama, su Samira suka amsa musu, sai tsofaffi biyu 'yan uwan Sajida suka shiga tsakiyar Sajida suka kaita gaban Samira suka durkusar, sannan kowa ya sami waje ya zauna. Bayan an gaggaisa aka fara bayani, dangin Sajida ne su ka ce. "To uwargida, ga Sajida mun kawo miki ku zauna lafiya qanwarki ce, koma mu ce 'yarki ce ki gyara mata, idan ta yi kuskure. Ke kuma Sajida yi na yi, bari na bari, ke ce qarama." Samira na murmushin qarfin hali, dan ba qaramin yaqi ta yi ba da ta danne kishinta ta zauna tana sauraron wadannan bayanai. Sajida kuwa idonta tsai akan Samira da tawagarta bayan kallon banza ma har da harara take harba musu daya bayan daya. Can idonta ya hasko mata Zahra a zaune a lungu, nan fa ta kafa mata ido tana harara sama da qasa har da girgiza kai wato 'ada kai kawai na fasa miki, yanzu kuma sai na ragargaza kan dukka'. Zahra ta yi sauri ta sunkuyar da kai qasa, yayin da jikinta ya dau rawa, a halin yanzu tafi tsoron Sajida a kan mutuwarta. Haka Hajja Farida ta riqe baki tana kallon Sajida tana gyada kai, tana jinjina fitsarar Sajida. Ta tabbatar yarinyar nan ba ta shigo da niyyar zaman lafiya ba. Haka suka dinga kallon-kallo tsakanin Samira da tawagarta da 'yan uwan Sajida. Tun kafin a gama bayani Sajida ta yi zumbur ta mike tsaye ta yi kiri-kiri da ido tana duban jama'ar, ma'ana idan za ku daina bata yawun bakin ku gara ku daina, don ni babu zaman lafiya a tare da ni. Manufarta kenan duk da ba ta furta ba. Ba shiri 'yan kawo amarya suka miqe suka saka ta a tsakiya aka ja ta zuwa dakinta, tun kafin ta bude baki ta fadi wata magana da za ta kunyata su. Sajida na tafiya ta na girgiza tana tabe baki. "Lallai wannan falalliyar 'yar za a yi da ita." ln ji Hajiya Zuwaira. Daya daga cikin yayyun Samira. Samira ta koma ta jingina da jikin kujera jikinta a sanyaye, sai gyada kai take tana al'ajabin yadda Bakura yana ji yana gani ya dauko wannan halittar ya kawo musu gida. Hajja Farida ta dau dogon salati ta salallame ta ce, "Tun da nake a doron kasa shekaruna arba'in har da doriya, ban taba ganin fitsararriyar amarya irin Sajida ba." Nan dai kowacce mace ta fara tofa albarkacin bakinta, tana zayyano abun al'ajabin da idanuwansu suka hango game da Sajida. Daga karshe suka bawa Samira hakuri da nasihar ta ci gaba da hakuri komai nisan jifa qasa zai fado. Ta ci gaba da yi wa mijinta biyayya ta zuba musu ido ta yi kallon yadda za ta qarqe musu, wato tsakanin ango da amarya. Daga karshe dangin Samira suka kaiwa dangin amarya abinci kala-kala, abun sha da snacks da aka yi musu, sannan kowacce ta kama gabanta. Sajida ta yi mamaki matuqa yadda Bakura ya kashe kudi ya gyara mata daki, ba tare da sisin yayenta ba. Ta yi matukar mamakin inda Bakura ya santa har ya kamu da sonta haka. Wasu abubuwan ma daga ita har yan uwanta ba su san shi ba, na turai ne, Musamman da suka shiga cikin bandakuna sun hadu an zuba kayan Kamshi da na decoration. Aka yi shawara a bar qawayen amarya guda hudu da tsohuwa daya su kwana da ita ko Allah zai sa hankalinta zai dan kwanta. Haka kuwa aka yi kafin sha biyun dare gaba daya 'yan rakiyar amarya da masu karbar amarya sun watse. Kawayen amarya ne guda hudu da tsohuwa daya suka rage a dakin Sajida. Samira da 'ya'yanta ne jugum a zaune a falo har Bakura ya shigo gidan ba su iya tashi sun je sun kwanta ba, abun duniya ya ishe su kasancewar Bakura ya san abinda zai tarar don haka bai bari ko da daya daga abokansa ya rako shi ba. Haka ya shigo hannunsa ziqai bai siyo kazar amarci ba irin ta al'ada. To duk abinda zai suyo na marmari akwai shi jingim a gidansa, masu aiki ma ya ishe su, balle iyalansa. Kaza ce, juices, fruits, duk su na nan a shaqe a firij. Ya yi sallama ya shigo falon, gami da murda mukulli ya kulle kofar. Su duka suka amsa masa a sanyaye. Ya dube su ya yi murmushi ya ce, "Yara ba ku yi barci ba, har yanzu? Gobe fa Monday. Yau ba a cewa Abba oyoyo ne?" Abubakar ya taso ya miqawa mahaifinsa hannu suka tafa, haka Umar da