← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 64

Sashe 36

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*** *** ***
A bangaren Bakura kuwa, ya na isa gida sai ya tsaya a masallacin qofar gidansa ya yi sallar magruba da Isha'i, ya đaga hannu sama ya yi ta addu'a akan Allah Ubangiji Ya yi masa jagora, ya zaba masa abin da ya fi alkhairi akan wannan al'amari.
Da ya isa cikin gida, sai ya iske iyalansa kakaf a falo. Bayan ya rungume kowannansu, an yi sannu da zuwa. Sai suka wuce kai tsaye kan daning table, inda
Samira da masu dafa musu abinci suka sarrafa abincicika kala-kala. Suka ci, suka sha, kowa ya qoshi. Sannan suka raba dare suna hira, har wajen sha biyun dare. Bakura ya ce yara duk su je su kwanta.
"Good night mama. Good night Abba. Good night my lovely Daddy, good night Mum."
Sautin da kake ji yana fitowa daga bakin Zahra da qannenta kenan.
"Good night my babies." Amsar da Bakura da matarsa suka ba su kenan. Sannan suka dunguma suka wuce dakunansu.
Samira ta matso kusa da maigidanta ta dube shi cikin fara'a da murmushi ta karya murya ta ce, "My dear, ka dawo lafiya?"
Ya dube ta da gefen ido ya yi murmushi ya lankwashe murya ya ce, "Lafiya my love. "
Ta sake naniqarsa ta riqe yatsun hannunsa ta ce, "Alkawari kaya ne, ina alkawarina?"
Bakura ya ji 'rass-rass'!!! Gabansa ya yanke ya fadi. Babu yadda zai yi ya gocewa maganar a matsayinsa na babba, mai halin dattako. Amma duk da haka ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya furta wata kalma. Can ya rufe ido, domin abin ya fi qarfin a fada ido a bude.
Ya ce, "Samira, za mu shiga wata sabuwar rayuwa, wacce ta sha bamban da irin wacce mu ke ciki a baya. Kin yi min biyayya, iya biyayya a zamanmu.Kin nuna min qauna, iyakar qauna. Amma sai yanzu da za mu shiga sabuwar rayuwar nan zan tabbatar da biyayyar da qaunar da kike yi min ta gaskiya ce.
"Sabuwar rayuwa?" Samira ta tambaya cike da mamaki.
Bakura ya bude ido ya dube ta ya yi murmushi ya gyara zama ya ce, "Sajida yarinya ce da take neman taimako, wacce rayuwarta take daf da rugurgujewa, domin ta rasa karatunta na boko da Islamiyya a sanadiyyar wani mayaudarin yaron da yake kade mata hankali. Don haka take buqatar a taimaka mata."
Samira ta sake jin wani mamaki mai kama da mafarki ya daure mata kai.
Ta ce, "Ban fahimce ka ba, Sajidar da ta fasawa 'yata kai, ka ke so mu dauko mu riqe ta a gidan nan ta ci gaba da karatu, har mu aurar da ita'? Ko kuma yaya kake nufin a yi? Abban Yagana, ka kula da irin mutanen da za ka jajibo. Duniya a yanzu ba gaskiya, ka daina la'akari da yadda zuciyarka take, ka dauka kowa haka yake. Rayuwa ta canja, ka yi wa mutum rana ne shi kuma yayi maka dare. Daga haduwa da Baban yarinya, yana koya maka karatu, shi kenan, kun zama 'yan uwa har za ka jajibo mana 'yarsa fitsararriya ta zo ta batawa namu 'ya'yan tarbiyya."
Bakura ya dakatar da ita ya ce, "Ba haka ba ne, mahaifinta ma baya so ta ci gaba da karatu, aure yake so ya yi mata."
Samira ta yi ajiyar zuciyar dadi ta ce, "Oho kayan daki yake so ka taimaka mu su da shi, ai ba komai zan dauki nauyin kayan kicin, ai sadaka ce."
Bakura ya yi shiru kansa a kasa. Can ya dago ya dubi Samira ya ce, "My wife, kin fi kowa sanin yadda Zuhuriyya take a wajena ko?"
Samria ta gyada kai ta ce "Na sani."
Ya sake cewa, "Kin fi kowa sanin irin tsananin quncin da nake ciki, tun daga ranar da Zuhuriya ta tafi ta bar ni, har zuwa yanzu ko? Kin fi kowa sanin yadda zan iya salwantar da rayuwata a wajen nemo inda Zuhuriyya take da a ce zan iya nemo ta don kawai in sake ganinta ko? Samira na san irin halaccin da ki ka yi min a rayuwata, wanda ba dan na hadu da so da qaunarki ba da ban kawo ga wannan matsayi ba. Ba ni da wacce ta fi ki, domin duk inda aka bata min rai Allah-Allah nake in dawo wajen ki, kece me kwantar min da hankali. Samira, ina so in taimaki rayuwar Sajida, saboda abu biyu."
