Sashe 60
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai ya ce "Kwarai kuwa qannena ne uwa daya, uba daya. Kamar yadda na tashi cikin wahala suma haka suka tashi cikin wahala da garari." Zahra ta ce "Su ba a sami mai karbar su ba?". Bakura ya yi murmushi ya ce "Babu wanda ya karbe su a wajen mahaifiyarmu suka girma sai dana girma ne na je na tallafa musu na sa su a makaranta nake yi musu aiken kudi a koda yaushe." Usman dan auta ya ce "Abba, mamarka ta gane ka kuwa, ba ta manta ka ba tunda ka girma?" Gaba daya aka kwashe da dariya. Bakura ya co, "Very good Usman, ashe kana fahimtar labarina Mamana ba ta manta ni ba, tana ganina ta shaida ni ta yi ta murna. Ashe bayan tafiyata ta yi ta zuwa gidan hakimi neman danta, kuka da ihu kullum. Aka yi a lallabata da kyar aka samu sauqin abun aka ce za aje dauko ni. Amma da ta sami wani cikin ta haifi kanina Babagana sai ta daina damuwa da ni. Innono ta san ma Zuhuriya ba za ta bar ni acan ba, nima ba zan yarda in zauna ba, dan haka ma ba ta fara cewa a bar ni ba, muka dingumo muka dawo Cinkilawa." Samira ta ce "A iya sanina Mama Fatukamba bata jin yaren Hausa sai Barbarci. Da wanne yare ku ke magana kai da sauran 'yan uwanka saboda na ga a qasar Hausa ka girma?" Bakura ya yi murmushi ya ce "Hausa ai a Cinkilawa na koya, kin manta ba na jin Hausa sai Barbarci sanda Zuhuriya ta dauko ni, kun manta Zuhuriya babarbariya ce ta wajen uwa da uba. Mahaifinta dan Mangono ne, mahaifiyarta kuma 'yar asalin Gashuwa ce aure ya kawo ta qasar Kano. Dan haka Barbarci muke a gidan, a wajen yara na koyi Hausa. Mun dawo Cinkilawa ba dadewa hutuna ya qare, Zuhuriya ta harhada ta ba ni duk abun da nake bukata, motar qaramar hukumarmu ta kwashe mu zuwa makaranta. Duk garin babu mai taimaka min da sisinsa sai Zuhuriya, babu mai agaza mata ita kuma. Ta yi min alkawari idan ribar alalarta ta taru za ta yi min aike makaranta. Ina son a yi hutu, saboda in ga Zuhuriya, amma na fi sakewa a makaranta fiye da a gida. Ni da Zuhuriya a rabe muke, saboda fada ko gore-goren da ake yi min. A haka a daddafe har na kai aji uku na gama qaramar sakandire. A hutun da zan tafi aji hudu wato babbar sakandire (SS1) a hutun Zuhuriya ta yi aure kuma, ta auri wani mutum a garin Yan lanya mai suna Malam Yahuza. Matansa biyu Aya da Umaima, bai taba haihuwa ba. An sha surutu a wannan auren jama'a suka yi ta ce masa kada ya auri Zuhuriya, ita ma ba mai haihuwa ba ce, ita kuma a ce kada ta aure shi matansa kashe kishiya suke. Daya an yi mata shaidar maita, daya an ce 'yar tsibbu ce bokaye take bi. Sun hada kai su biyu duk wacce ya aura sai sun kore ta ko su haukata ta. Hankalina ya tashi kafin a yi auren na kira Zuhuriya gefe ina kuka na ce ko za ta hakura da auren. Ta yi murmushi ta shafa kaina ta ce "Allah yana tare da mu Bakura ba komai. Ni ma bana son auren nan, na gaji da aure-auren nan Innono ce ba za ta kyale ni ba in zauna lafiya ba." Na yi mata addu'a Allah ya sanya alkhairi.Tun sanda aka kai amarya kauyen Yan lanya na ga yanayin gidan dan tsurkuki, zana ce da qasa zalla ga qanqanta, na tabbatar Zuhuriya ta ci baya ba ta taba aure a quntace irin wannan ba. Na haska na hasko ban ga daki ko zauren da zan yasar da filona in kwanta hakarkarina ba. Na shiga zulumin yadda rayuwa za ta kasance min. Na san muddin Zuhuriya ba ta Cinkilawa zamana a Cinkilawa ya qare, dan Innono ba za ta bar ni ba. Haka na dinga safara tsakanin Yan lanya da Cinkilawa. In kwana a Cinkilawa a dakin Zuhuriya gari na wayewa in niqi gari in tafi garin Yan lanya wajen Ummata Zuhuriya ta ba ni abincin safe, rana na dare. Idan Magaruba ta yi in dawo Cinkilawa in kwanta. Har hutu ya qare na koma makaranta na shiga S.S.1. Na fara girma na fara hankali, don a lokacin shekaruna goma sha hudu zuwa goma sha biyar, dan haka na fara tunanin yadda zan canza rayuwata, ba tare da na sake jawowa Zuhuriya matsala a aurenta ba. Don na fahimci kishiyoyinta sun fara harare-harare su na yi mata habaici akan tuwan da take ba ni. Na yankewa kaina hukuncin ko an yi hutu in yi zamana a Wudil ina dako ina cin abinci, har a dawo makaranta. Haka kuwa aka yi da aka yi hutu na ki tafiya har da guduwa na labe dan kada 'yan garinmu su ganni, sai dai na bawa wani abokina dan kusa da garinmu sallahu wajen Mamana Zuhuriya na ce ya ce