Sashe 31
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yi zumbur ya tashi zaune, ya rike kai yana Jujjuyawa saboda al'amura sun tsananta a gare shi. Ya rasa abun da yake yi masa dadi. Wayarsa ce ta dau ruri yana dubawa sai ya ga sunan Malam Yakubu, wato mahaifin Sajida. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, ya danna wayar da sauri gami da rada sallama. Sai ya ji muryar Malam na karkarwa, alamar yana cikin tashin hankali. Bakura ya tambaya cikin kidiméwa. "Malam lafiya?" Malam ya nisa ya ce, "Kamar yadda ka ba ni shawara in bi abun a hankali, na bi shawararka, na kira Sajida da Iyayye na tambaye su na ji duk yadda aka yi. Ka ji ashe da Abdul Majid suka fita, shi ne ya kai su Super Market siyayya. Uwarta na gida, ta amince musu suka fita dan haka na yanke hukunci akan Sajida. Ba duka, ba zagi, amma ba za ta wuce sati biyu a gidana ba zan daura mata aure ga duk wanda na ga dama, mahaifiyarta kuma dole ta fice ta bar min gidana." Bakura ya miqe tsaye, gami da dafe kirji ya ce,"Baba kada ka yi min haka. Ina fatan dai yanzu baka furta saki ba?" Malam ya matse hawaye ya ce"Ban sake ta ba, amma gara ta tafi gidansu can rigarsu ta huta, nima in huta, ta ga ko ina da amfani. Bakura ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka yi hakuri ka bar ta, kada ta tafi, kai namiji ne kada ka hada tunanin ka da na mace, ba ka ganin ko da ta hana Sajida fita sai ta fice din tunda bata tsoron kowa, yara ba su cika jin tsoron iyayensu mata ba. Musamman Sajida yadda take son Abdul Majid ba ta jin maganar kowa sai tasa, tana shakkarka shi yasa ba ta fita idan kana nan. Babu yadda Umma Furera za ta yi da ita ne shi yasa ta bar su suka fita, amma ka yi hakuri Malam. Zancen aure kuma nan da sati biyu ba zai yiwu ace Sajida ta yarda ta auri wanda ba ta sanı ba, wanda ba ta so, kuma ka ce a zauna lafiya. Ka bari a tsanake ka na addu'a sai ta dawo kan hanya ko Allah Ya shiryi Abdul majid din su yi aure, ko Allah ya yaye mata sonsa, ta sami wani nagari ta aura." Malam ya ji tamkar Bakura ya watsa masa wuta a zuciya, ya yi farat ya ce, "Wallahi idan kaga Sajida ta auri Abdul majid a duniya, sai dai in ba na numfashi, amma idan ka ga na ci gaba da zama da Sajida a cikin gidana fiye da sati biyun nan to duk mazajen duniya sun guje ta, amma idan da namijin da zan bawa ya karba, to na aurar da Sajida na gama duk talaucinsa, duk naqasarsa, kuturu ko makaho. A yanzu haka na aika almajirina Usman ya je kasuwar Dawanau ya kira min Sama'ila, wani almajirana da yake can yana kasuwanci, na ce ya zo ya aure ta na tabbatar ba zai qi ba. Domin Sama'ila yana da hankali, ya na yi min biyayya, duk da matansa biyu, ita sai ta zama ta uku. Kuma in kafe ta da addu'a sai ta zauna a gidan ba za ta iya fitowa ba, balle ta gudu." Hankalin Bakura ya tashi matuqa, duk da sanyin A.C da ke dakin amma zufa yake. Ya ce, "Baba kada ka yi haka amma kashe wayar zan kira ka, saboda kada in cinye maka kati maganar tamu ta na da tsawo." Malam ya kashe waya, Bakura ya koma ya kwanta yana mai tsunani akan wannan matsala. Hakika ya tausayawa Malam, haka yana tausayawa rayuwar Sajida, Ya tuno irin matsananciyar rayuwar da yara matan da ake yiwa auren dole suke shiga, haka duk akasarin karuwai daga auren dole suke fallewa. Ya tuno irin tsananin son da Sajida take yi wa Abdul majid, ya hasko irin barnar da za ta iya afkuwa idan Sajida ta samu ta fice daga gidan mijinta ta gudu wajen dan iskan nan Abdulmajid. Sai ya tuno 'yarsa Zahra, ya kwatanto a ce bayan ransa komai zai iya faruwa da ita. Ya shiga tunanin hanyar da zai bi ya warwarewa Malam da 'yarsa wannan matsalar, ba tare da kowa hankalinsa ya tashi ba. Da ya rintse ido babu abin da ya hango sai fuskar Sajida da tsananin kamar da suka yi da Zuhuriyyarsa, ya ji a ransa ya kamata ya taimakawa rayuwar Sajida ko don albarkacin kamar da ta yi da Zuhuriyya a matsayinsa na mai ilimi, mai dukiya, kuma cikakken Musulmi. "Ina mafita? Ina mafita?" Haka Bakura ya fada a bayyane yana ta nanatawa, tamkar karatu, ko kuma in ce tamkar wani tababbe, sabon kamu. Abdul majid, zai iya yiwuwa ma gama lalata rayuwar yarinyar nan." Ya jawo waya ya bugawa Malam, bugu daya Malam ya amsa ya ce da Bakura. "Ka kira ni anjima, ina tare da Sama'ila an kirawo min shi, zan isar masa da buqata ta, duk yadda muka yi zan sanarmaka." Bakura ya dakatar da Malam da sauri ya ce, "Kada ka yi haka Malam, ka bari mu yi shawara, yin haka zai iya cutar da rayuwar Sajida, ya wargazawa Sama'ila lissafi, ta rugurguza masa tsarin gidansa, ta wargaza kan iyalansa. Malam ka yi min wata alfarma yanzu ka taso daga gabansu Sama'ila ka fito qofar gida mu yi magana." Malam ya ce, "Yanzu haka na bar su a zaure na fito qofar gida." Bakura ya nisa ya ce, "Da za ka bi shawarata kada ka yanke wannan hukuncin, ka kirkiro wani dalili daban ka fadawa Sama'ila na dalilin kiransa, amma ba wannan ba. Tun da a kasuwar Dawanau yake na san awo yake, ka ce masa ina son buhun gero biyu, buhun masara biyu, ya kawo min zan saya, ka sallame shi ya tafi ba tare da ka fada masa ba." Malam ya ce "toh na ji shwararka, amma idan na sallame shi, ya tafi ya bar ni da Sajida ya ya zan yi da ita?" Bakura ya numfasa ya ce, "Sajida ka barta kamar yadda na fada a baya, har Allah Ya sa ta gane Abdul majid ba mai qaunarta ba ne sai kaga ta canja shawara, Allah zai kawo mata wani." Malam ya dakatar da Bakura ya ce "Na rantse Sajida ba za ta wuce sati biyu a gidana ba insha Allah, Bakura ka kasa gane halin tashin hankalin da hatsari da illar da ke tattare da zaman Sajida ba aure.Takai-ta-kawo Sajida ta fara daukar hure kunnen da Abdul majid yake yi mata akan ta daina jin maganar iyayenta ta bi shi su watse daga nan sai ya koya mata shaye-shaye. Ba ka ganin daga tafiyata ta fice, uwarta ma ta ce ba ta san da Abdul majid suka fita ba. Da ta fita kuma ta je ta debo min magana, har da fasawa yarinya kai, ba dan 'yarka ba ce da yanzu ina kulle. Ta jawo mutuncina ya zube a unguwa, ana ganin mota na zuwa ta na daukar 'yata ana fita da ita."Kai kafi cancanta