Sashe 34
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
a ci a bikinSajida." Bakura ya bude baki ya na duban Malam, duba irin na mamaki, ya tambayi Malam cike da tangardar sauti, "Bikin Sajida da wa, yaushe ne bikin?" Malam ya gyara zama, gami da tsuke fuska ya girgiza kai don takaici. Ya ce "Al'amarin Sajida da yaron nan Abdul majid sai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un. Wato bayan mun yi wayar nan da kai, na je na sallami Sama'ila ban fada masa abin da nake so in fada masa ba, na hakura har sai mun yi tunanı ni da kai, kamar yadda ka shawarce ni. Sai rana tsaka ba aka nemi Sajida aka rasa, ta katanga ta haura da qullin kayanta wai za ta gudu wajen Abdul majid." Wata mummunar faduwar gaba ce ta tabbata a zuciyar Bakura, ya dafe kirji ya fada a bayyane, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un. Yanzu ina Sajidar?" Malam ya girgiza kai ya tabe baki ya ce "tana cikin gida a daure, a mari na saka ta har yanzu bakinta bai daina ambaton za ta fita ta gudu ba. Ai tana kama hanyar gidan su Abdul majid ba ta kai ga qarasawa ba, wasu almajiraina suka ganta da gudu akan babur suka zo suka sanar da ni, muka runtuma akan babura muka damko ta, ni kuwa na sa mata mari na daure hannuwa da kafafuwan na jefa ta a akurkin dakinta." Bakura ya yi wata doguwar ajiyar zuciya a bayyane ya sunkuyar da kansa qasa yana mai tsananin tunani da daurewar kai. Malam ya katse masa tunani ya ci gaba da cewa "Kai har ta kai ta kawo na kira kawarta Iyayye na ritsa ta na karbi lambar wayar Abdulmajid, na zo gida. Ga ni, ga Sajida, ga mahaifiyarta na bugawa Abdul Majid waya, kuma na bude wayar (hand's free) yadda kowa zai ji." Bakura ya dago da sauri ya dubi Malam ya ce "Ka kira Abdul majid saboda me?" Malam ya ce saboda ina so in ga karshen soyayyarsu, ina so Sajida ta san wannan yaro ba sa'an auranta ba ne, ba tsarin su daya ba, ba martaba da tarbiyyar gidansu daya ba ce. Ina so ta san ba kaunarta yake ba, ba kuma aurenta zai yi ba." Bakura ya ajiye kudin da yake rike da shi tun dazu ya hada gwiwoyinsa biyu ya rike da hannayensa ya ci gaba da sauraron Malam. Malam ya ci gaba da cewa, "Bugu daya waya ta yi ringing, dan iskan ya dauka, abunka da lalatacce maimakon ya yi sallama, sai ya yi fito. Ya ce, "Ya ya aka yi ne babyna?" Ashe ma ya san lambata, har wayata take sata ta buga masa, idan na ajiye a caji na tafi masallaci." Bakura ya tsuke baki, sai kada kai yake kamar wani kadangare. Ya rasa ta cewa, sai tsananin bugun da zuciyarsa take yi, tamkar 'yarsa ce ta fada hannun mayaudari. Hakika ya tausayawa Malam, ya kudiri niyyar taimakawa Malam da 'yarsa Sajida wajen yaqi da Abdul majid, mayaudaran samarin da suke yaudarar 'yan mata. A kan me?" Malam ya ci gaba da cewa, "Sai na yi masa sallama, amma yaron nan bai razana ba ma da ya ji muryar tsoho. Har wani turanci ya juya yake yi min. Na ce masa ba na jin wannan yaren mu yi Hausa. Na tsufa, ga rashin isasshiyar lafiya." Sai hawaye ya surnano daga idon Malam. Bakura sai ajiyar zuciya yake yi, har yanzu gyada kai yake, yana huci kamar wani kumurcin miciji. Ga wata zufa da yake yi kai ka ce a gaban wuta yake. Malam ya ci gaba da cewa, "Dan haka auren Sajida da Sama'ila ya tabbata, don har na fadawa Sajida kuma yau din nan na kira Sama'ila na shaida masa." Bakura ya dago da sauri ya dubi Malam ya ce, "Ka fadawa Sama'ila?" Malam ya ce "Kwarai, kuma ya amince duk da shi ma ya yi tantamar iya zama da Sajida, amma ya amince har ya yi murna, gami da godiya. Ya ce zai je ya hado dan abun da Allah ya hore masa ya zo a daura aure. Don haka ne ma na ce ni na sayi gero da masarar, sai ya kawo maka wasu." Bakura ya buga kansa da hannu, ya ja dogon numfashi mai ribas, ya girgiza kai. Ya ce, "Malam ba ka nemo mafita ba, wannan abu bai yi ba, wannan qofar ba mai 6ullewa ba ce." Malam ya yi tsuru yana duban Bakura. Can ya ce "Me yasa ka ce haka?" Bakura ya ce, "Sajida za ta dauwama a daure a mari ne? Za'a yi zaman aure ne a haka a daure? To idan ba haka ba Sajida ba za ta yadda ta zauna a gidan Sama'ila ba guduwa za ta yi. Auren dole yana iya jawowa mace ta falle ta gudu, ta shiga yawon bariki. Auren dole kan iya sawa mace ta nemi ta kashe kanta, ko ta kashe mijin, koKai kafi cancanta paid book #300