← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 64

Sashe 44

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Balle karya kumallo, bashi da shirin yin wanka ya fita. Daga dukkan alamu zafin rabuwa da Sajida ya shige shi, don a da yana ganin wasa ne ba auren za ta yi ba yanzu kuwa ya tabbata. Har suka gaisa bai
fahimci ita ce ba, sai da ya ji kalamanta masu ratsa masa jiki, sannan ya farga. Kan ka ce kwabo ya ware murya.
Tambayar da ya fara jero mata ita ce, "Da fatan dai baki yarda wani abu ya hada ku ke da wannan banzan mutumin ba kö? Ina fatan ba kya sakar masa fuska, balle ya yi hira da ke ko?"
Ta amsa masa da, "Shi ya isa ma ya matso kusa da ni. Ai ko kallon inda yake ba na yi."
Ana badakala, haka Sajida da Abdulmajid suka dau lokaci mai tsawo su na waya, har sai da kudin wayarta ya qare, shi ma ya kira kudin wayarsa ya qare. Sai ya turo mata text massage cewar ta yi hakuri idan ya fita waje zai sa kati zai kira ta.
Yau farin ciki a zuciyar Sajida baya faduwa, ta sumbaci wayar ta rungume filo, gami dą lumshe ido tamkar tana tare da Abdul a kusa da ita. Yini guda Sajida na nade a daki, sallah ce ke tashinta daga kan gadonta.
Grace ce take kai kawo tsakanin kicin da dakin Sajida. Samira ba ta gaji ba ta aika aka kai mata abincin rana, da a ka kai na dare aka kwaso kwanukan rana. Ba kunya ba tsoro Allah Sajida take nadar abinci ta koma ta kwanta. Bakura bai shigo gida ba sai bayan sallar Isha'i.Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya zauna a babban falo, tare da 'ya'yansa da uwar gidansa Samira. Ya taya yara Home work, suka yi 'yar hira, sannan ya sallami kowanne yaro ya je ya kwanta. Samira ma ta yi zumbur ta mike, gami da yi masa sallama ta nufi dakinta. Bakura ya yi kiran duniyar nan Samira ta qi dawowa, ta shige dakinta ta rufe. Yana qoqarin kiranta a waya ta murtsike wayar ta kashe. Ya dade a zaune, sannan ya miqe don tafiya dakinsa ya kwanta, domin ya gaji.Daidai qofar dakin Sajida ya jiyo muryar Sajida na hira har da kyalkyala dariya. Hakan ta ja hankalinsa ga tsayawa tsai yana sauraro. Da farko ya dauka talabijin ce, amma da ya kara kunnensa ya tabbatar muryar Sajida ce ya yi mamaki, sai ya shiga tunanin da wa Sajida take hira haka, to ko qawayen nata ba su tafi ba ne? Sai ya yanke hukuncin shiga dakin ya gani. Yana murda kofa, sai qofa ta bude ya ci sa'a a bude take ba an datse ba. Tsuru-tsuru ya ga Sajida ita kadai, ta yi daidai a kan doguwar kujera tana waya. Sanye take da atamfar dazu, amma kanta babu dankwali ta zubo gashinta har baya tana shafawa, Saboda dadin hira. Ya kalle ta, ta kalle shi kallon Kallon ake yi.
Sai yaji ta ce, "Ka gan shi ma ya shigo dakina ya tsaya yana ta muzu-muzu da ido, ka san kallo ne da shi kamar wani baqauye."
Da jin haka sai Bakura ya sami kújera a setinta ya zauna cike da mamaki.
Can ya yi qarfin hali ya tambaya. "Da wa kike waya, Sajida?"
Ta fada cikin gadara ta ce, "Abdulmajid."
Yadda ta ga Bakura ya tunkaro ta a fusace kamar mai shirin mauje ta, sai ta tsorata, ta wurgar da wayar ta qanqame akan kujera.
Bakura ya tsugunna ya dauki wayar a qasa, sai ya ga har yanzu wayar a kunne take Abdulmajid ne ke ta magana. Bakura ya kara wayar a kunnensa yana sauraronsa, kalmar da yaji yana cewa. "Baby, are you there?"
Bakura ya yi gyaran murya, gami da' cewa, Ba baby ba ce, wannan mai gidanta ne."
Abdui majid ya fada cike da gadara, "Alhamdulillahi, daman ina nemanka. Kai wawa ne, banza, jahili, ta yaya za ka auri yarinya bata sonka, saboda kana da kudi? To wallahi ka kuka da kanka.
idan ba ka saki Sajida ba sai na sa an farfarda min
cikinka."
Bakura ya yi murmushin haushi ya gyada kai. Ya ce "Yaro, idan ni da kai zaa hado mutane masu hankali mu zauna akan teburi daya kowa ya bada labarin abin da ya faru, to jama'a za su tantance waye wawa, banza, jahili. Ka san kai ne wawa, tunda ka bari na kwace maka Sajida a cikin dan qanqanin lokaci, alhali kun dade tare har kun shaqu, don da kana da wayo ba za ka bari in kwace ta daga hannunka ba. Idan jama'a suka ji haka zasu tabbatar maka kai banza ne, tunda aka baka dama ka fito ka aure ta ka kasa fitowa ka qi yin amfani da damar da aka ba ka, har sai da ta subuce maka. Sannan daga karshe ko jama'a ba su fada maka ba, kai da kanka ka san kai jahili ne, marar tarbiyyar addini, tunda za ka raba dare kana magana da matar aure, wacce ba matarka ba. Kuma ina jiran ranar da za ka sa a farde min ciki."
