← Book details Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 142

Sashe 94

Garkuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aysha ce zaune gaban Umaymah Aunty Juwairiyya na gefenta ita da Hibba, cikin kula Umaymah tace.
"Yauwa Aysha kinga wannan ki ɗauke ta matsayin yayarki ita ɗin yar babban Yayanmu ne wanda na nuna miki jiya.
Mijinta kuma ya'yan Jabeer ne, Side ɗinta na kusa da naku.
In kinga duk wani abun da baki fahimta ba ki tambayeta, in kin gaji da zaman kaɗaici zaki iya shiga wurinta, da wurin Mamanku, da kuma nan wurin Gimbiya Aminatu".
A hankali ta ɗan kalli Aunty Juwairiyya, tare da cewa.
"Ina kwana Aunty". Cikin jin daɗi Aunty Juwairiyya tace.
"Lfy lau ya baƙunta". A hankali tace.
"Alhamdulillah!".Hibba ce ta ɗan tsuke baki cikin sanyi tace.
"Shike nan ai, an gabatar mata da kowa sai ni aka ware".
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"To Aysha ga Hibba wutar Umaymah, duk family itace auta a jikokin Sitti na nan ƙasar".
Murmushi ta ɗan yi sabida ganin yadda Hibba tayi sai Junainah ta faɗo mata a rai.
Ita kuwa Hibba motsata tayi tare da cewa.
"My happiness".
Cikin murmushi Aysha ta nuna kanta, alamun "Nice my happiness?".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Yes haka Umaymah tace wai kece farin cikin ahlimu da izinin ubangiji".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta.
Haka nan taji tana jin sonsu a ranta, Especially Umaymah da Hibba.
Aunty Juwairiyya kuwa da Ummi breakfast Suka gabatar mata, kana suka fita.
Umaymah da kantane ta haɗa mata tea mai kauri ita da Hibba kana ta zuba musu abincin da Aunty Juwairiyya ta kawo musu tare da cewa.
"Bismillah kuci abinci".
tana faɗin haka ta miƙa ta fita,
Ita kuwa Hibba da tsauri ta gyara zamanta tare da ɗaukan Fork ta matso gaban plate ɗin da aka zuba mata soyyyan dankali da kwai, hannun tasa ta soki guda biyu tare da ɗagowa zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya tare da zubawa Aysha ido ganin ta riƙe mata hannunta.
Cikin sanyi da ɗan sakin jiki da Hibba ta girgiza mata kai tare da cewa.
"Kada kici wannan abincin".
Cikin juya ido Hibba tace.
"Meyasa!?".
Kai ta jujjuya mata kana ta gyara zamanta, tare da ɗan kallon ƙofar shigowa ta gefen idonta.
Wani kekyawan Foodflaks da aka kawo daga sashin Gimbiya Saudatu ta jawo tare da cewa.
"Ki ɗiba a nan kici". Cikin mamaki.
Hibba tace.
"Aunty Aysha, ai Bama cin abincin gidan Gimbiya Saudatu, kuma naga Hadimanta ne suka kawoshi".
Cikin rashin gane manufar zancen Hibba tace.
"Meyasa bakwa ci?".
Juyawa Hibba tayi ta kalli bayanta kana ta juyo ta kalleta da kyau kana a hankali tace.
"Bata son Hamma Jabeer dama duk ƴan uwanshi, cewa take zata kasheshi in ta samu dama, shiyasa Umaymah take hanamu cin abinci ta".
Wani irin nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare da kallon Hibba cikin cushewar tunani ta kalli jerin kulolin da a ƙalla sun kusa takwas a gabansu.
Cikin sanyi tace.
"Buɗe su mu gani".
Jin hakane yasa Hibba buɗe su ɗaya bayan ɗaya.
ita kuwa ido take zubawa duk kular da Hibba ta buɗe.
Kular ƙarshe wacce ke ɗauke da Chicken Ball's mai zafi sai turiri yakeyi da ƙamshi.
ta nunawa Hibba tare da cewa.
"Kici wannan".
Murmushi Hibba tayi kana tace.
"Yauwa shinema na Gimbiya Aminatu kuma ta iya girki tsohuwar hakana hadimanta, a plate ta zu musu. Kana suka faraci suna ɗan korawa da ruwan tea mai zafi da kauri.
Sunaci Hibba nata janta da hira duk da ita Aysha zuciyarta a cushe yake.

