← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 64

Sashe 39

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

RANAR DAURIN AURE
Allah mai yadda Ya so, duk abinda ka ga ya faru da bawa to bawan ya kudira a ransa rubutacce ne daga Rabbul samawati. Babu wanda ya isa ya tsallake kaddarar da Allah ya rubuto masa. Matar wani ba ta auren mijin wata, haka Baban wani baya haifar dan wani.
Ranar Asabar da misalin qarfe goma na safe ne, daurin auren Alh. Bakura da Haj. Sajida. Haka kuwa aka yi, kafin goma ta cika kofar gidan Malam Yakubu ya cika maqil da bil-adama. Dangin Sajida na wajen uwa da uba sun hallara, yaransu da manyansu . Haka dangin Bakura daga Maiduguri na wajen uwa da na uba suma sun hallara kacokan dinsu. Ga uwa-uba abokan Bakura, abokan kasuwancinsa daga garuruwa daban-daban. Tsofaffin abokanansa tun na sakandire suma ba a bar su a baya ba. Don a cikinsu har da masu girma gwamnoni da mataimakansu na jihohi uku, Kano, Maiduguri, dana Yobe. Haka kusan gaba daya dangin Samira sun zo kama daga mahaifinta, yayansa, surukansa da 'yan uwansa suma ba a bar su a baya ba. Saboda su na son Bakura, suna ganin mutuncinsa, saboda ya san mutuncin kowa. Gashi su na jin dadin yadda ya riqe musu 'yarsu hannu bibiyu ita da 'ya'yanta asirinsu a rufe. Don haka da Bakura ya je ya sanarwa mahaifin Samira zai qara aure bai damu ba, sai ya yi masa addu'a gami da yi masa nasihu masu ratsa jiki.
Ya nunawa Bakura hatsarin rashin nuna adalci ga namijin da ya hada mata biyu. Daga karshe ya sa aka turo masa 'yarsa Samira ya yi mata fada sosai, ya ja mata kunne akan kada ta tayar da hankalinta, kuma ta bi mijinta sau da qafa, ta zauna da kishiryarta lafiya.
Ba gidan Malam Yakubu kadai ba, gaba daya layin ya cika. Kowacce kofar gida cunkoson jama'a ce makil. Babu abun da ka fi hangowa sai galla-gallan shaddoji a jikin jama'a dinkin Tazarce da manyan riguna malum-malum. Ga kamshin turararruka yana tashi. Maroka kuwa ba a iya kirga su, masu busa kuwa Suma yi suke saboda masu sarautar da suke wajen. Dakyar ake hango ango, saboda taron jama'ar da yake bi yana ta gaggaisawa da su. Hakika daga ka ga ango za ka gasgata shi ne ango ko ba ka taba ganinsa ba.Saboda ya fi kewa caba ado ya zankada kyau da wani tsadadden yadi fari tas, wanda ya sha surfani a rigar ciki da babbar rigar. Ya dora baqar hula da baqin takalmi tsadaddu.
Masu daukar hoto da bidiyo suka hau aikinsu, duk inda Bakura yasa kafarsa su na biye da shi. Saboda hayaniya da kyar suka tsagaita, misalin karfe goma sha daya da rabi aka daura auren. Waliyan ango suka miqawa waliyan amarya sadaki naira dubu hamsin lakadan. Aka yi sallati ga Shugabanmu Manzon Allah (S.A.W.) aka shafa, sannan kowa ya kama gabansa. Kowa ya shaida Sajida ta zama matar Alh. Bakura, kowa na yi musu fatan alhairi Allah Ya bada zaman lafiya.
Mata ma ba a barsu a baya ba wajen nado 'yan daurin kayansu su ka dungumo gidan biki. Don haka gidansu Sajida da makwabtansu a cike yake da 'yan yinin biki. Sai dahuwar abinci ake kace-kace komai a wadace. Uwar biki Umma Furera kuwa, sai shiga leshina da shaddoji take, kai ka ce ita ce amaryar. Danginta na kauye sai bin ta da kallo suke zuciyarsu cike da sha'awa, dama su ne suka sami irin wannan. Duk wadannan hidindimu da ake yi ina amarya?
Amarya na daka, a dakin ma a bayan qofa, ba wanka balle a cancada ado, duk da tulin leshina, atamfofi super, shaddoji masu tsada kala-kala, materials na zamani bayan gwala-gwalai 'yan kunnaye, sarkoki, zubbuna, da awarwaraye. Amma Sajida ta yi qiirmisisi ta toshe kunnuwanta ta qi sauraron kowa.Juyin duniyar nan da lallashi babu wanda Ummarta da danginta ba su yi mata ba, amma Sajimajid ta kekashe kasa ta ce sai dai a kashe ta, amma ba za ta yi wanka ba. Kawayenta ma ba su ji dadin wannan al'amari ba, sun so Sajida ta ware su karbi kudi a wajen ango su hada hadadden party a cashe, amma Sajida ta ki daukar shawararsu. Haka aka dinga kai kawo ana cashewa, amma biki ba amarya, har da masu kidan kwarya a tsakar gida mata suna ta shan rawa, amma Sajida ko tsakar gida ta qi leqowa. Tana bayan qofa a takure zuciyarta cike da tsantsar takaici, idanuwanta sun jejjeme. Duk ciye-ciyen nan da ake yi tun safe ko kwayar shinkafa Sajida ba ta jefa a bakinta ba, duk da tulin abincin da aka jere mata a gabanta.
La'asar sakaliya Sajida ta yi niyya da kanta ta fito tsakar gida, sanye da wata kodaddiyar doguwar rigarta ja da zurmikeken hijabinta ruwan toka. Fitowar ma ta dole ce, domin fitsari ne ya cika mata mara, ga salloli a kanta Azahar da La'asar. Nan da nan masu daukar hoto da masu daukar bidiyo suka yi ruddugu suna daukarta, ba tare da ta shirya ba. Da kyar Sajida ta samu ta shiga bandaki, saboda jama'ar da suka baibaye burtintinar amarya su na daukar hoto da ita. Shigarta bandaki ke da wuya, kafin ta rufo kofa Umma Furera ta danna kai dauke da ruwa bokiti guda da kwandon soso da sabulu na wanka. Mata uku ne suka shiga bandaki su na yi wa Sajida magiya ta daure ta yi wanka, idan ba ta yi da kanta ba zasu danne ta su yi mata.
Sajida ta cije, ta tubure ta ce ita fa ba za ta yi ba, amma da ta ga da gaske shirin tube ta suke da karfi za su wanke ta, sai ta saduda ta ce su fita za ta yi da kanta. Su ka fito suka bar ta a bisa sharadin idan ba ta yi wankan kirki ba sai sun sake yi mata wani.
Sajida ta fashe da kukan takaici, tana wanka tana kuka babu abun da take tunawa sai Abdul Majid' dinta. Ta yi wanka mai kyau, ta yi brush, ta dauro alwala ta fito ta wuce daki fuskarta a murtike haushin kowa take ji. Bayan ta idar da sallolin da ke kanta, nan ma iyaye da qawayenta suka baibaye ta kowa đauke da kayan kwalliya. Masu taje kai na yi ana mulka mai, masu yanke farce na yi, masu shafa mata mai na yi, masu shafa hoda da jagira na yi. Ta yi ta fizge-fizge tana fadar baqaqen maganganunta da fitsara iri-iri babu wanda ya damu da abin da take fada kowa burinsa amarya ta yi kyau, domin yau da daddare za a kai ta gidan angonta Bakura.
Wani tsalelen leshi ne baqi, wanda aka yi masa ado da fulawa ruwan goro, wanda ya sha dinkin riga da siket matsattse, shi ne aka sakawa Sajida. Yayin da aka dandan bara mata gwal-gwalai a kunne, wuya, yatsu, da awarwarye a hannunta kan ka ce kwabo Sajida ta fito sak amaryarta. Abarka da Kai ka fi cancanta..