mata ina makaranta lafiyata qalau ba zan zo huta ba, saboda ina zana jarrabawa. Haka ya je ya shaida mata jikinta ya yi sanyi ya ce min sai hawaye take tana tambayarsa me yasa su ba su zauna sun zana jarrabawar ba sai Bakuranta shi kadai tunda shima ta san ajinmu daya? Duk da ba ta da ilimi, amma tana da kaifin basira." Umar ya ce "Abba, kai kadai kake kwana a dakin dalibai (hostel)?" Bakura ya girgiza kai ya ce "Daf da Magaruba wani Malami ya ritsani a lungun da na maqale ya jawo kunnena har gidan principal. Kamar yadda na shaida muku tun farkon zuwana makaranta principal dinmu ya san ni, kuma yana sona koda yaushe yana yaba qoqarina yana bada misalai da ni a wajen assembly, dan haka yana ganina ya ce da malamin ya sakar min kunne. Bakura yana da hankali akwai dalilin da yasa ya gudu ya buya bai tafi gida ba." Bayan malamin ya tafi ya zaunar da ni a gabansa yasa matarsa mai suna Asiya ta zubo min abinci na ci na qoshi dan ya ga alamar yunwa da wahala a jikina, Na ci abinci na qoshi, ya fara yi min nasiha hade da dabara gami da lallashi a kan in fadi dalilina na ain tafiya gida. Da farko na 6oye masa daga karshe na zayyana masa tarihin rayuwata tun daga farko har karshe. Na kuma fada masa dalilina na qin komawa gida hutu. Abun mamaki sai na ga ya tausaya min matuka kamar zai rusa kuka, ya kira matarsa Asiya ya laburta mata labarin rayuwata ya fada mata dukkan labarin dana ba shi. Mutuniyar kirki ce, sai ita ma ta tausaya min ta ba shi shawarar to ya bar ni in dinga yin hutun a nan wajen su mana. Malam Abbas Shagari ya ce 'A'a sai na je garin ko na aika an tabbatar min haka ne, sannan zan bar shi ya zauna. " Da ya aika aka tabbatar masa haka ne sai ya qyale ni na zauna a gidansa, kamar yadda na ce masa zan dinga dako ina cin abinci sai ya hana ni yin dako, ya dinga ciyar da ni a kyauta. A lokacin yana da yara guda uku babban Abdul Wahab, sai mace Amina da wani dan jariri da ake goyo shi ma Abdul sunansa. Na ji dadin zama a gidan Malam Abbas Shagari saboda shi da matarsa su na da kirki su na kula da ni kamar dansu. Kamar yadda na ji dadin zama da su su ma sun ji dadin zama da ni, saboda ba na gajiyawa wajen aikace-aikacen gida kamar mace, babu abin da ban iya ba. Shara, wanke-wanke, wanki, aike, noma Koyawa yara karatu da rainonsu duk ni nake yi wa Aunty Asiya. Kafin hutu ya qare sai ga Zuhuriyya wurjanjan an rakota gidan da nake. Ina ganinta gabana ya fadi, saboda yadda na ga ta rame ta lalace akwai alamar damuwa da wahala a tattare da ita. Na riqe ta ina tambayarta ko lafiya? Ta rushe da kuka ta ce "yanzu Bakura ni ka ke guda, an yi hutu kowacce uwa ta ga danta ni ban ganka ba, wacce irin jarrabawa ce a cikin hutu? Ba na barci ko da yaushe ina leken hanya, idan na ji maganar wani sai in fito da gudu daga daki in zaci kai ne." Na ba ta hakuri, sannan na shiga da ita cikin gida na shaidawa Malam da matarsa ga mahaifiyata. Bayan ta zauna sun gaisa ta ci abinci, sai ta fara kuka tana shaidawa Malam irin halin da ta shiga na damuwa da fargabar akan rashin ganina. Malam ya yi mata bayanin dalilan da na shaida masa. Sai ta sake shiga damuwa ta ce ba ta taba tunanin har akwai gidan da Zaa ce ita kadai zata zauna baa yarda Bakura ya zauna ba kuma ta ci gaba da zama a gidan ba, dan haka in har tana gidan dole Bakura ya zauna tare da ita. Kasancewar ta tubure ba za ta bar ni ba Malam ya ce in shirya in bi ta mu tafi. Da yake yamma ta yi ya shawarce ta ta kwana gobe sai mu tafi, ta ce maigidanta ya ce lallai-lallai ta koma a ranar, dan haka a lokacin na hada 'yan kayana na bi ta duk da hutun ya kusa qarewa. Kamar yadda na fada muku ba daki a gidan, Zuhuriya sai haya ta kama min daki daya a makwabtansu na zauna duk da surutun akan abincin da ake ba ni kishiyoyin suke yi mata. Na lura cewar su na takura mata tashin hankali da masifa kullum. Wannan ta yi mata yau, gobe wancan ta yi mata. Duk da irin haqurin da nayi ta yi na cije ban je na rama mata ba. Wata rana kasa daurewa na yi, na shigar mata fadan. Domin sun tarar mata su biyu za su yi mata duka har sun kaita qasa, na zo na tade qafar daya ta fadi qasa, dayar kuwa angaje ta na yi ta fadi gefe. Na tashe ta tsaye na karkade mata jikinta. Da maigidan ya zo suka shaida masa karya da gaskiya sai ya kore mu ni da Zuhuriya, amma bai sake ta