Bayan sun gamane, Hadiman Gimbiya Aminatu suka shigo suka tattare komai suka gyara wurin bisa umarni Jakadiya.

Ganin Aysha ta ɗan saki jiki da Hibba ne yasa, Umaymah ta wuce Side ɗinsa ita da Umminshi.

A falo suka samu Jafar, Jalal, Jamil, Haroon. Suna bisa kujerun Dinning area, Aunty Juwairiyya tana zuzzuba musu abincin.

Murmushi Umaymah tayi cikin jin daɗin ganin su, da wal-wala hatta Jalal fuskarshi a sake take.
Jamil ne ya kalleta lokacin data ƙara so kusa dasu, cikin murmushi yace.
"Umaymah mu sai yaushe za'a nuna mana Amaryar a gabatar mata damu, ta sanmu da kyau".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ai ku tun daren jiya nagabatar da sunayenku da matsayinku gareta".
Haroon ne ya ɗan kurɓi tea tare da cewa.
"Yo ai Ni dai ba sai an gabatar daniba, domin nasanta tun safiyar jiya kafinma a ɗaura auren ko Jalal?".
Taɓe baki Jalal yayi tare da cewa.
"To ni mamaki nakeyi, ko dai dama ita tazone dan taga wanda za'a aura mata".
Umaymah ce ta ɗan zauna kusa da Jafar tare da kallonsu kana tace.
"Babu sam ita kanta bata saniba bata zata ba bata tsammaci aurenta a jiyaba.
Sai dai arashi kukayi, Ni tun jiya da kuka gayamin nasan arashi ne kawai ya haɗaku a asibitin. Bata san komaiba akan auren nan hakama iyayenta, basu da zaɓine kawai dan sun san ƙa'idar gasar Shaɗi ne hakan yasa sukayi haƙuri."
Kai Jalal ya jinjina tare da cewa.
"Uhummm mu dai yanzu yan kallone. Dan na sani tabbas yanzu za'a fara buga Game ɗin yanzu wasan zai soma".
Cikin yin ƙasa da murya Jamil yace.
"Sosai ma, dan kuwa akwai kitimurmurar da za'ayi a masarautar Joɗa, wannan Ustaz Sheykh Malam akarmakallahu Hamma Jabeer ɗin, salonshi na dabanne a dukkan lamuran yauda kullum wannan auren dai zamuga ya zai kasance!". Ya ƙarishe mgnar da yin ƙasa da murya sosai, yanayi kuma yana kallon hanyar falon Sheykh Jabeer.
Cikin haɗe fuska na wasa Umaymah tace.
"Al'khairi shine zai wanzu".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"Inafa al'khairi a wannan abun da bashi da tushe, ni kaina naji baƙin cikin wannan al'amari, auren Muhammad Jabeer ya zama kamar a munafuce a ɓoye babu wani shiri bare kimtsi kun bari an auro mishi mace kamar auren ƴar tsana".
Jafar kam abincinsa yakeci, ba tare da ya kulasuba.
Jamil kuwa sai murmushi yakeyi.
Jalal kuwa shiru yayi alamun nazari.

Ummi kuwa ware wasu kyawawan Foodflaks takeyi gefe.
Tare da abinci a cikinsu.

Bayan ta gamane ta ajiyesu gefe.
Tare da cewa Umaymah.
"Ga breakfast ɗin Sheykh".
Kai Umaymah ta gyaɗa mata.

Nan sukaci gaba da hira.

