Sashe 21
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
da Zuhuriyya. Ba dan ta je gidan ba, da tsautsayi bai sa ta bada aron wayarta ba. Da a ina Abdul majid zai sami nummbar wayarta? Hawaye ya dinga surnano mata babu tunanin da bai zo mata ba a rai ba, ta ji kamar ta hada kayanta ta gudu wajen dangin mahaifinta a Maiduguri a neme ta a rasa, saboda ta san yau hukuncin da zai dauka akanta ba kadan ba ne. Muryar mahaifinta da mahaifiyarta ta ji su na fitowa daga dakinsa, Zahra ta zabura ta miqe tsaye gami da goge hawayen da ya yi mata faca-faca a Idanuwanta. Ta yi zuruf tana kokarin shigewa cikin daki da gudu sai ta ji muryar mahaifinta ya kwalla kiran sunanta. Ta waiwayo a firgice cikin rawar murya ta amsa. Ya qaraso kofar falonta a inda take tsaye ya mika mata wayarta. Ba tare da ya sake duban inda take ko ya yi wata magana ba, ya zarce zuwa babban falo. Mahaifiyarta ce ke biye da shi ita ce ta tsaya tana kallon Zahra kallo irin na lafiyarki qalau kuwa? Zahra ta gaishe da mahaifiyarta cikin firgici. Samira ta amsa gami da jero mata tambayoyi har guda uku a jere. "Lafiyarki kalau kuwa? Me ke damunki duk ki a susuce? Me yasa kika kashe wayarki?" Amsar wadannan dogayen tambayoyi su ne, "Ba komai." In ji Zahra. Ba tare da Maman Zahra ta sake cewa komai ba ta jüya ta nufi falo. Zahra ta yi wuf ta afka cikin falonta gami da datse kofar da mukulli, ta dade a jikin kofar a jingine, ta yi ajiyar zuciya mai fitar da tsantsar tashin hankali. Sannan zuciyarta ta tuno mata da addu'ar da ake karantawa idan ka gamu da wata masifa. "Inna lil laahi wa innaa ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fii musiibatii wa aq-likini khairan minhaa." Ta fada ta maimaita ta sake ta maimaita har sau uku, sannan ta ji numfashinta ya fara dira daidai. Ta wuce bandaki domin dauro alwala. Rabon Zahra da ta rasa sallar Asuba har ta manta, amma yau saboda tsananin tashin hankalin da Abdul majid ya jawo mata ya sa ta rasa sallah akan lokaci, sai da gari ya waye tangararai. Sallamar sallarta ke da wuya. sai wayarta ta dau ruri. Ta yi ta maza ta suri wayar gami da dubawa, sai Ta ga lambar Abdulmajid ce, a take ta ji wani takaici da daci a ranta. Ta danna a fusace ba tare da ta ce masa komai ba ta kasa kunne tana sauraronsa. Ya yi ta magana tamkar da itace yake waya. Ya yi gyaran murya ya ce, "Ko ba Zahmajid ba ce, shin kin ga sakonnina na jiya da na yau da safe kuwa ??" da tsurawa aljihun Bakura ido.?JUT