Bakura ya katse wayar ya kashe ta gaba daya ya juya ya dubi Sajida wacce tuni ta kufula tana harararsa. Ya koma ya zauna a kan kujerarar da take fuskantarta, ya dube ta. Ya ce "Abdul majid din ne har yanzu ba ku rabu ba, shin idan shi bai san darajar aure ba ke ba ki sani ba? Ina tabbatar miki halaka ce da azabar Ubangiji akan matar auren da take magana da da namiji, wanda ba muharraminta ba. Sajida ba kya jin maganar iyayenki, ba kya jin maganar mijinkı, alhali mu ne masu qaunarki da gaske."
Ta ji tamkar Bakura yana mata yayyafin ruwan zafi a sassan jikinta, domin kalamansa tamkar zaginta yake haka take ji a kanta.
Ta miqe tsaye tana mai sharara kuka, tana zubar da hawaye ta rike kugu tana girgiza ta ce, "Malam ka rufe min baki ka daina shiga rayuwata, na fada maka na sake maimaitawa na tsane ka, kuma ba zan zauna da kai ba. Wannan wayar da ka kwace ita ce ginshiqin zamana a gidanka, amma tunda ka kwace wallahi sai an neme ni an rasa."
Bakura ya ce "Babu inda za ki je Sajida, ina da kyakkyawan tsaro a gidana, wanda ko jikin get ba za ki iya tabawa ba balle ki bude ki fita, kin shigo gidan nan kenan. Yanzu kin zama killatacciyar kwaryar da na rataye a ragaya, don yin ado da ita, kin fita daga sahun kwarya mai garari a tsakar gida."
Daman kalmar da Bakura ya fara fada mata kenan ita ce ta jawo tsanar da ta yi masa tun farko, yanzu ma an kuma.
Ta sharbe hawaye ta ce "Zahra 'yarka ita ce kwarya mai garari a tsakar gida ba ni ba."
Ta juya a fusace ta na rusa kuka kamar ranta zai fita. Kukan Sajida tamkar dafi ne a cikin zuciyarsa, saboda ji yake tamkar Zuhuriyya ce take kuka. Ya ji hankalinsa ya tashi, ya miqe da sauri ya bi bayanta har cikin daki tana danna qofa yana turawa, har ya kutsa kai.
Ta tafi jikin bango ta maqale ta zazzare masa jajayen idanuwanta masu zubar hawaye. Ta ce "Ka fita ka ba ni waje, ba na sonka, ba na son ganinka, na tsane ka na tsani mai sonka gara in kashe kaina da in zauna da kai."
Bakura ya yi tsaye yana dubanta, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi. Ya fada cikin sanyayyiyar murya Ya ce "Me kike so in yi miki a duniya, don ki yi farin ciki?"
Ta ce "Ka bar ni in auri Abdul majid."
Ya yi shiru, can ya ce, "Abdul Majid ba zai aure ki ba, da na bari ya aure ki."
Ta ce "To ka ba ni wayata don sai na ji muryarsa nake jin dadi."
Abin mamaki sai Bakura ya kunna waya da sauri ya danno lambar Abdul majid, bugu daya wayar ta shiga, sai ya miqa mata, gami da cewa, "Ga Abdul majid dinki"
Cike da mamaki, gami da sanyin jiki ta miqa hannu ta karba ta kara a kunnenta, tabbas shi din ne kuwa. Nan da nan ya ga ta fara murmushi. Ta zo ta wuce Bakura a tsaye kamar gunki ta koma falo ta luntsuma akan kujera ta na hirar soyayyarta ba tsoro, balle fargaba.
Bakura ya zo falo ya sami kujera ya zauna, ya tsura mata ido ya na kallo. Hakika dariyar Sajida ita ce farin cikinsa, domin ji yake tamkar dariyar Zuhuriyya ce. Sai ya tsinci kansa ya na murmushi, tamkar Zuhuriyya ce take cikin farin ciki. Ta yi ta waya ita da abin qaunarta har sai da suka gaji, sannan suka yi sallama ta kashe waya. Ta harari Bakura ta tabe baki ta mike tana tafe tana girgiza ta shige daki ta datse ta yi kwanciyarta.
Tsawon awa guda Bakura bai motsa ba, yana zaune kansa ya kulle. Ya kan raşa abinda yake faruwa da shi. Abu na farko, ba wai tsananin son Sajida yake ba, kuma baya sha'awarta, amma yana ji a jikinsa ba zai iya rabuwa da ita ba saboda kamar da ta yi da wacce ya fi so a rayuwarsa. Haka ko kadan bai ji kishin wayar da suke yi da Abdul majid ba. Ya rasa dalilin da yasa baya gajiya da duban surar Sajida da sauraron muryarta ba. Ya kasa gane daliin da yasa baya Son ganin bacin ranta, balle ya ga hawayenta. Baya taba jin haushin rashin kunyar da take tafka masa, balle ya ji ya tsane ta. Idan ya zo gabanta baya iya yi mata musu, saboda girmamawa. Amsar ita ce Sajida na cin albarkacin Zuhuriyya a wajen Bakura.
Ya miqe a sanyaye ya fito daga dakin Sajida, ya nufi dakinsa. A jikin labule ya hango Samira tana lekensa ta wundon dakinta. Su na hada ido ta yi sauri ta saki labulen ta koma, da alama kishi ya hana ta barci.
Ya yi murmushi ya ce a ransa, "Kya yi kya gama, da kin san yadda muka yi da Sajida da kin tausaya min. Na san duk bayanin da zan yi miki ba za ki yarda ba, don haka shiru shi ya fi alkhairi."
Yana shiga dakinsa ya kulle ya kwanta, sai dai ya dade yana jujjuya abubuwan da suka faru tsakaninsa da Sajida da Abdulmajid.
Chapter 44 · 0% Book details