Sashe 1
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Jamila Tanko: KAI KA FI CANCANTA...
Na
Jamila Umar Tanko
(JUT)
Bayan tsawon lokaci da b'atansa an samo shi kuma an rubuta shi a zamanance. Domin yara da su ka taso yanzu ba su san shi ba da kuma wadanda suka karanta a baya da dadewa sun manta.
Part 1,2 & 3
PAGE: 1️⃣
La'asar sakaliya garin Kano ya yi sanyi, ga yanayi irin na farkon shigowar damuna. Iska mai sanyi ta na kad'awa tana fifita duk wani mai rai da ke cikin wannan garin. Babu abinda za ka dinga hangowa sai korayen ganyen dake kadawa, tufafin jamaa yana kadawa, don haka jama'ar da ke giftawa su na tafe cikin nishadi ba tare da gajiya ko wahalar tafiya ba.
Alhaji Bakura matashin mutum ne dan kimanin shekaru arba'in cif-cif. Wanda ke tafe cikin tsaliliyar motarsa qirar INFINITI EX 32 SUV. Mai launin ruwan toka (silver), kasancewar sanyin iskar da ke kadawa tafi sanyin A.C motarsa dadi sai ya kashe ya bude gilasan wanduna, ya na tafe iska na kada shi. Nan da nan ya tsinci kansa cikin nishadi, kallo daya za ka yi' masa annurin fuskarsa ya tabbatar maka da hakan. Dadin dadawa ma kid'a da wakar D'an kwairon da ke tashi a hankali daga cikin rediyon motarsa ya k'ara masa nishadi.
Mace duk kawaicinta da kunyarta idan ta kalli Bakura sai ta sake kallonsa saboda mutum ne kyakykyawan gaske mai kyawun fasali, Allah Ya tsara halittarsa a jikin Bakura. Dogo ne sosai mai bakar fata lallausa mai shek'in kyau, gashi da dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, bakinsa madaidaici mai k'unshe da wasu kyawawan hak'ora masu matukar haske har da wasu siraran wushiryoyi a sama da k'asan hakoran, yana da bak'in dadashi wanda ya kara fito da tsananin farin hakoran.
Duk da kyawun da Rabbul samawati Yayi masa sai Ya yi shi mutum mai tsananin tsafta da son kwalliya hakan ya sake fitar masa da kyawawan suffarsa a fili. Kwalliya ba ta tafiya daidai Idan babu kudin da za'a sayi kayan kwalliyar, amma Bakura yayi sa'a Allah Ya hada masa dukka. Ya bashi arziki mai yawa don a yanzu haka shahararran dan kasurwa ne a cikin k'asar nan har ma da kasashen k'etare baya ga dinbin ilimin qur'ani da na boko da Allah Ya bashi. Domin mahaddacin kur' ani ne, a bangaren boko kuwa Masters gare shi a bangaren Engineering.
Kallo daya za ka yiwa yadin dake jikin Bakura ka tabbatar da tsadarsa saboda kwanciyar da yayi luf a jikinsa don laushi, yadin mai launin ruwan madara(cream) sai ya saka bakar hula da bakin takalmi tsadaddu.
Kamshin turaren jikinsa kuwa duk ta inda ya gifta fiye da minti talatin kamshin baya barin wajen. Bakura dan mutanen Maiduguri kana ganinsa ka ga Kanuri kasancewar anyi masa tsage irin na barebari fashin goshi da tsage bibbiyu a kuncinsa, amma sai idan ka k'ura masa ido sosai sannan za ka iya tantancewa akwai tsaga a fuskarsa domin zanen bai fito rangadadai ba.
Mutum ne mai yawan fara'a da son zolaya idan ya ga dama, amma fa wasu lokutan akwai tsare gida, idan ya b'ata rai babu mai iya sa shi dariya. Dokoki ya gindayawa iyalansa da duk wasu da suke zaune a qarqashinsa kala-kala a, kuma dole su bi idan su na son su zauna da shi lafiya. Mutum ne wanda baya son raini, baya son rashin tarbiyya da rashin kamun kai. Baya son sakaci da addini.
Hatta yadda ake yin magana ya koyawa yaransa da matarsa, yadda za su dinga fitar da sautin maganarsu a nutse ba'a baragada ba. Idan ka shiga gidansa za ka tabbatar akwai tarbiyya domin qarami ya na girmama na gaba da shi duk qanqantar shekarun da ke tsakaninsu. Gashi d'an boko komai a tsare yake an rubuta a time table kamar lokacin tashi daga barci, lokacin sallah, lokacin cin abinci, lokacin makarantar boko da islamiyya, lokacin kallon talabijin ko hira, lokacin da yara za su dinga fita farfajiyar gidan da kekuna su zazzagaya. Haka lokacin fita wuraran shaqatawa ma an ware kamar Zoo, shopping a super markets, cinema da dai sauransu. Idan aka yi dogon hutu kuma an rubuta qasar da za' ayi visa su dunguma su tafi har da wasu daga cikin masu aiki.
Tsanani irin na Bakura ba akan iyalinsa kad'ai ya tsaya ba, abun ya shafi 'ya'yan makwabtansa ma. Za ka ga yaran makwabta sun ga mahaifinsu ba su razana sun daina fitinar da suke yi ba, amma su na ganin Bakura za su nutsu dan tsoro da kwarjini hade da girmamawa da suke yi masa. Domin shi halinsa ko wucewa ya zo yi ya ga yara su na rashin da'a zai dawo baya ya kira yaron yayi masa fada, idan ta kama da murde kunne ya murde, idan kuma ya ga ya san mahaifin yaron ko yarinyar lallai kuwa zai yi sallama a gidan ya fad'awa mahaifinsa cewar ga fitinar da d'anka yake yi a waje don haka a kula a saka ido.
Duk da wadannan tsauraran matakai da ra'ayi nasa bai sa jama' ar unguwa da iyalansa sun tsane shi ba saboda Allah Ya gani tsakani da Shi ya ke duk abinda ya yake yi ba dan ganin ido ba ne, dan haka Allah Ya zamar masa jagora, Ya bashi farin jini a wajen iyayen yara da kwarjini a idon yaran gari.
Haka kuma a zamani irin wannan da wuya ka sami mutum mai arzikin da yake taimakon jama'ar gari da daukar nauyin iyalinsa irin Bakura. Mutum ne mai matukar kyauta da kyautatawa. A kullum kuma a koda yaushe bayarwa yake dare da rana mikawa yake, saboda haka ubangiji Ya ke sake buda masa.
*** *** ***