Sashe 13
Kai Kafi Can Canta Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
Kwanci tashi Bakura ya shafe watanni hudu yana zuwa daukar karatu wajen malam Yakubu, a sati sau uku bai taba fashi ba. Haka sabon zumunci da shakuwa ya dasu a zuciyoyinsu. Abu kamar wasa har abun ya fara bawa Bakura kunya domin kusan duk haduwar da zasu yi da Malam Yakubu sai ya dauko wani abu ya bashi, kuma ya tilasta masa dole sai ya karba. Ga uwa uba hidimar abinci da yake sawa a dafa masa duk sanda suka gama karatu ya kuma tilasta masa sai ya ci, amma har rana irin ta yau Bakura bai taba ido hudu da Sajida ba balle mahaifiyarta sai dai yakan jiyo muryarsu sama-sama daga cikin gida.