A can Side ɗin Mama kuwa,
Tunda batun auren Jabeer ya basu ya riski kunnuwan ahlin masarautar Joɗa,
kowa da abinda ke ransa.

Batool kuwa hankalin Mama in yayi dubu ya tashi, bisa irin kukan da Batool ketayi har cewa takeyi ta gane ai dama Mama bata son ya aureta.
Da kyar ta samu tasha kanta,

Gimbiya Saudatu kuwa, da Baba Nasiru da Baba Basiru da Laminu.
Zaman gaggawa suka tanada.

Suna tattauwana wannan baƙin lbrin da bai musu daɗi ba.

Zaune yake gaban wani ƙasurƙumin boka matsafi.
Cikin tsantsar tashin hankali da kiɗima yace.
"Boka Tsitaka haka mukayi da kai? Yaushe ka fara min ƙarya kan aiyukan da nake baka? Ya za'ayi kwatsam rana tsaka ace wannan shegen yaron da nakeji tamkar in kasheshi yayi aure? Da kai mukayi mgna a nan tsawon shekaru kace min ka, kashe min wutsiyar ɗan iska mai jajayen kunnuwa, babushi ba mace har yaumal ta ƙunun nadi.
Ka bani tabbacin. Har gobe sihirin na bibiyarshi, kace min duk sanda zanen kan macijin ya isa kan tsaitin ƙahon zuciyarshi zai mutu kowama ya huta. Sai kuma jiya kamar sauƙan aradu ace yayi aure!".
Wata iriyar razanenniyar dariya mara daɗin amo boka Tsitaka ya kece da ita, wanda har saida tsaunuka da kwazazzaban dake wurin suka amsa amonta.
Dariyar mugunta yakeyi babu ƙaƙƙautawa, har saida baƙon nashi ya fara hatsala cikin tashin hankali yace.
"Wannan ai insakanci ne, in bazaka iyaba ina nemo wasu matsafan. Ya zan zo da matsalata da sanyin safiyar nan kai kuma ka kama min dariya, Ni mahaukacin gidanku ne?".
Cikin dariyar boka Tsitaka yace.
"To ai tashin hankali na banzane, kana kokonto kan aikin da shekaru goma sha biyu yana cinsa yana bin jikinshi. Kana zaton ya karye ne? To bari kaji wannan sihiri yana nan a jikinshi, har kwanan gobe wutsiyarsa bata harbawa, baya jin kanshi a namiji.
Ba kuma zaiji yadda maza kejiba har abadan.
Iya bincikena banga mai mgnin da zai gani aikin da mukayi mushiba.
Auren da akayi mishi, da ya sani tabbas da zai watsa abun. In kuwa kana zaton sihirin yana sauƙa kaje ka dubu, zanen bindin maciciyar da yake tun daga kan ƴar babbar ƴatsar ƙafarshi ta dama, zaka samu kan macijiyar ya ƙetare ƙugunshi.
Na kuma gaya maka duk sanda kan macijiyar ya isa kan ƙirjinshi, saman nononshi, zai mutu, kuma yadda zai bar duniya haka ƙannenshi da wanshi zasubar masarautar Joɗa har abada yadda ba'a tambayi yaushe matacce zai dawo duniyaba haka suma baza'a tambaya ba."
Cikin ɗan jin daɗi baƙon bokan yace.
"To ai dole hankalina ya tashi, kaida kace min bazai wuce shekaru biyar ba zai rasu gashi yanzu shekaru goma sha biyu bai mutuba".
Cikin zare ido boka Tsitaka yace.
"Kai ai mun ma yi dacen yin asirin da wurine, tun kafin ya gama girma da yanzune sam bazai kamashiba, mutumin da baya rabuwa da sunan Allah a bakinshi. Yaronda ko yaushe da al'wala yake zama, ai badan hakaba da tuni mun hallakashi".
Cikin ɗan samun nitsuwa baƙon ya direwa Boka Tsitaka kuɗi kana ya miƙa ya fice.
Chapter 94 · 0% Book details