← Book details Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 64

Sashe 14

Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata rana, ranar Litinin da yamma Bakura ne ke tafe cikin jibgegiyar motarsa Jeep Murano. Gefansa kuma babbar 'yarsa ce Zahra, sanye take da qaton hijabi. Babu abin da za ka iya gani a jikinta daga fuskarta, sai tafukan hannayenta. Daga dukkan alamu daga makarantar Islamiyya take, domin ga jakarta a rataye a kafadarta cike da Kur'anai. Ta juya ta dubi mahaifinta wanda ke kallon gabansa yana tuki da alama ya na cikin matsanancin tunanin da ya saba yi a kwanakin nan. Ta mika hannu ta kunna C.D da ke jikin motar. Kan ka ce kwabo wakar Sani Aliyu Dan Dawo wacce ya yi wa gwamnan Sokoto ta fara tashi, yayin da speakers din da ke kusurwoyin motar suka fara fitar da sautin ganguna. Bakura ya juya ya dubi Zahra, sai ta yi murmushi. Ya sa hannu ya kashe radiyon ya juya kansa ya ci gaba da kallon gabansa ba tare da ya ce mata komai ba. Ta yi shiru na wani dan lokaci mai tsawo. Can ta murda makulli ta bude gaban motar inda gaba daya disc din C.D kala-kala a layi ta zabo wani, shi kuma na karatun Kur'ani ne wanda Sudes limamin masallacin Makkah ya yi. Ta cire wancan na ciki ta saka wani. Cikin 'yan sakonni qira'a mai dadi ta fara tashi. Bakura ya juya ya dubi Zahra sai ta yi murmushi a karo na biyu, ya sa hannu ya kashe. Sai mamaki ya rufe Zahra kamar za ta yi magana sai ta fasa don ba ta ga fuskar yin magana ba. Ta sake bude wajen ajiyar za ta dauko wani C.D na-wakar Shata sai Bakura ya ture hannunta gefe ya mayar da wajen ya rufe. Ya ce, "Wai yaya haka ne Mamana. Kin cika kiriniya kamar wata karamar yarinya, ko ke ce Usman dan auta?" Ta yi dariya ta gyara zama ta zare farin gilashin da ke fuskarta. Ta ce "Abba, kwana biyu kamar kana cikin damuwa, Umma ta ce wai ka ga wata mai kama da Zuhuriyya?" Ya yi shiru yana dubanta yayin da amsa ta qauracewa bakinsa. Can jimawa Zahra ta sake cewa. "Abba, ni kuwa zan so in ga mai kama da Zuhuriyyarka ko ba komai zan dinga tuna kamanninta a rayuwata." Wannan karon ma da sauri ya waiwayo ya dube ta ba tare da ya ce mata komai ba, sai ta ga ya juya kan mota sun canza titi sun baude daga hanyar gida su na ta tafiya ba tare da wani daga cikinsu ya sake magana ba. Zahra ta yi shiru tana tunani a ranta. "Shin me yasa Abba ya juya da kan mota, ina za mu je ne?" Musamman da ta ga an wuce Lamido Cresent an shiga Badawa Layout. Su ka wuce sai ta ga su na ketawa cikin gidajen gargajiya. Zahra ta gyara zama ta dubi unguwar sosai ta juya ta dubi mahaifinta. Ta ce "Abba, ya sunan nan unguwar?" Ya dube ta ya kawar da kai gefe kamar ba zai ba ta amsa ba, dan daga dukkan alamu baya son yin magana. Can ya bude baki da kyar. Ya ce, "Sunan nan unguwar Kawon Alhaji Sani." Zahra ta gyada kai sannan ta maimaita sunan unguwar. Ta ga yana sake danna kan motar cikin lunguna, ga kwata ga gidajen kasa. Sai Zahra ta ji hankalinta ya fara tashi a tunaninta wani kauye ne suka shigo ba cikin Kano ba.Tsoro ya hana ta sake yi masa wata tambayar. Daidai wani kofar gida ta ga ya ja burki ya tsaya. Zahra ta dubi kofar gidan da suka tsaya ta daqa-daqa babu ko fenti ga almajirai nan tsibiri-tsibiri a qofar gidan su na ta karatu. Ta juya ta dubi mahaifinta cike da mamaki take tambayarsa. "Abba, ina ne nan?" Ya yi dan murmushi ya ce, "Na kawo ki gidan mai kama da Zuhuriyya. Ba kin ce ki na so ki ganta ba, ko kin fasa mu juya?" Ta yi dariya ta ce, "A'a mu shiga mu ganta." Ya yi dariya ya ce, "Ki shiga dai ni ina kofar gida, ya ya zan shiga gidan matan aure? Ki shiga tana ciki Sunanta Sajida." Zahra ta tambaya, 'Sajida sunanta? What a nice name? I like the name Sajida." Su ka bude kofar mota suka fito gaba daya. Malam Yakubu cike da mamaki mai hade da farin ciki ya mike ya tari Bakura ya na fadin, "Lale marhaban, yau muna da manyan baki sannunku da zuwa. Kai da 'yar jikar tamu ce?" Bakura ya duqa ya gaishe da Malam. Nan da nan Zahra ta zube har kasa ta kwashi gaisuwa. Bakura ya nuna Zahra ya ce, "Malam ga Zahra 'yata ta fari na dauko ta daga Islamiyya na ce bari in biyo da ita ta gaishe ku saboda wata rana, kar a hadu a hanya ba a san juna ba." Malam Yakubu ya fada cikin jin dadi, "Lallai na ga Zahra ai daga gani babu tambaya naga kamarta da kai sak, Zahra kai ta biyo kama daina wahalar da kanka wajen gabatar da ita duk inda