Gashinta kuwa mai laushi ne aka gyara aka zubo mata da shi har bayan qeyarta, aka nade mata daurin dankwalin leshin a samansa, sannan aka yafa ma ta mayafin da ya dace da leshin wato mai ruwan goro, takalmi ma kalarsa ne, yayin da aka feshe duk illahirin jikinta da turarurruka masu qamshi na cikin lefe.
Aka ruqo ta zuwa tsakargida aka zaunar da ita akan wata doguwar kujera aka fara daukar hotuna. Babu yadda Sajida za ta yi, domin an ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma zuciyarta cike take da baqin ciki da damuwa. A zaune take tamkar gunki, sai kallon mutane take sasarai kai ka ce ba ta da laka a jikinta. Duk sanda ta tuna ita da Abdul majid shi kenan sun rabu sai ta ji zuciyarta ta harba kamar ana harba bindiga. Idan ta tuno mutumin da aka daura mata aure sai ta ji ta qara tsanarsa.
Ta ce a ranta "Lallai kuwa mutumin nan ya yi kuskuren aurena. Iyayena sun yi kuskuren ba shi aurena, sun yi kuskuren karbar dukiyarsa saboda asara ce. Sai na zame masa tamkar kunama mai cizo a shimfidarsa. Zan zame masa duhu alhali da hasken rana. Sai na disashe farin cikin zuciyarsa, ya koma tsananin baqin ciki da damuwa kamar yadda ya sakani ni da Abdul Majid dina. Sai na fardo wannan kyakkyawar kwaryar tasa da yake ji da ita wacce ya saqale a ragaya, idan ta fado qasa ko ba ta fashe ba, zata yi gagari a tsakar gida. Sai na yaqi uwar gidansa na hana ta sukuni a gidanta. Sai na takurawa duk wani mai rai a gidan in ya so idan ya gaji zai sake ni, ko ya kore ni, sai ya ji ya tsani zama da ni."
Sajida ta yi murmushin mugunta, wanda har wushiryarta ta fito ta girgiza qafa, 'yan biki suka dau shewa hadi da guda a tunaninsu amarya ta saki ranta ta amince da auren.
Chapter 39 · 0% Book details