Samira ta yi murmushin jin dadi, zuciyarta cike da annuri ta ji rabin ranta, abun qaunarta yana yabonta.
Ta gyara zama tana mai muradin ta ji abin da zai zano mata.
Bakura ya lumshe ido gami da kankame yanyatsun hannunta ya ce, "abu na farkon da yasa nake jin ba zan iya barin rayuwar Sajida ta wulakanta ba, shi ne ina da 'ya'ya, akwai mutuwa, akwai laurara, ba na fatan yau a ce babu ni 'yata Yagana ko qannenta su shiga irin rayuwar da Sajida take shirin fadawa. Ni Musulmi ne, Sajida Musulma ce, ya cancanci in taimaka mata."
Samira ta gyada kai ta ce, "Haka ne my dear. Allah zai taimaki duk wani mai taimakon jama'a. Bayanka zai yi kyau, da izinin Ubangiji."
Bakura ya ci gaba da cewa, "Sai abu na biyu kamar yadda na fada miki a baya, Sajida ta yi kama da Zuhuriyya, tamkar kafar hagu da dama, tamkar an baskara goro gida biyu. Tun da nake ganin tagwayen da ake haifa tare su yi kama daya, ban taba ganin irin wannan kamar ta Sajida da Zuhuriyya ba. Na rasa Zuhuriyya, na hadu da Sajida, bana jin zuciyata za ta iya barin Sajida ta kauracewa idanuwana, ma'ana in daina ganinta a doron qasa ba, ba na so ta yi nesa da ni."
Wannan karon Samira ta ji kirjinta ya buga,bamm'!! Kamar an buga ganga.
Ta zare ido ta ce,
"Kamar yaya, ban gane ba?"
Bakura ya sunkuyar da kai kasa ya ce,
"Ni ne kadai na cancanci in auri Sajida. Har na amsawa mahaifanta."
Kamar wani garwashin wuta, haka Samira ta warbar da hannun Bakura daga hannunta, ta zabura ta miqe tsaye. Yayin da gaba daya gidan ya fara jujjuya mata, ji take tamkar kanta ya koma kasa, qafafuwanta ne a sama. Ta rasa gabas, ta rasa kudu. Ta ji kwakwalwarta ta rude, ta kasa tuno duk wani abin da ya taba faruwa a rayuwarta, wato ta yi (loosing memory).
Bakura ya taso yana qoqarin ya riqe ta, sai ta daka tsalle gefe tana ja da baya.
Fadi take. "Kar ka taba ni, kar ka qaraso inda nake, ba na son ganinka."
Bakura cike da mamaki ya ce, "Samira, nine fa. Ni kike cewa ba kya son ganina?"
Daga yadda ya ga idanuwanta na wurwurgawa daga inda ya tabbatar Samira ba ta cikin hayyacinta.
Bin ta yake yana lallashi, ita kuwa sai ja da baya take, daga qarshe ma ta bude qofa ta fice waje da gudu.
Bakura ya bi ta a guje suka dinga tsere a farfajiyar gidan, ba tare da masu gadi sun san abin da yake faruwa ba. Bakura ya yi ta maza, ya damkota ta na fisgewa tana fadin ita ya bar ta ta fice ta tafi ko'ina ne ma a rasa ta da ta ci gaba da zama da shi.
Ya kankame ta tsam a kirjinsa babu kalmar da take fitowa daga bakinsa sai "I'm really sorry my dear, I love you my love."
Kalaman maigidanta sun zame mata tamkar zuma a zuciyarta, sun zame mata tamkar ana hura sarewa a kunnuwanta, don haka ta ji ta kasa fisgewa saga jikinsa. Sai ta fashe da kuka, mai tafe da hawayen kunar zuci.
Hankalin Bakura ya tashi matuqa, idan ya duba hawayen Samira sai ya tuno hawayen Sajida, sai ya tuno hawayen Zuhuriyya, sai ya ji zuciyarsa tamkar an diga darmar wuta, ma'ana hawayensu dafi ne a ransa.
Ya fada a bayyane "Hawayenku tamkar dafi ne a cikin zuciyata. Ku yi hakuri zan mayar da kukanku dariya, in Allah Ya yarda."
Da kyar da sudin goshi Bakura ya lallashi Samira ta yarda suka shiga dakinsa suka kwanta, yadda ta kwana bata runtsa ba, haka ya kwana bai runtsa ba.
Kuka take, shi kuwa
Chapter 36 · 0% Book details