ku ka shiga kallo daya za'asan 'yarka ce,na dade banga irin dan da yayi kama da uba ba haka. kuma ka kyauta daka kawo min Zahra, amma fa na ji dadi. Allah ya yi muku albarka, Allah ya qara zumunci. Zahra shiga cikin gida gani nan zan shigowa zan yi musu bayani. Alh. Bakura bari in dauko maka tabarma in shimfida maka a kofar gidan makwabtanmu saboda kofar gidan namu yau a cike yake da yan makaranta." Bakura ya yi dariya ya ce, "A'a babu komai Malam, zan koma cikin mota in jira har ta fito saboda ba dadewa za ta yi ba, za mu wuce Magriba ta kusa." Malam Yakubu ya ce, "To bari in shiga cikin gidan in gabatar da ita a wajen Sajida da mahaifiyarta, don ba su sanku ba, ita ba ta san su ba." Bakura ya ce, "Haka ne, lallai ba ta san yadda za ta gabatar da kanta ba, don nima ban yi mata bayani ba." Malam na shiga cikin gidansa ya iske Zahra a Zaune kan tabarma, mahaifiyar Sajida kuwa Furera na Zaune akan kujera a gaban murhu tana hidimar siyar da kunun kanwarta da dan wake. Yahuza kuwa ya zo ya saka Zahra a gaba a jima ya faki idonsu ya ce mata. "Bakuwa za ki ba ni naira hamsin idan za ki tafi?" Sajida kuwa ta dauko turmi ta hau tana hira da makwabta. Wayar da aka hana ta yi shi ne take lekawa makwabta ta katanga kawarta Hajiyayye tana ba ta aron waya tana kiran Abdulmajid. Don haka tana jin muryar mahaifinta ta yi sauri ta wurga musu wayarsu ta daka tsalle ta diro. Malam ya daka mata tsawa ya ce, "Sajida ban hana ki hirar nan da kawayenki ta katanga ba? Idan hirar suke so da ke su zagayo mana dan dai ke ba zan bari ki leka kofar gida ba, balle ki shiga makwabta mutaniyar banza. Ga bakuwa nan kin yi ko kula ta ba ki yi ba, baki iya sannu da zuwa ba, balle ga ruwa. Kun qi shimfida mata tabarma kowa ya juya yana harkokinsa, ko ruwa ba ku iya kawowa bakuwa ba. Yanzu Furera da girmanki a matsayinki na uwa sai an fada miki, sannan za ki kula bakuwa dan baki san ta ba." Furera ta zabura ta ce, "Wallahi ni na dauka bakuwar Sajida ce ko 'yar makarantarsu ce ta ga kwana biyu ba ta zuwa ta zo ta gani ko lafiya. Ta shigo ta yi sallama na ba ta tabarma ta zauna muka gaisa, ai ban san daga kofar gida ka ce ta shigo ba." Malam ya fusata ya daka tsawa, "rufe min baki, bakya kula ni, ni kaina idan kina gaban kunun nan baki da lokacin kowa ta sayar da kununki kike yi kawai. To wallahi ząn hana sana'ar nan." Ya juya ya dubi Yahuza ya yi masa tsawa ya ce, "Me ye kai kuma ka zo ka saka ta a gaba? Tashi ka dauko mata ruwa ta sha." BFurera ta tambaya, "Malam yar gidan waye wannan din." Malam ya ce, "Tsagwaron zumunci da girmamawa ce tsakanina da mahaifinta, shi ne mai zuwa daukar karatun nan wanda nake cewa a dinga zubo min abicin mutane biyu ni da shi. To 'yarsa ce ya kawo ta ta gaishe mu." Furera na budar baki sai ta ce, "Wai wa yaga dorin dosano 'yar gidan mai daukar karatu a kofar gida. To mu da ba kofar gida muke lekawa ba yaya za a yi mu sa mahaifinta, balle mu san 'yarsa? ka ga dole sai ka shigo ka yi mana bayani." Zahra ta dago da sauri ta dubi Furera da alama kalaman Furera bai yi mata dadi ba. Malam ma bai ji dadin maganar ba, sai ya ji kunya ta lullube shi. Yahuza ya kawo wani dakalallen ruwa a cikin wani ragargajejjen kwano mai lamba da tsatsa. Sajida na tsaye ta na kallon Zahra kasa-kasa, Allah-Allah take Malam ya fita ta kara hawa turmi ta leka katanga kawarta ta miko mata aron waya ta kira rabin ranta Abdulmajid. Malam ya harari Sajida ya ce, "Ki dauki ruwan ki ja ta dakinki ku gaisa mana ki dawo ki zuba mata kunu." Furera ta zabura ta dube shi ta ce, "Kunun nawa zan zuba?Ai ka san na siyarwa ne." Zahra ta yi saurí ta ce, "Ah! Alhamdulillah, a bar shi na koshi." Malam ya ji wani mummunan bacin rai, ya kudira a ransa idan Zahra ta tafi sai ya tozarta su kamar yadda su ka tozarta shi a gaban baquwarsa. Bai ce komai ba sai ya kada kai ya fice. Ya na fita Sajida ta dubi Zahra ta ce, "Ke dan Allah ki na da waya?" Zahra ta tambaya "Wacce irin waya?" Sajida ta ce, "Ashe fa 'yar gayu ce ba ki san waya ba, ina nufin hanset." Zahra ta ce, "Yes, ina da hand set." Sajida ta yi fari da ido ta ce, "Akwai kudi kuwa a wayar? " Zahra ta ce, "Akwai dubu shida a ciki." Sajida ta yi ihu ta fada cike da mamaki mai yawa ta ce, "Dubu shida? Lallai wannan 'yar gidan masu maiko ce. Saurayinki ne ya hada miki wayar ya ke sako miki kati haka da yawa?"
Chapter 14 · 0% Book details